IRM 1

Kiran Irmiya da Keɓewarsa

1 Maganar Irmiya ɗan Hilkiya ke nan, na cikin firistocin da suke a Anatot, a yankin ƙasar Biliyaminu,

2 wanda Ubangiji ya yi masa magana a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza, a shekara ta goma sha uku ta mulkinsa,

3 da a zamanin Yehoyakim ɗan Yosiya Sarkin Yahuza kuma, har ƙarshen shekara ta goma sha ɗaya ta Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, har zuwa lokacin da aka kai mazaunan Urushalima zaman talala a wata na biyar.

4 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

5 “Na san ka tun kafin a yi cikinka,

Na keɓe ka tun kafin a haife ka,

Na sa ka ka zama annabi ga

al’ummai.”

6 Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah!

Ban san abin da zan faɗa ba,

Gama ni yaro ne.”

7 Amma Ubangiji ya ce mini,

“Kada ka ce kai yaro ne,

Kai dai ka tafi wurin mutanen da zan

aike ka,

8 Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da

kai,

Zan kiyaye ka.

Ni Ubangiji na faɗa.”

9 Sa’an nan Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina, ya ce mini,

“Ga shi, na sa maganata a bakinka.

10 Ga shi, a wannan rana na ba ka iko a

kan al’ummai da mulkoki,

Don ka tumɓuke, ka rusar,

Ka hallakar, ka kaɓantar,

Ka gina, ka dasa.”

11 Sai Ubangiji ya tambaye ni, ya ce, “Irmiya, me ka gani?”

Na amsa, na ce, “Sandan itacen almond.”

12 Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Ka gani sosai, gama zan lura da maganata don in cika ta.”

13 Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce, “Me kuma ka gani?”

Na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, daga wajen arewa kamar za ta jirkice wajen kudu.”

14 Sai Ubangiji ya ce mini, “Daga wajen arewa masifa za ta fito ta auka wa dukan mazaunan ƙasar.

15 Ga shi kuwa, ina kiran dukan kabilan mulkokin arewa, za su kuwa zo su kafa gadajen sarautarsu a ƙofofin Urushalima, su kewaye dukan garukanta da dukan sauran biranen Yahuza.

16 Zan hurta hukuncin da zan yi musu saboda dukan muguntarsu, da suka bar bina, suka ƙona turare ga gumaka, suka kuma bauta wa gumakan da suka yi.

17 Amma kai, ka tashi ka sha ɗamara, ka faɗa musu dukan abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu domin kada in tsoratar da kai a gabansu.

18 Ni kuwa, ga shi, yau na maishe ka birni mai kagara, da ginshiƙin ƙarfe, da bangon tagulla ga dukan ƙasar, da sarakunan Yahuza, da shugabanninta, da firistocinta, da mutanen ƙasar.

19 Za su yi gāba da kai, amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, ni Ubangiji na faɗa.”