IRM 2

Ubangiji Ya Ji da Isra’ila da Masu Ridda

1 Ubangiji ya ce mini,

2 in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce,

“Na tuna da amincinki a lokacin

ƙuruciyarki,

Da ƙaunarki kamar ta amarya da

ango.

Yadda kika bi ni a cikin jeji, da a

ƙasar da ba a shuka ba.

3 Isra’ila tsattsarka ce ta Ubangiji,

Nunar fari ta girbina.

Dukan waɗanda suka ci daga cikinki

sun yi laifi,

Masifa za ta auko miki.

Ni Ubangiji, na faɗa.”

4 Ku ji jawabin Ubangiji, ku zuriyar Yakubu, ku dukan kabilan Isra’ila.

5 Ubangiji ya ce,

“Wane laifi ne na yi wa kakanninku,

Da suka bar bina?

Suka bauta wa gumaka marasa

amfani,

Su kuma suka zama marasa amfani.

6 Ba su kula da ni ba,

Ko da yake na cece su daga ƙasar

Masar.

Na bi da su a cikin hamada,

A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai,

Busasshiya mai yawan hatsari,

Ba a bi ta cikinta,

Ba wanda yake zama cikinta kuma.

7 Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi,

Don su more ta su ci amfaninta,

Amma da suka shiga, sun ƙazantar

mini da ita,

Suka sa ƙasar da na gādar musu ta

zama abar ƙyama.

8 Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina Ubangiji

Yake?’ ba.

Masanan shari’a ba su san ni ba.

Masu mulki sun yi mini laifi,

Annabawa sun yi annabci da sunan

Ba’al,

Sun bi waɗansu abubuwa marasa

amfani.”

Shari’ar da Ubangiji yake Yi wa Mutanensa

9 “Domin haka, ni Ubangiji zan

gabatar da ku gaban shari’a,

Ku da ‘ya’yanku, da ‘ya’yan

‘ya’yanku, wato jikokinku.

10 Ku haye zuwa tsibirin Kittim wajen

yamma, ku gani,

Ku aika zuwa Kedar wajen gabas, ku

duba da kyau,

A dā an taɓa yin wani abu haka?

11 Akwai wata al’umma da ta taɓa

sāke gumakanta

Ko da yake su ba kome ba ne?

Amma mutanena sun sauya darajarsu

da abin da ba shi da rai.

12 Sammai, ku girgiza saboda wannan,

ku razana,

Ku yi shiru, ni Ubangiji na faɗa.

13 Mutanena sun yi zunubi iri biyu,

Sun rabu da ni, ni da nake

maɓuɓɓugar ruwan rai,

Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa,

hudaddu,

Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba.

14 “Isra’ila ba bawa ba ne, ba a kuma

haife shi bawa ba,

Amma me ya sa ya zama ganima?

15 Zakuna suna ruri a kansa,

Suna ruri da babbar murya.

Sun lalatar da ƙasarsa,

Garuruwansa sun lalace,

Ba wanda yake zaune cikinsu.

16 Mutanen Memfis kuma da na

Tafanes sun fasa ƙoƙwan kansa.

17 Ya Isra’ila, kai ne ka jawo wa kanka

wannan,

Da ka rabu da Ubangiji Allahnka,

Sa’ad da ya bishe ka a hanya.

18 Wace riba ka samu, har da ka tafi

Masar,

Don ka sha ruwan Kogin Nilu?

Wace riba ka samu, har da ka tafi

Assuriya,

Don ka sha ruwan Kogin

Yufiretis?

19 Muguntarka za ta hore ka,

Riddarka kuma za ta hukunta ka.

Sa’an nan za ka sani, ka kuma

gane,

Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a gare

ka

Ka rabu da Ubangiji Allahnka,

Ba ka tsorona a zuciyarka.

Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna na

faɗa.”

Isra’ila Ya Ƙi Yi wa Ubangiji Biyayya

20 “Ya Isra’ila, tun da daɗewa, ka ƙi

yarda

Ubangiji ya mallake ka,

Ka ƙi yin biyayya da ni,

Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’

Amma ka yi karuwanci a kan

kowane tudu,

Da kowane ɗanyen itace.

21 Na dasa ka kamar zaɓaɓɓiyar

kurangar inabi, zaɓaɓɓen iri mafi

kyau.

Ta yaya ka lalace haka ka zama

rassan kurangar inabi ta jeji,

Waɗanda ba zan yarda da su ba?

22 Ko da za ka yi wanka da sabulun

salo,

Ka yi amfani da sabulu mai yawa,

Duk da haka zan ga tabban

zunubanka.

Ni Ubangiji Allah na faɗa.

23 Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar da

kanka ba,

Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba’al ba?

Ka duba hanyarka ta zuwa cikin

kwari, ka san abin da ka yi.

Kana kama da taguwa, mai yawon

neman barbara.

24 Kamar jakar jeji kake, wadda take

son barbara,

Wadda take busar iska,

Sa’ad da take son barbara, wa zai iya

hana ta?

Jakin da take sonta, ba ya bukatar

wahalar da kansa

Gama a watan barbararta za a same

ta.

25 Kai Isra’ila, kada ka bar ƙafafunka

ba takalma,

Kada kuma ka bar maƙogwaronka

ya bushe.

Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani,

Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwa

zan bi.’

26 “Kamar yadda ɓarawo yakan sha

kunya sa’ad da aka kama shi,

Haka nan mutanen Isra’ila za su sha

kunya,

Da su, da sarakunansu, da

shugabanninsu,

Da firistocinsu, da annabawansu.

27 Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai ne

mahaifinmu.’

Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, ka

haife mu.’

Gama sun ba ni baya, ba su fuskance

ni ba.

Amma sa’ad da suke shan wahala,

sukan ce,

‘Ka zo ka taimake mu.’

28 Ina gumakan da kuka yi wa

kanku?

Bari su tashi in sun iya cetonku

lokacin wahalarku.

Yahuza, yawan gumakanku sun kai

Yawan garuruwanku.

29 Ni Ubangiji, ina tambayarku, ‘Wace

ƙara kuke da ita game da ni?’

Kun yi mini tawaye dukanku.

30 Na hori ‘ya’yanku, amma a banza, ba

su horu ba,

Kun kashe annabawanku da takobi

kamar mayunwacin zaki.

31 Ya ku mutanen zamanin nan, ku

saurari maganata.

Na zamar wa Isra’ila jeji? Ko ƙasar

da take da kurama?

Don me fa mutanena suke cewa,

‘Mu ‘yantattu ne,

Ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?

32 Budurwa ta manta da kayan

kwalliyarta?

Ko kuwa amarya ta manta da kayan

adonta?

Amma mutanena sun manta da ni

kwanaki ba iyaka.

33 Kun sani sarai yadda za ku yi ku

farauci masoya,

Har mugayen mata ma, kun koya

musu hanyoyinku.

34 Tufafinku sun ƙasantu da jinin

marasa laifi,

Waɗanda ba ku same su suna fasa

gidajenku ba.

Amma duk da haka kuna cewa,

35 ‘Ba mu da laifi, hakika kuwa,

Ubangiji bai yi fushi da mu ba.’

Amma ni Ubangiji zan hukunta ku,

Domin kun ce ba ku yi zunubi ba.

36 Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya,

Sai ku yi nan ku yi can?

Masar za ta kunyata ku kamar yadda

Assuriya ta yi.

37 Da hannuwanku a kā za ku komo

daga Masar don kunya.

Gama waɗanda kuke dogara gare su,

ni Ubangiji, na ƙi su,

Ba za ku yi arziki tare da su ba.”