IRM 22

1 Haka Ubangiji ya faɗa, “Ka tafi ka gangara zuwa gidan Sarkin Yahuza, ka faɗi wannan magana a can,

2 ka ce, ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya Sarkin Yahuza, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda kai da barorinka, da mutanenka waɗanda suke shiga ta ƙofofin nan.

3 Haka Ubangiji ya ce, ka yi gaskiya da adalci, ka ceci wanda ake masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka cuci baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, kada kuma ka zubar da jinin marasa laifi a wannan wuri.

4 Hakika idan ka kiyaye wannan magana, sa’an nan sarakunan da za su zauna a kan gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan gida da karusai da dawakai, su da barorinsu da jama’arsu.

5 Amma idan ba ka kula da waɗannan zantuttuka ba, na rantse da zatina,’ in ji Ubangiji, ‘wannan fāda ta zama kufai.’ ”

6 Abin da Ubangiji ya ce ke nan a kan fādar Sarkin Yahuza,

“Kyanta kamar Gileyad take a gare

ni,

Kamar kuma ƙwanƙolin Lebanon.

Duk da haka zan maishe ta hamada,

Birnin da ba kowa ciki.

7 Zan shirya waɗanda za su hallaka

ta.

Kowannensu da makamansa,

Za su sassare zaɓaɓɓun itatuwan

al’ul ɗinta, a jefa su a wuta.

8 “Al’ummai masu yawa za su wuce ta gefen wannan birni, kowane mutum zai ce wa maƙwabcinsa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’

9 Za su amsa, su ce, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada ga gumaka, suka bauta musu.’ ”

10 Ku mutanen Yahuza, kada ku yi

kuka saboda sarki Yosiya,

Kada ku yi makokin rasuwarsa,

Amma ku yi kuka ƙwarai saboda

ɗansa Yehowahaz.

Sun ɗauke shi, sun tafi da shi, ba zai

ƙara komowa ba,

Ba kuma zai ƙara ganin ƙasar da

aka haife shi ba.

11 Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba.

12 Amma a wurin da suka kai shi zaman talala, a can zai mutu, ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.

13 Kaiton wanda ya gina gidansa ta

hanyar rashin adalci,

Benayensa kuma ta hanyar rashin

gaskiya.

Wanda ya sa maƙwabcinsa ya yi

masa aiki a banza,

Bai ba shi hakkinsa ba.

14 Kaiton wanda ya ce,

“Zan gina wa kaina babban gida

Da waɗansu irin benaye

musamman.”

Ya yi masa tagogi,

Ya manna masa itacen al’ul,

Sa’an nan ya yi masa jan shafe.

15 Kana tsammani kai sarki ne,

Da yake ƙasarka ta itacen al’ul

ce?

Amma ubanka ya ci, ya sha,

Ya yi gaskiya, ya aikata adalci,

Ya kuwa zauna lafiya.

16 Ya biya wa matalauta da masu

bukata hakkinsu,

Ya kuwa yi kyau.

Abin da ake nufi da sanina ke nan,

In ji Ubangiji.

17 Amma ka sa idonka da zuciyarka ga

ƙazamar riba,

Da zubar da jinin marar laifi,

Da yin zalunci da danniya.

18 Domin haka ga abin da Ubangiji ya ce a kan Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza,

“Ba za su yi makoki dominsa ba, ko

su ce,

‘Wayyo ɗan’uwanmu!’ ko, ‘Wayyo

‘yar’uwarmu!’

Ba za su yi makoki dominsa ba, su

ce,

‘Wayyo ubangidanmu!’ ko ‘Wayyo mai martaba!’

19 Za a binne shi kamar jaki,

Za a ja shi a yar a bayan ƙofofin

Urushalima.”

20 Ku haura zuwa Lebanon, ku yi

kuka,

Ku ta da muryarku cikin Bashan,

Ku yi kuka daga Abarim,

Gama an hallakar da dukan

ƙaunatattunku.

21 Ubangiji ya yi muku magana a

lokacin wadatarku.

Amma kun ce, “Ba za mu kasa

kunne ba!”

Wannan shi ne halinku tun kuna

samari,

Don ba ku yi biyayya da murya

Ubangiji ba.

22 Iska za ta kwashe shugabanninku,

Za a kai ƙaunatattunku cikin

bauta,

Sa’an nan za ku sha kunya ku ruɗe,

Saboda dukan muguntarku.

23 Ya ku mazaunan Lebanon,

Waɗanda suke zaune cikin itatuwan

al’ul,

Irin nishin da za ku yi sa’ad da azaba

ta same ku,

Azaba ce irin ta mace mai

naƙuda!

24 “Ni Ubangiji na rantse da raina, ko da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, zoben hatimi ne a yatsan hannun damana, duk da haka zan kwaɓe shi,

25 in bashe shi a hannun waɗanda suke neman ransa, da a hannun wanda yake jin tsoronsa, wato Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da Kaldiyawa.

26 Zan jefar da shi da uwarsa a wata ƙasa inda ba a haife shi ba, a can zai mutu.

27 Amma ƙasan nan da suke marmarin komowa cikinta, ba za su koma cikinta ba.”

28 Ashe, Yekoniya kamar fasasshen

tulu yake,

Wanda ba wanda ya kula da shi?

Me ya sa aka watsar da shi da

‘ya’yansa,

A ƙasar da ba su sani ba?

29 Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa!

Ki ji maganar Ubangiji!

30 Haka Ubangiji ya ce,

“Rubuta wannan mutum, marar

‘ya’ya.

Mutumin da ba zai yi albarka a duk

kwanakinsa ba.

Gama ba wani daga zuriyarsa

Da zai gāji gadon sarautar Dawuda,

Ko ya yi mulki kuma a Yahuza.”