IRM 13

Misali da Abin Ɗamara

1 Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, ya ce, “Tafi ka sayo lilin na yin ɗamara, ka sha ɗamara da shi kada kuwa ka tsoma shi a ruwa.”

2 Sai na sayo abin ɗamara kamar yadda Ubangiji ya ce, na sha ɗamara da shi.

3 Ubangiji kuma ya sāke yin magana da ni sau na biyu,

4 ya ce, “Ka ɗauki abin ɗamara da ka sayo, wanda ka ɗaura, ka tafi Kogin Yufiretis, ka ɓoye shi a cikin kogon dutse.”

5 Sai na tafi, na ɓoye shi a Yufiretis kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.

6 Bayan an ɗan daɗe, sai Ubangiji ya ce mini, “Tashi, ka tafi Yufiretis, ka ɗauko abin ɗamara wanda na umarce ka ka ɓoye a can.”

7 Sai na tafi Yufiretis, na haƙa na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi. Amma abin ɗamara ya lalace, ba shi da sauran amfani.

8 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

9 “Haka zan lalatar da alfarmar Yahuza da yawan alfarmar Urushalima.

10 Wannan muguwar jama’a, wadda ta ƙi jin maganata, wadda ta taurare, ta bi son zuciyarta, ta kuma bi gumaka ta bauta musu, ta yi musu sujada, za ta zama kamar abin ɗamaran nan, wanda ba shi da sauran amfani.

11 Gama kamar yadda abin ɗamara yakan kame tam a gindin mutum, haka na sa dukan mutanen Isra’ila da dukan mutanen Yahuza su manne mini domin su zama jama’a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.”

Misali da Tulun Ruwan Inabi

12 “Sai ka faɗa musu wannan magana cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na Isra’ila na ce, a cika kowane tulu da ruwan inabi.’ Su kuwa za su ce maka, sun sani sarai za a cika kowane tulu da ruwan inabi.

13 Sa’an nan za ka faɗa musu, Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan sa dukan mazaunan ƙasar su bugu da ruwan inabi, wato sarakunan da suka hau gadon sarautar Dawuda, da firistoci, da annabawa, da dukan mazaunan Urushalima.

14 Zan sa su kara da junansu, iyaye maza da ‘ya’yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi, ko juyayi, ko jinƙai ba za su sa in fasa hallaka su duka ba.’ ”

Yahuza bai Tuba ba, za a Kai shi Zaman Talala

15 Ku kasa kunne, ku ji,

Kada ku yi girmankai, gama

Ubangiji ya yi magana.

16 Ku girmama Ubangiji Allahnku,

Kafin ya kawo duhu,

Kafin kuma ƙafafunku su yi tuntuɓe

a kan dutse, da duhu duhu,

Sa’ad da kuke neman haske, sai ya

maishe shi duhu,

Ya maishe shi duhu baƙi ƙirin.

17 Amma idan ba za ku ji ba,

Raina zai yi kuka a ɓoye saboda

girmankanku,

Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za su

zub da hawaye,

Domin an kai garken Ubangiji zuwa

bauta.

18 Ubangiji ya ce wa Irmiya,

“Ka faɗa wa sarki da sarauniya,

uwarsa, su sauka daga gadon

sarautarsu,

Domin an tuɓe kyakkyawan rawanin

sarautarsu daga kansu.

19 An kulle biranen Negeb,

Ba wanda zai buɗe su,

Yahuza duka an kai ta zaman dole,

Dukanta an kai ta zaman dole.

20 “Ku ta da idanunku, ku ga waɗanda

suke zuwa daga arewa!

Ina kyakkyawan garken nan da aka

ba ku?

21 Me za ku ce sa’ad da aka naɗa muku

shugabanni,

Waɗanda ku da kanku kuka koya

musu, suka zama abokanku?

Ashe, azabai ba za su auko muku ba

Kamar yadda sukan auko wa mace

mai naƙuda?

22 Idan kun ce a zuciyarku,

‘Me ya sa waɗannan abubuwa suka

same mu?’

Saboda yawan zunubanku ne,

Shi ya sa an tone tsiraicinku,

Aka wahalshe ku.

23 Mutumin Habasha zai iya sāke

launin fatar jikinsa?

Ko kuwa damisa za ta iya sāke

dabbare-dabbarenta?

Idan haka ne, ku kuma za ku iya yin

nagarta,

Ku da kuka saba da yin mugunta.

24 Zan warwatsar da ku

Kamar yadda iskar hamada take

watsar da ƙaiƙayi.”

25 Ubangiji ya ce, “Wannan shi ne

rabonku,

Rabon da na auna muku, ni Ubangiji

na faɗa.

Domin kun manta da ni, kun dogara

ga ƙarairayi,

26 Ni kaina kuma zan kware muku

suturarku ta rufe fuskarku

Don a ga tsiraicinku.

27 Na ga abubuwanku masu

banƙyama,

Wato zinace-zinacenku, da haniniya

kamar dawakai,

Da muguwar sha’awarku ta

karuwanci a kan tuddai da filaye,

Ya Urushalima, taki ta ƙare!

Har yaushe za a tsarkake ki?”