AMOS 7

Wahayin Fāra

1 A wahayin da Ubangiji ya nuna mini, sai na ga ya yi cincirindon fara nan da nan bayan da aka ƙarasa yankan rabon ingiricin da yake na sarki, ciyawar kuma ta soma tohuwa.

2 A wahayin, na ga fara ta cinye kowane ɗanyen ganye a ƙasar. Sai na ce,

“Ka gafarta wa jama’arka, ya

Ubangiji!

Ƙaƙa za su tsira?

Ga su ‘yan kima ne, marasa

ƙarfi.”

3 Ubangiji kuwa ya dakatar da

nufinsa,

Ya ce, “Abin da ka gani, ba zai faru

ba.”

Wahayin Wuta

4 A wahayin da Ubangiji ya nuna mini, na gan shi yana shirin hukunta jama’arsa da wuta. Wutar ta ƙone babbar teku, har ma ta fara ƙone ƙasar.

5 Sa’an nan na ce,

“Ya Ubangiji, in nufinka ne ka bari!

Ƙaƙa jama’arka za su tsira?

Ga su ‘yan kima ne, marasa

ƙarfi.”

6 Ubangiji kuwa ya dakatar da nufinsa, ya ce,

“Wannan ma ba zai faru ba.”

Wahayin Ma’auni

7 Ubangiji kuma ya nuna mini wani wahayi. A wahayin sai na gan shi, yana tsaye kusa da bangon da ake ginawa. Yana riƙe da igiyar awon gini.

8 Ya tambaye ni, ya ce, “Amos, me ka gani?”

Sai na ce, “Igiyar awon gini na gani.”

Ya kuma ce,

“Duba, da wannan zan nuna yadda

jama’ata sun zama kamar bangon

da ya karkace.

Ba zan sāke nufina a kan yi musu

hukunci ba.

9 Zan hallakar da wuraren sujada na

zuriyar Ishaku.

Za a hallakar da tsarkakan wurare na

Isra’ila.

Zan fāɗa wa zuriyar sarki

Yerobowam da yaƙi.”

Amos da Amaziya

10 Amaziya, firist, na Betel kuwa, ya tafi ya faɗa wa Yerobowam Sarkin Isra’ila, ya ce, “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a cikin jama’ar Isra’ila. Maganganunsa za su hallakar da ƙasar.

11 Abin da ya faɗa ke nan, ‘Za a kashe Yerobowam a bakin dāga, a sa jama’ar Isra’ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ ”

12 Amaziya kuwa ya ce wa Amos, “Kai maƙaryaci ne na ainihi! Koma ƙasar Yahuza ka nemi abin zaman gari, ka yi ta annabcinka a can.

13 Amma a nan Betel kada ka ƙara yin annabci. Nan wurin yin sujada na sarki ne, haikali ne na al’umma.”

14 Sai Amos ya amsa ya ce, “Ni ba annabi ba ne. Wannan ba aikina ba ne. Ni makiyayi ne, mai kuma lura da itatuwan ɓaure.

15 Amma Ubangiji ya raba ni da aikina na kiwo, ya umarce ni in tafi in yi magana da jama’arsa, wato Isra’ila.

16 Domin haka, sai ka kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce. Saboda ka ce mini in daina yin annabci gāba da jama’ar Isra’ila, kada kuwa in yi wa zuriyar Ishaku ɓaɓatu,

17 to, ga abin da Ubangiji ya ce maka, ya kai Amaziya, ‘Matarka za ta zama karuwa a birni, za a karkashe ‘ya’yanka a cikin yaƙi. Za a rarraba wa waɗansu ƙasarka, kai kanka kuwa za ka mutu a ƙasar arna. Za a sa jama’ar Isra’ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ ”