HAB 1

Damuwar Habakuk a kan Rashin Gaskiya

1 Jawabin da annabi Habakuk ya hurta ke nan.

2 Ya Ubangiji, ina ta kukan neman taimako,

Amma ka ƙi ji, sai yaushe za ka ji?

Ina kuka a gare ka saboda zalunci,

Amma ba ka yi taimako ba.

3 Me ya sa ka sa ni in ga mugunta,

In kuma dubi wahala?

Hallaka da zalunci suna a gabana.

Jayayya da gardama sun tashi.

4 Ba a bin doka,

Shari’a kuma ba ta aiki.

Mugaye sun fi adalai yawa nesa,

Don haka shari’a tana tafe a karkace.

Kaldiyawa Za Su Hori Yahuza

5 Ubangiji ya ce,

“Ka duba cikin al’umman duniya! Ka gani!

Ka yi al’ajabi! Ka yi mamaki!

Gama zan yi aiki a kwanakinka,

Ko an faɗa maka ba za ka gaskata ba.

6 Ga shi, ina tā da Kaldiyawa,

Al’umman nan mai zafi, mai fitina,

Waɗanda suke tafiya ko’ina a duniya,

Sun ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.

7 Suna da bantsoro da firgitarwa.

Adalcinsu da ikonsu sun danganta ga yadda suke so.

8 “Dawakansu sun fi damisa sauri,

Sun fi kyarketan maraice zafin hali,

Sojojin dawakansu suna zuwa a guje.

Sojojin dawakansu suna zuwa daga nesa,

Sukan tashi kamar gaggafa da sauri don su cinye.

9 “Sun zo don su yi kama-karya.

Ana jin tsoronsu tun ma kafin su zo.

Sun tattara bayi kamar yashi.

10 Sukan yi wa sarakuna ba’a,

Sukan mai da masu mulki abin wasa.

Kowace kagara abin dariya ce a wurinsu,

Sukan tsiba ƙasa, su hau, su cinye ta.

11 Sukan wuce da sauri kamar iska,

Su yi tafiyarsu.

Su masu laifi ne,

Ƙarfinsu shi ne gunkinsu.”

Habakuk Ya Ƙara Kuka ga Ubangiji

12 Ba kai ne madawwami ba?

Ya Ubangiji Allahna Mai Tsarki.

Ba za mu mutu ba.

Ya Ubangiji, kai ne ka sa su su yi hukunci,

Ya dutse, kai ne ka kafa su don su yi horo.

13 Kai mai tsarki ne,

Ka fi ƙarfin ka dubi mugunta.

Kai da ba ka duban laifi.

Me ya sa kake duban marasa imani?

Kana iya shiru sa’ad da mugu yake haɗiye

Mutumin da ya fi shi adalci?

14 Gama ka mai da mutane kamar kifaye a cikin teku,

Kamar abubuwa masu rarrafe da ba su da shugaba.

15 Kaldiyawa sukan kama mutane da ƙugiya,

Sukan jawo su waje da tarunsa,

Sa’an nan su tara su cikin ragarsu,

Su yi murna da farin ciki.

16 Domin haka sukan miƙa hadaya ga tarunsa,

Su ƙona turare ga ragarsu,

Domin su ne suka jawo musu wadata, da abinci mai yawa.

17 Za su ci gaba da juye tarunsa ke nan?

Su yi ta karkashe al’umman duniya ba tausayi?