A.M. 4

Bitrus da Yahaya a gaban ‘Yan Majalisa

1 Suna cikin yin magana da jama’a sai firistoci da shugaban dogaran Haikali da Sadukiyawa suka ji haushi ƙwarai, suka aukar musu,

2 don suna koya wa jama’a, suna tabbatar da tashi daga matattu, suna misali da Yesu.

3 Sai suka kama su, suka sa su a gidan waƙafi kafin gobe, don magariba ta riga ta yi.

4 Amma da yawa daga cikin waɗanda suka ji wa’azin sun ba da gaskiya, har jimillarsu ta kai wajen mutum dubu biyar.

5 Kashegari shugabanninsu da dattawansu da malamansu na Attaura suka taru a Urushalima,

6 tare da Hanana, babban firist, da Kayafa, da Yahaya, da Iskandari, da kuma duk waɗanda suke dangin babban firist.

7 Da suka tsai da su a tsakiya, suka tuhume su, suka ce, “Da wane iko ne, ko kuwa da wane suna ne, kuka yi haka?”

8 Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce musu, “Ya ku shugabannin jama’a, da dattawa,

9 in dai ana tuhumarmu ne yau a kan alherin da aka yi wa gajiyayyen mutumin nan, ta yadda aka warkar da shi,

10 to, sai ku sani, ku duka, da kuma duk jama’ar Isra’ila, da sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda ku kuka gicciye, wanda kuma Allah ya tashi shi daga matattu, albarkacinsa ne mutumin nan yake tsaye a gabanku lafiyayye.

11 Wannan shi ne dutsen nan da ku magina kuka raina, shi ne kuwa ya zama mafificin dutsen gini.

12 Ba kuma samun ceto ga wani, domin ba wani suna duk duniyan nan da aka bayar cikin mutane, wanda lalle ta wurinsa ne za mu sami ceto.”

13 To, da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yahaya, suka kuma gane marasa ilimi ne, talakawa kuma, suka yi mamaki, suka kuwa shaida su, a kan dā suna tare da Yesu.

14 Amma da suka ga mutumin nan da aka warkar ɗin yana tsaye tare da su, suka rasa hanyar yin mūsu.

15 Bayan sun umarce su, su fita daga majalisa, suka yi shawara da juna,

16 suka ce, “Yaya za mu yi da mutanen nan? Don hakika sanannen abu ne ga dukan mazauna Urushalima, cewa an yi wata tabbatacciyar mu’ujiza ta wurinsu, ba mu kuwa da halin yin mūsawa.

17 Amma don kada abin ya ƙara bazuwa a cikin mutane, sai mu yi musu kashedi, kada su kuskura su ƙara yi wa kowa magana, suna kama wannan suna.”

18 Sai suka kirawo manzannin, suka kwaɓe su, kada su kuskura su yi wa kowa magana, ko su ƙara koyarwa suna kama sunan Yesu.

19 Amma Bitrus da Yahaya suka mayar musu da jawabi suka ce, “To, in daidai ne a gun Allah mu fi jin taku da ta Allah, sai ku duba ku gani.

20 Domin mu kam, ba yadda za a yi sai mun faɗi abin da muka ji, muka kuma gani.”

21 Da kuma suka daɗa yi musu kashedi, suka sake su, don sun rasa yadda za su hore su saboda jama’a, domin dukan mutane suna ɗaukaka Allah saboda abin da ya auku.

22 Mutumin nan da aka yi wa mu’ujizar nan ta warkarwa kuwa ya ba shekara arba’in baya.

Masu Bi Sun Yi Addu’a Su Yi Magana Gabagaɗi

23 Da aka sau su, suka tafi wurin mutanensu, suka ba su labarin duk abin da manyan firistoci da shugabanni suka faɗa musu.

24 Su kuwa da jin haka, sai suka ɗaga muryarsu ga Allah da nufi ɗaya, suka ce, “Ya Mamallaki, Mahaliccin sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu,

25 wanda ta Ruhu Mai Tsarki, ta bakin kakanmu Dawuda baranka, ka ce,

‘Don me al’ummai suka husata?

Kabilai kuma suka yi makidar al’amuran wofi?

26 Sarakunan duniya sun kafa dāga,

Mahukunta kuma sun haɗa kai,

Suna gāba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.’

27 Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al’ummai da jama’ar Isra’ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.

28 Sun haɗa kai domin su yi dukan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ga ikonka da nufinka.

29 Yanzu kuma ya Ubangiji, dubi wannan kashedin nasu, ka yi wa bayinka baiwar yin maganarka da iyakar ƙarfin hali,

30 kana kuma miƙo hannunka kana warkarwa, ana kuma yin mu’ujizai da abubuwan al’ajabi albarkacin sunan Baranka mai tsarki Yesu.”

31 Bayan sun yi addu’a, wurin da suke a tattare ya raurawa. Sai duk aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta faɗar maganar Allah gabagaɗi.

Kome na ‘Yan Ikkilisiya Ɗaya Ne

32 To, duk taron da suka ba da gaskiya kuwa nufinsu ɗaya ne, ra’ayinsu ɗaya, ba kuma waninsu da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, sai dai kome nasu ne baki ɗaya.

33 Manzanni kuma suka yi shaida da tabbatarwa mai ƙarfi a kan tashin Ubangiji Yesu daga matattu. Alheri mai yawa yana tare da kowannensu,

34 har ba wanda yake da rashi a cikinsu ko ɗaya, don duk masu gonaki ko gidaje sun sayar da su,

35 sun kawo kuɗin, sun ajiye gaban manzanni, an kuwa rarraba wa kowa gwargwadon bukatarsa.

36 Ana cikin haka sai Yusufu, wani Balawiye, asalinsa mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannin suke kira Barnaba, (wato ɗan ƙarfafa zuciya),

37 ya sayar da wata gonarsa, ya kawo kuɗin ya ajiye a gaban manzannin.