TIT 2

Koyar da Kyakkyawar Koyarwa

1 Amma kai kam, sai ka faɗi abin da ya dace da sahihiyar koyarwa.

2 Dattawa su kasance masu kamunkai, natsattsu, mahankalta, masu sahihiyar bangaskiya, da ƙauna, da kuma jimiri.

3 Haka kuma, manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke, ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyar da kyakkyawan abu,

4 ta haka su koya wa mata masu ƙuruciya su so mazansu da ‘ya’yansu,

5 su kuma kasance natsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah.

6 Haka kuma, ka gargaɗi samari su yi kamunkai.

7 Kai ma sai ka zama gurbi na aiki nagari ta kowace hanya, da koyarwarka kana nuna rashin jirkituwa, da natsuwa,

8 da kuma sahihiyar maganar da ba za a kushe mata ba, don a kunyata abokan hamayya, su rasa hanyar zarginmu.

9 Bayi su yi biyayya ga iyayengijinsu, su kuma gamsar da su ta kowane hali. Kada su yi tsayayya,

10 ko taɓe-taɓe, sai dai su riƙi amana sosai, don su ƙawatar da koyarwar Allah Mai Cetonmu ta kowane hali.

11 Alherin Allah ya bayyana saboda ceton dukkan mutane,

12 yana koya mana mu ƙi rashin bin Allah da mugayen sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyar nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah,

13 muna sauraron cikar begen nan mai albarka, wato bayyanar ɗaukakar Allahnmu Mai Girma, Mai Cetonmu Yesu Almasihu,

14 wanda ya ba da kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama’a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.

15 Ka yi ta sanar da waɗannan abubuwa, kana gargaɗar da su, kana tsawatarwa da ƙaƙƙarfan umarni. Kada ka yarda kowa yă raina ka.