A.M. 3

An Warkar da Gurgu a Ƙofar Haikali

1 To, Bitrus da Yahaya suna tafiya Haikali a lokacin addu’a, da ƙarfe uku na yamma,

2 sai ga wani mutum da aka haifa gurgu, ana ɗauke da shi. Kowace rana kuwa akan ajiye shi a ƙofar Haikali, wadda ake kira Ƙawatacciyar Ƙofa, don ya roƙi sadaka ga masu shiga Haikali.

3 Da ganin Bitrus da Yahaya suna shiga Haikalin, ya roƙe su sadaka.

4 Bitrus kuwa ya zuba masu ido, tare da Yahaya, ya ce, “Dube mu.”

5 Sai kuwa duk hankalinsa ya koma a kansu, da tsammanin samun wani abu a gunsu.

6 Amma Bitrus ya ce, “Kuɗi kam, ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. Da sunan Yesu Almasihu Banazare, yi tafiya.”

7 Sai Bitrus ya kama hannunsa na dama, ya tashe shi. Nan tāke ƙafafunsa da wuyan sawunsa suka yi ƙarfi.

8 Wuf, sai ya zabura, ya miƙe tsaye, ya fara tafiya, ya shiga Haikalin tare da su, yana tafe, yana tsalle, yana kuma yabon Allah.

9 Duk mutane suka gan shi yana tafe yana yabon Allah.

10 Suka kuwa gane shi ne mai zama a bakin Ƙawatacciyar Ƙofa ta Haikali yana bara. Sai mamaki ya kama su, suna al’ajabi ƙwarai a kan abin da aka yi masa.

Jawabin Bitrus a Shirayin Sulemanu

11 Tun yana riƙe da Bitrus da Yahaya, duk jama’a suka sheƙa a guje zuwa wurinsu a cikin shirayin da ake kira Shirayin Sulemanu, suka ruɗe don mamaki.

12 Da Bitrus ya ga haka, sai ya yi wa jama’a jawabi, ya ce, “Ya ku ‘yan’uwa Isra’ilawa, don me kuke mamakin wannan? Don me kuma kuke ta dubanmu, sai ka ce da ikon kanmu ne, ko kuwa don ibadarmu muka sa shi tafiya?

13 Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allahn kakanninmu, shi ya ɗaukaka Baransa Yesu, wanda kuka bashe shi, kuka kuma ƙi shi, a gaban Bilatus, sa’ad da ya ƙudura zai sake shi.

14 Amma ku kuka ƙi Mai Tsarkin nan, mai adalci kuka roƙa a saukar muku da mai kisankai,

15 kuka kuwa kashe Tushen Rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga haka.

16 To, sunansa ne, wato ta wurin bangaskiya ga sunansa, shi ne ya ba mutumin nan da kuke gani, kuka kuma sani, ƙarfi. Hakika, bangaskiyar da take ta wurin Yesu ita ta ba mutumin nan cikakkiyar lafiya, a gaban idonku duka.

17 “To, yanzu ‘yan’uwa, na sani da jahilci kuka yi haka, kamar yadda shugabanninku ma suka yi.

18 Amma ta haka Allah ya cika faɗar da ya riga ya yi ta bakin annabawa duka, cewa Almasihunsa zai sha wuya.

19 Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da ku,

20 ya kuma aiko da Almasihun da aka ƙaddara muku tun dā, wato Yesu,

21 wanda lalle ne ya zauna a Sama, har kafin lokacin nan na sabunta dukkan abubuwa da Allah ya faɗa tun zamanin dā ta bakin annabawansa tsarkaka.

22 Musa ma ya ce, ‘Ubangiji Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin ‘yan’uwanku, kamar yadda ya tashe ni. Lalle ne ku saurari duk abin da ya faɗa muku.

23 Zai zamana kuma duk wanda ya ƙi sauraron annabin nan, za a hallaka shi daga cikin jama’a.’

24 Hakika dukan annabawa da suka yi annabci, wato tun daga kan Sama’ila da waɗanda suka zo daga baya, duk sun yi faɗi a kan waɗannan kwanakin.

25 Ku ne tsatson annabawa, ku ne kuma magadan alkawarin da Allah ya yi wa kakanninku, da ya ce wa Ibrahim, ‘Ta zuriyarka ne za a yi wa dukkan kabilan duniya albarka.’

26 Da Allah ya taso da Baransa, gare ku ne ya fara aiko shi, don yă yi muku albarka ta juyo da ko wannenku ga barin muguntarsa.”