GAL 4

1 Ana nufin, magaji, muddin yana yaro bai fi bawa ba, ko da yake yana da mallakar dukkan kome.

2 A hannun iyayen goyo da wakilai yake har zuwa ranar da mahaifinsa ya sa.

3 Haka yake a gare mu, wato sa’ad da muke kamar yara, a cikin ƙangin bautar al’adun duniya muke.

4 Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari’a,

5 domin ya fanso waɗanda suke a ƙarƙashin Shari’a, a mai da mu a matsayin ‘ya’yan Allah.

6 Tun da yake ku ‘ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, yana kira, “Ya Abba! Uba!”

7 Don haka, kai ba bawa ba ne kuma, amma ɗa ne. Da yake ɗa ne kuma, to, magāji ne bisa ga ikon Allah.

Alhinin Bulus a kan Masu Bangaskiya

8 Dā da ba ku san Allah ba, kuna bauta wa waɗansu gumaka, waɗanda ga ainihi ba a bakin kome suke ba.

9 Amma a yanzu da kuka san Allah, ko ma dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sāke komawa a kan raunanan al’adu marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu?

10 Ga shi, al’adun ranaku, da na watanni, da na lokatai, da na shekaru ba sa wuce ku!

11 Amma kun ba ni tsoro, kada ya zamana na yi wahala a kanku a banza!

12 Ina roƙonku, ya ku ‘yan’uwana, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma in zama kamar yadda kuke. Ba ku taɓa yi mini wani laifi ba.

13 Kun dai sani a dalilin rashin lafiyata ne na yi muku bishara a zuwana na fari.

14 Ko da yake rashin lafiyata ta hana ku sukuni, duk da haka ba ku nuna mini raini ko ƙyama ba, sai dai kuka yi na’am da ni kamar wani mala’ikan Allah, ko ma Almasihu Yesu kansa.

15 To, ina daɗin nan da kuka ji a game da ni? Don na shaide ku a kan lalle da mai yiwuwa ne da kun ƙwaƙule idanunku kun ba ni!

16 Ashe, wato na zama abokin gābarku ne don na gaya muku gaskiya?

17 Waɗannan suna habahaba da ku, amma ba da kyakkyawar niyya ba. Niyyarsu su raba ku da mu, don su ma ku yi habahaba da su.

18 Ai, in da kyakkyawar niyya, abu ne mai kyau koyaushe a yi habahaba da mutum, ba sai ina tare da ku kaɗai ba.

19 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har Almasihu ya siffatu a zuciyarku!

20 Da ma a ce ina tare da ku a yanzu in sauya muryata! Gama na ruɗe a kan sha’aninku.

Ishara da Hajaratu da Saratu

21 Ku gaya mini, ku da kuke son Shari’a ta yi iko da ku, ba kwa sauraron Sharia ne?

22 Domin a rubuce yake, Ibrahim yana da ‘ya’ya biyu maza, ɗaya ɗan kuyanga, ɗaya kuma ɗan ‘ya.

23 Ɗan kuyangar nan, an haife shi ne bisa ga ɗabi’a, ɗan ‘yar kuwa ta cikar alkawarin ne.

24 Wannan kuwa duk don ishara ne, wato matan nan a kan alkawari biyu suke. Ɗaya tushensa Dutsen Sina’i, mai haihuwar bayi, wato Hajaratu ke nan.

25 To, ai, Hajaratu Dutsen Sina’i ce a ƙasar Larabawa. Ita ce kwatancin Urushalima ta yanzu, don ita da ‘ya’yanta duk a bauta suke.

26 Amma Urushalima ta sama, ai ‘ya ce, ita ce kuma uwarmu.

27 Domin a rubuce yake cewa,

“ki yi farin ciki, ya ke bakarariya da ba kya haihuwa,

Ki ɗauki sowa, ke da ba kya naƙuda,

Don yasasshiya ta fi mai miji yawan ‘ya’ya.”

28 To, ‘yan’uwa, mu ma ‘ya’yan alkawari ne kamar Ishaku.

29 Kamar yadda dā, shi da aka haifa bisa ga ɗabi’a ya tsananta wa wanda aka haifa bisa ga ikon Ruhun, haka a yanzu ma yake.

30 Amma me Nassin ya ce? “Ka kori kuyangar da ɗanta, don ko kaɗan ɗan kuyangar ba zai ci gādo tare da ɗan ‘ya ba.”

31 Saboda haka ‘yan’uwa, mu ba ‘ya’yan kuyanga ba ne, na ‘ya ne.