IRM 14

Babban Fari

1 Maganar da Ubangiji ya yi wa Irmiya a kan fari ke nan,

2 “Yahuza tana makoki,

Ƙofofin biranenta suna lalacewa,

Mutanenta suna kwance a ƙasa,

suna makoki,

Urushalima tana kuka da babbar

murya.

3 Manyan mutanenta sun aiki

barorinsu su ɗebo ruwa.

Da suka je maɓuɓɓuga, sai suka

tarar ba ruwa.

Sai suka koma da tulunansu

haka nan,

An kunyatar da su, an ƙasƙantar

da su,

Suka lulluɓe kansu don kunya.

4 Saboda ƙasar ta bushe,

Tun da ba a yi ruwa a kanta ba,

Manoma sun sha kunya,

Suka lulluɓe kansu don kunya.

5 Barewa ma a saura takan gudu,

Ta bar ɗanta sabon haihuwa,

Domin ba ciyawa.

6 Jakunan jeji suna tsaye a kan tuddan

da ba ciyawa,

Suna haki kamar diloli,

Idanunsu ba su gani

Domin ba abinci.”

7 Irmiya ya ce,

“Ko da yake zunubanmu su ne

shaidunmu,

Ya Ubangiji, ka yi taimako saboda

sunanka!

Gama kāsawarmu ta yi yawa,

Domin mun yi maka zunubi.

8 Ya kai, wanda kake begen Isra’ila,

Mai Cetonta a lokacin wahala,

Ƙaƙa ka zama kamar baƙo a ƙasar?

Kamar matafiyi wanda ya kafa

alfarwarsa a gefen hanya don ya

kwana, ya wuce?

9 Ƙaƙa ka zama kamar wanda bai san

abin da zai yi ba,

Kamar jarumin da ya kasa yin

ceto?

Duk da haka, ya Ubangiji, kana nan

a tsakiyarmu.

Da sunanka ake kiranmu,

Kada ka bar mu!”

10 Haka Ubangiji ya ce a kan waɗannan mutane, “Sun cika son yawaceyawace, ba su iya zama wuri ɗaya, don haka ni Ubangiji, ban yarda da su ba, zan tuna da laifofinsu in hukunta zunubansu.”

11 Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu’a domin lafiyar jama’an nan.

12 Ko da sun yi azumi, ba zan ji kukansu ba, ko da sun miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta sha, ba zan karɓe su ba. Amma zan hallaka su da takobi, da yunwa, da annoba.”

13 Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ga shi, annabawa sun faɗa musu, sun ce, ‘Ba za ku ga takobi ko yunwa ba, amma zan ba ku dawwamammiyar salama a wannan wuri.’ ”

14 Ubangiji kuwa ya ce mini, “Annabawa, annabcin ƙarya suka yi da sunana. Ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba, ban kuma yi magana da su ba. Annabcin da suke yi muku na wahayin ƙarya ne, dubar da suke yi marar amfani ce, tunaninsu ne kawai.

15 Domin haka ga abin da ni Ubangiji na ce a kan annabawan da suke yin annabci da sunana, ko da yake ban aike su ba, waɗanda suke cewa, ‘Takobi da yunwa ba za su shigo ƙasan nan ba.’ Za a hallaka su da takobi da yunwa.

16 Mutanen da suka yi wa annabci, za a jefar da su waje a kan titunan Urushalima, a karkashe su da yunwa da takobi, ba wanda zai binne su, da su, da matansu, da ‘ya’yansu mata da maza. Zan sa muguntarsu ta koma kansu.

17 “Irmiya, ka faɗa wa mutanen baƙin

ciki da ya same ka,

Ka ce, ‘Bari idanuna su yi ta zub da

hawaye dare da rana,

Kada su daina, saboda an buge

budurwa, ‘yar jama’ata,

An yi mata babban rauni da dūka

mai tsanani.

18 Idan na tafi cikin saura,

Sai in ga waɗanda aka kashe da

takobi!

Idan kuma na shiga birni,

Sai in ga waɗanda suke ta fama da

yunwa!

Gama annabi da firist, sai harkarsu

suke ta yi a ƙasar,

Amma ba su san abin da suke yi

ba.’ ”

Mutane Sun Roƙi Ubangiji

19 “Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum?

Ranka kuma yana jin ƙyamar

Sihiyona ne?

Me ya sa ka buge mu, har da ba za

mu iya warkewa ba?

Mun zuba ido ga samun salama,

amma ba wani abin alheri da ya

zo.

Mun kuma sa zuciya ga warkewa,

amma sai ga razana.

20 Mun san muguntar da muka yi, ya

Ubangiji,

Da wadda kakanninmu suka yi,

Gama mun yi maka zunubi.

21 Saboda darajar sunanka, kada ka

wulakanta mu,

Kada kuma ka ƙasƙantar da

darajar kursiyinka,

Ka tuna da alkawarin da ka yi

mana,

Kada ka ta da shi.

22 A cikin gumakan al’ummai akwai

mai iya sa a yi ruwa?

Sammai kuma su yi yayyafi?

Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji

Allahnmu?

Domin haka a gare ka muke sa

zuciya,

Gama kai ne mai yin waɗannan

abubuwa duka.”