AFI 2

Daga Mutuwa zuwa Rai

1 Ku kuma yā raya ku sa’ad da kuke matattu ta wurin laifofinku da zunubanku,

2 waɗanda dā kuke a ciki, kuna biye wa al’amarin duniyar nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskar nan da take zuga zuciyar kangararru a yanzu.

3 Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha’awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi’a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran ‘yan adam.

4 Amma Allah da yake mai yalwar jinƙai ne, saboda matsananciyar ƙaunar da yake yi mana,

5 ko a sa’ad da muke matattu ma ta wurin laifofinmu, sai ya rayar da mu tare da Almasihu (ta wurin alheri an cece ku),

6 a cikin Almasihu Yesu kuma ya tashe mu tare, har ya ba mu wurin zama tare a samaniya.

7 Allah ya yi wannan kuwa domin a zamani mai zuwa ya bayyana yalwar alherinsa marar misaltuwa, ta wajen nuna mana alheri ta wurin Almasihu Yesu.

8 Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah,

9 ba kuwa saboda da aikin lada ba, kada wani ya yi fariya.

10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

Zama Ɗaya da Almasihu

11 Saboda haka, ku tuna dā ku al’ummai ne bisa ɗabi’a, ga waɗanda ake kira masu kaciyar nan kuwa, sukan kira ku marasa kaciya (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).

12 Ku kuma tuna a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu, bare ne ga jama’ar Isra’ila, bāƙi ne ga alkawaran nan da Allah ya yi, marasa bege, marasa Allah kuma a duniya.

13 Amma a yanzu, a cikin Almasihu, ku da dā kuke can nesa, an kawo ku kusa ta wurin jinin Almasihu.

14 Domin Almasihu shi ne salamarmu, shi wanda ya mai da Yahudawa da al’ummai ɗaya, wato ya rushe katangar nan da ta raba su a kan gāba.

15 Har ya soke Shari’ar nan mai umarni da dokoki, ta wurin ba da jikinsa, domin ta gare shi yă halicci sabon mutum guda daga mutanen nan biyu, ta haka yă kawo salama,

16 yă kuma sulhunta su duka biyu ga Allah, su zama jiki ɗaya ta wurin gicciye, ta haka yă kashe gābar.

17 Ya kuwa zo ya yi muku albishirin salama, ku da kuke nesa, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa.

18 Domin ta gare shi ne dukanmu biyu muka sami isa gun Uba ta hanyar Ruhu guda.

19 Wato ashe, ku ba baƙi ba ne kuma, ko kuwa bāre, ai, ku abokan ‘yanci ne na tsarkaka, iyalin Allah kuma,

20 waɗanda aka gina bisa tushen manzanni da annabawa, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne mafificin dutsen ginin,

21 dukan wanda aka haɗa tsarin ginin a cikinsa, yana kuma tashi ya zama haikali tsattsarka na Ubangiji.

22 A cikinsa ne ku kuma aka gina ku, ku zama mazaunin Allah ta wurin Ruhu.