AMOS 9

Ba a Kauce wa Hukuncin Allah

1 Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce,

“Bugi ginshiƙan Haikali don shirayi

duka yă girgiza.

Farfasa su, su fāɗi a kan mutane!

Sauran mutane kuwa,

Zan kashe su a wurin yaƙi.

Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.

2 Ko da za su nutsa zuwa lahira,

Zan kama su.

Ko sun hau Sama,

Zan turo su.

3 Ko da za su hau su ɓuya a bisa

ƙwanƙolin Dutsen Karmel,

Zan neme su in cafko su.

Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashin

teku,

Sai in sa dodon ruwa yă yayyage su.

4 Idan kuwa abokan gābansu ne suka

kama su,

In umarce su su hallaka su da

takobi,

Tun da na yi ƙudurin ƙare su.”

5 Ubangiji Allah Mai Runduna

Ya taɓi duniya, ta girgiza.

Duk waɗanda suke zaune cikinta

Suna baƙin ciki.

Duniya duka takan hau

Ta kuma gangara kamar ruwan

Kogin Nilu.

6 Ubangiji ya gina al’arshinsa a sama,

Ya shimfiɗa samaniya a bisa duniya.

Ya sa ruwan teku ya zo,

Ya kwarara shi a bisa duniya.

Sunansa Ubangiji ne!

7 Ubangiji ya ce, “Jama’ar Isra’ila,

Ina yi da ku daidai yadda nake yi da

Habashawa.

Na fito da Filistiyawa daga Kaftor,

Suriyawa kuwa daga Kir,

Daidai yadda na fito da ku daga

Masar.

8 Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi.

Zan hallaka su daga duniya,

Amma ba zan hallaka dukan jama’ar

Yakubu ba.

9 “Zan umarta a rairayi jama’ar Isra’ila

Da matankaɗi kamar hatsi.

Zan rairaye su daga cikin sauran

al’umma,

Duk da haka ko ƙwaya ɗaya ba za

ta salwanta ba.

10 Masu zunubi daga cikin jama’ata za

su mutu a yaƙi,

Wato dukansu da suke cewa,

‘Allah ba zai bar wata masifa ta

kusace mu ba!’ ”

Ceton da Za a Yi wa Isra’ila Nan Gaba

11 “Wata rana zan sāke tayar da birnin

Dawuda

Tankar yadda akan ta da gidan da ya

rushe.

Zan gyara garunsa, in sāke mai da

shi.

Zan sāke gina shi in mai da shi

kamar yadda yake tun dā.

12 Ta haka jama’ar Isra’ila za ta ci

nasara bisa sauran ƙasar Edom

wadda ta ragu,

Da bisa dukan al’umman da a dā su

nawa ne,”

In ji Ubangiji, wanda zai sa

al’amarin ya auku.

13 Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna

zuwa,

Sa’ad da girbi zai bi bayan huda nan

da nan,

Matsewar ruwan inabi kuma

Za ta bi bayan shuka nan da

nan.

Duwatsu za su zubo da ruwan inabi

mai zaƙi,

Tuddai kuma su gudano da shi.

14 Zan komo da mutanena ƙasarsu,

Za su giggina biranensu da suka

rurrushe,

Su zauna a cikinsu.

Za su shuka gonakin inabi, su sha

ruwan inabin.

Za su yi lambuna, su ci amfaninsu.

15 Zan dasa su a ƙasar da na ba su,

Ba kuwa za a ƙara tumɓuke su

ba.”

Ubangiji Allahnku ne ya faɗa.