AFI 3

Hidimar Bulus ga Al’ummai

1 Domin haka, ni Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu domin amfanin ku al’ummai,

2 in dai kun ji labarin mai da ni mai hidimar alherin Allah wanda aka yi mini baiwa saboda ku,

3 wato yadda aka sanar da ni asirin Ubangiji ta wahayi, kamar yadda na riga na rubuta a taƙaice.

4 A yayin da kuka karanta wannan, za ku iya gane basirata saboda asirin Almasihu,

5 wanda a zamanin dā ba a sanar da ‘yan adam ba, kamar yadda a yanzu aka bayyana wa manzanninsa tsarkaka da annabawa, ta wurin Ruhu,

6 wato, yadda ta wurin bishara al’ummai da suke abokan gādo da mu, gaɓoɓin jiki guda, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Almasihu Yesu.

7 An kuwa sa ni mai hidimar wannan bishara, a bisa ga baiwar alherin Allah da aka yi mini ta ƙarfin ikonsa.

8 Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al’ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,

9 in kuma bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda shekara da shekaru yake a ɓoye a gun Allah, wanda ya halicci dukkan abubuwa.

10 An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala’iku da masu iko a samaniya, ta hanyar Ikkilisiya.

11 Wannan kuwa bisa ga dawwamammen nufin nan ne da Allah ya zartar a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

12 A cikinsa muke da gabagaɗin isa ga Allah, da amincewa, ta wurin bangaskiyarmu a gare shi.

13 Saboda haka, ina roƙonku kada ku karai da ganin wahalar da nake sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.

A San Ƙaunar Almasihu

14 Saboda haka, nake durƙusawa a gaban Uban,

15 shi da yake sa wa kowace kabila ta sama da ta ƙasa suna,

16 ina addu’a ya yi muku baiwa bisa ga yalwar ɗaukakarsa, ku ƙarfafa matuƙa a birnin zuciyarku ta wurin Ruhunsa,

17 har ma Almasihu yă zauna a zukatanku ta wurin bangaskiyarku, domin ƙauna ta kahu da gindinta sosai a zukatanku,

18 har ku sami kaifin basira tare da dukan tsarkaka, ku fahimci ko mene ne fāɗin ƙaunar Almasihu, da tsawonta da zacinta, da kuma zurfinta,

19 ku kuma san ƙaunar da Almasihu yake yi mana, wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan falala ta Allah.

20 Ɗaukaka tā tabbata ga wannan da yake da ikon aikatawa fiye da dukkan abin da za mu roƙa, ko za mu zata nesa, wato, aikatawa ta ƙarfin ikonsa da yake aiki a zuciyarmu.

21 Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a cikin Ikkilisiya ta wurin Almasihu Yesu, har ya zuwa dukkan zamanai har abada abadin. Amin.