A.M. 22

1 “Ya ku ‘yan’uwa da shugabanni, ku ji hanzarin da zan kawo muku a yanzu.”

2 Da suka ji ya yi musu magana da Yahudanci, sai suka ƙara natsuwa. Sa’an nan ya ce,

3 “Ni bayahude ne, haifaffen Tarsus, ƙasar Kilikiya, amma a nan garin na girma, aka kuma karantar da ni wurin Gamaliyal, bisa ga tsarin tsanantacciyar hanyar nan ta Shari’ar kakanninmu. Ina mai himmar bauta wa Allah, kamar yadda dukanku kuke a yau,

4 har na tsananta wa masu bin wannan hanya, ina karkashe su, ina ɗaure mutane maza da mata, ina jefa su a kurkuku.

5 Babban firist ma da dukan majalisar shugabannin jama’a za su iya shaidata, daga gunsu ne kuma na karɓi wasiƙu zuwa ga ‘yan’uwanmu Yahudawa, na tafi Dimashƙu, don in ɗebo waɗanda suke can ma, in zo da su Urushalima a ɗaure, a azabta su.”

Bulus Ya Ba Da Labarin Juyowarsa

6 “Ina cikin tafiya, da na yi kusa da Dimashƙu, wajen rana tsaka, kwamfa sai wani matsanancin haske ya bayyano daga sama, ya haskaka kewaye da ni.

7 Sai na fāɗi, na kuma ji wata murya tana ce mini, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?’

8 Ni kuma na amsa na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ Sai ya ce mini, ‘Ni ne Yesu Banazare wanda kake tsananta wa.’

9 To, waɗanda suke tare da ni sun ga hasken, amma ba su ji kalmomin mai yi mini maganar nan ba.

10 Sai na ce, ‘To, me zan yi, ya Ubangiji?’ Sai ubangiji ya ce mini, ‘Tashi, ka shiga Dimashƙu, a can ne za a faɗa maka duk abin da aka ɗora maka ka yi.’

11 Da na kāsa gani saboda tsananin hasken nan, sai waɗanda suke tare da ni suka yi mini jagora, har na isa Dimashƙu.

12 “Sai kuma wani mai suna Hananiya, mai bautar Allah ne wajen bin Shari’a, wanda duk Yahudawan da suke zaune a can suke yabo,

13 ya zo ya tsaya a kusa da ni, ya ce mini, ‘Ya ɗan’uwana Shawulu, ganinka yă komo maka.’ Nan tāke, sai ganina ya komo, na kuwa gan shi.

14 Sai ya ce, ‘Allahn kakanninmu ya zaɓe ka don kă san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji jawabi daga bakinsa.

15 Don za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abin da ka gani, ka kuma ji.

16 To, a yanzu me kake jira? Tashi, a yi maka baftisma a wanke zunubanka ta wurin kira bisa sunansa.’ ”

Kiran Bulus zuwa ga Al’ummai

17 “Da na komo Urushalima, ina addu’a a Haikali, sai wahayi ya zo mini.

18 Na gan shi, yana ce mini, ‘Yi sauri maza ka fita daga Urushalima, don ba za su yarda da shaidarka a kaina ba.’

19 Ni kuma na ce, ‘Ya Ubangiji, ai, su ma kansu sun sani a kowace majami’a na ɗaɗɗaure waɗanda suka gaskata da kai, na kuma daddoke su.

20 Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanas, mashaidin nan naka, ni ma ina a tsaye a gun, ina goyon bayan abin da aka yi, har ma ina tsare tufafin masu kisansa.’

21 Sai ya ce mini, ‘Tashi ka tafi, zan aike ka can nesa a wurin al’ummai.’ ”

Shugaba Ya Tsare Bulus

22 Suna ta sauraronsa har ya iso kalmar nan, sai suka ɗau ihu suka ce, “A kashe shi! A raba irin mutumin nan da duniya, bai kyautu ya rayu ba!”

23 Da suka dinga ihu suna kaɗa mayafansu suna ta ature da ƙura,

24 sai shugaba ya yi umarni a kai Bulus kagarar soja a tuhume shi da bulala, don yă san abin da ya sa suke masa ihu haka.

25 Bayan sun ɗaɗɗaure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa jarumin ɗin da yake tsaye kusa, “Ashe, ya halatta a gare ka ka yi wa mutumin da yake da ‘yancin Roma bulala, ba ko bin ba’asi?”

26 Da jarumin ɗin ya ji haka, sai ya je ya shaida wa shugaban, ya ce, “Me kake shirin yi ne? Mutumin nan fa Barome ne.”

27 Sai shugaban ya zo ya ce wa Bulus, “Faɗa mini gaskiya, kai kuwa Barome ne?” Sai ya ce, “I”.

28 Sai shugaban ya amsa ya ce, “Ni fa da kuɗi masu yawa na sami ‘yancin nan.” Bulus ya ce, “ni kuwa da shi aka haife ni.”

29 Saboda haka, waɗanda suke shirin tuhumarsa, suka rabu da shi nan da nan. Shi ma shugaban da ya fahimci Bulus Barome ne, sai ya tsorata, ga shi kuwa, ya ɗaure shi.

Bulus a gaban ‘Yan Majalisa

30 Kashegari kuma da shugaban ya so sanin ainihin ƙarar da Yahudawa suke yi a kan Bulus, sai ya kwance shi, ya yi umarni manyan firistoci da dukan majalisa su taru, sa’an nan ya sauko da Bulus ya tsai da shi a gabansu.