TIT 3

Himmantuwa ga Aiki Nagari

1 Ka riƙa tuna musu su yi wa mahukunta da shugabanni ladabi, suna yi musu biyayya, suna kuma zaune da shirinsu na yin kowane irin kyakkyawan aiki.

2 Kada su ci naman kowa, kada su yi husuma, sai dai su zama salihai, suna yi wa dukan mutane matuƙar tawali’u.

3 Mu kanmu ma dā can mun yi wauta, mun kangare, an ɓad da mu, mun jarabta da muguwar sha’awa da nishaɗi iri iri, mun yi zaman ƙeta da hassada, mun zama abin ƙi, mu kuma mun ƙi waɗansu.

4 Amma sa’ad da alherin Allah Mai Cetonmu da ƙaunarsa ga ‘yan adam suka bayyana,

5 sai ya cece mu, ba don wani aikin adalci da mu muka yi ba, a’a, sai dai domin jinƙan nan nasa, albarkacin wankan nan na sāke haihuwa, da kuma sabuntawar nan ta Ruhu Mai Tsarki,

6 wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Almasihu Mai Cetonmu.

7 Wannan kuwa domin a kuɓutar da mu bisa ga alherinsa ne, mu kuma zama magāda masu bege ga rai madawwami.

8 Maganar nan tabbatacciya ce.

Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa ƙwarai, don waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su himmantu ga aiki nagari, waɗannan abubuwa kuwa masu kyau ne, masu amfani kuma ga mutane.

9 Amma ka yi nesa da gardandamin banza, da ƙididdigar asali, da husuma, da jayayya a kan Shari’a, domin ba su da wata riba, aikin banza ne kuma.

10 Mutumin da yake sa tsattsaguwa kuwa, in ya ƙi kula da gargaɗinka na farko da na biyu, to, sai ka fita sha’aninsa.

11 Ka dai sani irinsa ɓatacce ne, mai yin zunubi, shi kansa ma ya sani haka yake.

Waɗansu Umarnai

12 Sa’ad da na aiko Artimas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi matuƙar, ƙoƙari ka zo wurina a Nikafolis, don na yi niyyar cin damuna a can.

13 Ka yi himmar taimakon Zinas, masanin shari’a, da Afolos, su kamo hanya, ka kuma tabbata ba abin da ya gaza musu.

14 Jama’armu su koyi himmantuwa ga aikin kirki don biyan bukatun matsattsu, kada su zama marasa amfani.

Sa Albarka

15 Duk waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gayar mini da masoyanmu, masu bangaskiya.

Alheri yă tabbata a gare ku, ku duka.