FILIB 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus da Timoti, bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka a cikin Almasihu Yesu waɗanda suke a Filibi, tare da masu kula da ikkilisiya da kuma masu hidimarta.

2 Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu, su tabbata a gare ku.

Addu’ar Bulus domin Filibiyawa Masu Bin Almasihu

3 Ina gode Allahna duk sa’ad da nake tunawa da ku,

4 a kullum kuwa a kowace addu’a da nake muku duka, da farin ciki nake yi.

5 Ina godiya saboda tarayyarku da ni wajen yaɗa bishara, tun daga ranar farko har ya zuwa yanzu.

6 Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu.

7 Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.

8 Domin Allah shi ne mashaidina a kan yadda nake begenku duka, da irin ƙaunar da Almasihu Yesu yake yi.

9 Addu’ata ita ce, ƙaunarku ta riƙa haɓaka da sani da matuƙar ganewa,

10 domin ku zaɓi abubuwa mafifita, ku zama sahihai, marasa abin zargi, har ya zuwa ranar Almasihu,

11 kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.

Manufar Rayuwata, Almasihu Ne

12 ‘Yan’uwa, ina so ku sani, al’amuran nan da suka auku a gare ni, har ma sun yi amfani wajen yaɗa bishara,

13 har dai ya zama sananne ga dukan sojan fāda da sauran jama’a, cewa ɗaurina saboda Almasihu ne.

14 Har ma galibin ‘yan’uwa cikin Ubangiji suka ƙarfafa saboda ɗaurina, sun kuma ƙara fitowa gabagaɗi, su faɗi Maganar Allah ba tare da tsoro ba.

15 Lalle waɗansu suna wa’azin Almasihu saboda hassada da husuma, amma waɗansu kam, saboda kyakkyawar niyya ne.

16 Waɗannan suna yi ne a kan ƙauna, sun sani, an sa ni nan ne domin kāriyar bishara.

17 Waɗancan kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin ɗaurina.

18 Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Almasihu, na kuma yi farin ciki da haka. I, zan yi farin ciki kuwa.

19 Domin na san duk wannan zai zama sanadin lafiyata, ta wurin addu’arku da taimakon Ruhun Yesu Almasihu.

20 Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata.

21 Domin ni, a gare ni, rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce.

22 In ya zamanto rayuwa zan yi a cikin jiki, to, zan yi aiki mai amfani ke nan. Amma na rasa abin da zan zaɓa.

23 Duka biyu suna jan hankalina ƙwarai. Burina in ƙaura in zauna tare da Almasihu, domin wannan shi ne ya fi kyau nesa.

24 Amma in wanzu a cikin jiki, shi ya fi wajabta saboda ku.

25 Na tabbata haka ne, na kuwa sani zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku yin farin ciki,

26 ku kuma sami ƙwaƙƙwaran dalilin yin taƙama da Almasihu ta wurina, saboda sāke komowata gare ku.

27 Sai dai ku yi zaman da ya cancanci bisharar Almasihu, domin ko na zo na gan ku, ko kuwa ba na nan, in ji labarinku, cewa kun dage, nufinku ɗaya, ra’ayinku ɗaya, kuna fama tare saboda bangaskiyar da bishara take sawa,

28 ba kwa kuwa jin tsoron magabtanku sam. Wannan kuwa ishara ce a gare su ta hallakarsu, ku kuwa ta cetonku, isharar kuwa daga Allah take.

29 Gama an yi muku alheri, cewa ba gaskatawa da Almasihu kawai za ku yi ba, har ma za ku sha wuya dominsa,

30 kuna shan fama irin nawa wanda kuka gani, wanda kuke ji nake sha har yanzu.