A.M. 21

Tafiyar Bulus zuwa Urushalima

1 Sa’ad da muka rabu da su da ƙyar, muka shiga jirgi muka miƙa sosai zuwa tsibirin Kos, kashegari kuma sai Rodusa, daga nan kuma sai Batara.

2 Da muka sami jirgi mai hayewa zuwa ƙasar Finikiya, muka shiga muka tafi.

3 Da muka tsinkayo tsibirin Kubrus, muka mai da shi hagun, muka ci gaba zuwa ƙasar Suriya, muka sauka a Taya, don a nan ne jirgin zai sauke kayansa.

4 Da muka sami inda masu bi suke, muka zauna a nan kwana bakwai. Sai Ruhu ya iza su suka gaya wa Bulus kada ya je Urushalima.

5 Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da ‘ya’yansu, suka raka mu bayan gari, sa’an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu’a, muka yi bankwana da juna.

6 Sai muka shiga jirgi, su kuma suka koma gida.

7 Da muka gama tafiyarmu daga Taya, muka isa Talamayas, muka gaisa da ‘yan’uwa, muka kuma kwana ɗaya a wurinsu.

8 Kashegari muka tashi muka zo Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai yin bishara, wanda yake ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan, muka sauka a wurinsa.

9 Shi kuwa yana da ‘ya’ya huɗu ‘yan mata, masu yin annabci.

10 To, muna nan zaune ‘yan kwanaki, sai wani annabi, mai suna Agabas, ya zo daga Yahudiya.

11 Da ya zo gare mu, ya ɗauki ɗamarar Bulus ya ɗaure kansa sawu da hannu, ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara, su kuma bashe shi ga al’ummai.’ ”

12 Da muka ji haka, mu da waɗanda suke wurin muka roƙi Bulus kada ya je Urushalima.

13 Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan kuke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai, ni a shirye nake, ba wai a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”

14 Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Ubangiji ya yi yadda ya so.”

15 Bayan ‘yan kwanakin nan muka shirya muka tafi Urushalima.

16 Waɗansu masu bi daga Kaisariya suka rako mu, suka kawo mu wurin Manason, mutumin Kubrus, wani daɗaɗɗen mai bi, wanda za mu sauka a gunsa.

Bulus Ya Ziyarci Yakubu

17 Da muka zo Urushalima, ‘yan’uwa suka karɓe mu da murna.

18 Kashegari Bulus ya tafi tare da mu wurin Yakubu, dattawan Ikkilisiya kuwa duk suna nan.

19 Bayan da ya gaisa da su, sai ya shiga bayyana musu filla filla abubuwan da Allah ya yi a cikin al’ummai ta wurin hidimarsa.

20 Su kuwa da suka ji haka, suka ɗaukaka Allah. Suka ce wa Bulus, “To, kā gani ɗan’uwa, dubban mutane sun ba da gaskiya a cikin Yahudawa, dukansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari’a.

21 An kuwa sha gaya musu labarinka, cewa kai ne kake koya wa dukan Yahudawan da suke cikin al’ummai su yar da Shari’ar Musa. Wai kuma kana ce musu kada su yi wa ‘ya’yansu kaciya, ko kuwa su bi al’adu.

22 To, ƙaƙa ke nan? Lalle za su ji labarin zuwanka.

23 Saboda haka sai ka yi abin da za mu faɗa maka. Muna da mutum huɗu da suka ɗauki wa’adi.

24 Sai ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka, kowa zai sani duk abin da aka gaya musu game da kai, ba wata gaskiya a ciki, kai kuma kana kiyaye Shari’a.

25 Amma game da al’ummai da suka ba da gaskiya, mun aika da wasiƙa a kan mun hukunta, cewa su guji cin abin da aka yanka wa gunki, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.”

26 Sa’an nan Bulus ya ɗibi mutanen nan, kashegari kuma da suka tsarkaka tare, sai ya shiga Haikali domin ya sanar da ranar cikar tsarkakewar tasu, wato ranar da za a ba da sadaka saboda kowannensu.

An Kama Bulus Cikin Haikali

27 Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, Yahudawan ƙasar Asiya suka gan shi a Haikalin, sai suka zuga taron duka, suka danƙe shi,

28 suna ihu suna cewa, “Ya ku ‘yan’uwa Isra’ilawa, ku taimaka! Ga mutumin da yake bi ko’ina yana koya wa mutane su raina jama’armu da Shari’a, da kuma wannan wuri. Banda haka kuma har ma ya kawo al’ummai a cikin Haikalin, ya ƙazantar da wurin nan tsattsarka.”

29 Don dā ma can sun ga Tarofimas Ba’afise tare da shi a cikin gari, sun kuma zaci Bulus ya kawo shi Haikalin.

30 Sai duk garin ya ruɗe, jama’a suka ɗungumo a guje suka danƙe Bulus, suka ja shi waje daga Haikalin, nan da nan kuma aka rufe ƙofofi.

31 Suna neman kashe shi ke nan, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar yaƙi, wai Urushalima duk ta hargitse.

32 A nan tāke ya ɗibi soja da jarumawa, suka ruga zuwa wajensu. Su kuwa da ganin shugaban da soja suka daina dūkan Bulus.

33 Sai shugaban ya matsa kusa ya kama Bulus, ya yi umarni a ɗaure shi da sarƙa biyu, sa’an nan ya tambaya ko shi wane ne, da abin da kuma ya yi.

34 Taron kuwa suka ɗau kururuwa, waɗansu suka ce kaza, waɗansu suka ce kaza. Don tsananin hargowa ma har ya kasa samun ainihin tushen maganar, ya yi umarni a kai shi kagarar sojoji.

35 Da Bulus ya zo ga bakin matakala, sai da soja suka kinkime shi saboda haukan taron,

36 don taron jama’a na dannowa a bayansu, suna ihu suna cewa, “A yi da shi!”

Hanzarin Bulus

37 An yi kusan shigar da Bulus kagarar sojoji ke nan, sai ya ce wa shugaban, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai shugaban ya ce, “Ashe, ka iya Helenanci?

38 Shin, ba kai ne Bamasaren nan da shekarun baya ya haddasa tawaye ba, har ya ja mutanen nan dubu huɗu masu kisankai jeji?”

39 Sai Bulus ya amsa ya ce, “Ai, ni Bayahude ne na Tarsus ta ƙasar Kilikiya, ɗan shahararren birni, ina roƙonka ka bar ni in yi wa mutane jawabi.”

40 Da ya ba shi izini, sai Bulus ya tsaya a kan matakala, ya ɗaga wa jama’a hannu su yi shiru. Da suka yi tsit, sai ya yi musu magana da Yahudanci.