GAL 5

Ku Dāge a Cikin ‘Yanci

1 Almasihu ya ‘yanta mu, ‘yantawar gaske. Don haka sai ku dāge, kada ku sāke sarƙafewa a cikin ƙangin bauta.

2 To, ni Bulus, ina gaya muku, in kuna yarda a yi muku kaciya, Almasihu ba zai amfane ku kome ba ke nan.

3 Ina sāke tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari’a.

4 Ku da kuke neman kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari’a, kun katse daga Almasihu ke nan, kun noƙe daga alherin Allah.

5 Gama mu, ta wurin ikon Ruhu, muke ɗokin cikar begen nan namu na samun adalcin Allah saboda bangaskiya.

6 In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.

7 Dā, ai, kuna ci gaba sosai. Wane ne ya hana ku bin gaskiya?

8 Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne.

9 Ai, ɗan yisti kaɗan, yake game dukkan curin gurasa.

10 Na dai amince da ku a cikin Ubangiji, ba za ku bi wani ra’ayi dabam da nawa ba. Wannan da yake ta da hankalinku kuwa zai sha hukunci, ko shi wane ne.

11 Amma ‘yan’uwa, in da har yanzu wa’azin yin kaciya nake yi, to, don me har yanzu ake tsananta mini? In da haka ne, ashe, an kawar da hamayyar da gicciyen Almasihu yake sawa ke nan!

12 Da ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su mai da kansu babanni!

13 Ya ku ‘yan’uwa, don ‘yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da ‘yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna.

14 Don duk Shari’a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

15 Amma in kuna cin naman juna, ku mai da hankali fa, hanyar hallaka juna ke nan.

Albarkar Ruhu da Halin Mutuntaka

16 Maganata ita ce, ku yi zaman Ruhu, ba kuwa za ku biye wa halin mutuntaka ba.

17 Don halin mutuntaka gāba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gāba da halin mutuntaka. Waɗannan biyu gāba suke yi da juna, har ba kwa iya yin abin da kuke so.

18 In Ruhu ne yake bi da ku, ashe, Shari’a ba ta da iko da ku, ke nan.

19 Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci, da aikin lalata, da fajirci,

20 da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya,

21 da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina faɗakar da ku kamar yadda na faɗakar da ku a dā, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba.

22 Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,

23 da tawali’u da kuma kamunkai. Masu yin irin waɗannan abubuwa, ba dama shari’a ta kama su.

24 Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha’awace-sha’awace iri iri.

25 In dai rayuwar tamu ta Ruhu ce, to, sai mu tafiyar da al’amuranmu ta wurin ikon Ruhu.

26 Kada mu zama masu homa, muna tsokanar juna, muna yi wa juna hassada.