IRM 23

Komowar waɗanda suka Ragu

1 “Taku ta ƙare! Makiyayan da suka lalatar, suka kuma warwatsar da tumakin makiyayanta!” In ji Ubangiji.

2 Haka Ubangiji Allah na Isra’ila ya faɗa a kan makiyayan jama’arsa. “Kun warwatsar da garkena kun kore su, ba ku lura da su ba. Ni ma haka zan yi da ku saboda muguntarku, ni Ubangiji na faɗa.

3 Sa’an nan zan tattaro sauran garkena daga wuraren da aka warwatsa su, zan komo da su cikin garkensu, zan sa su hayayyafa su riɓaɓɓanya.

4 Zan sa makiyayan da za su lura da su. Ba kuwa za su ƙara jin tsoro, ko razana ba, ba kuma wanda zai ɓace, ni Ubangiji na faɗa.

5 “Ga shi, ni Ubangiji na ce, kwanaki

suna zuwa,

Sa’ad da zan tsiro da wani mai adalci

daga zuriyar Dawuda

Wanda zai ci sarauta.

Zai yi sarauta da hikima,

Zai aikata abin da yake daidai a

ƙasar.

6 A zamaninsa za a ceci Yahuza,

Isra’ila kuwa za ta zauna lafiya.

Sunan da za a kira shi da shi ke

nan,

‘Ubangiji Adalcinmu.’

7 “Saboda haka, ga shi, kwanaki suna zuwa, ni Ubangiji na faɗa, sa’ad da mutane ba za su ƙara cewa, ‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da jama’ar Isra’ila daga cikin ƙasar Masar ba,’

8 amma za su ce, ‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da zuriyar Isra’ila daga ƙasar arewa, daga kuma dukan ƙasashen da ya warwatsa su!’ Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu ta kansu.”

Jawabi a kan Annabawan Ƙarya

9 A kan annabawa kuwa, zuciyata ta

karai,

Dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa,

Saboda Ubangiji da kuma maganarsa

mai tsarki.

Na zama kamar mashayi, wanda ya

bugu da ruwan inabi,

10 Gama ƙasar cike take da mazinata,

Saboda la’ana, ƙasar za ta yi

makoki,

Wuraren kiwo na jeji sun bushe,

Manufarsu mugunta ce,

Ba su mori ƙarfinsu a inda ya

kamata ba.

11 “Annabi da firist, dukansu biyu

marasa tsoron Allah ne,

Har a cikin Haikalina na tarar da

muguntarsu.”

Ubangiji ya faɗa.

12 “Saboda haka hanyarsu za ta zama

da santsi da duhu,

Inda za a runtume su, su fāɗi.

Gama zai kawo musu masifa a

shekarar da za su sha

hukuncinsu.”

Ubangiji ya faɗa.

13 “A cikin annabawan Samariya,

Na ga abu marar kyan gani.

Da sunan Ba’al suke yin annabci,

Suna ɓad da jama’ata Isra’ila

14 Amma cikin annabawa na

Urushalima,

Na ga abin banƙyama.

Suna yin zina, suna ƙarya,

Suna ƙarfafa hannuwan masu aikata

mugunta,

Saboda haka ba wanda ya juya ga

barin muguntarsa,

Dukansu suna kama da Saduma,

Mazaunanta kuwa kamar

Gwamrata.”

15 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce a kan annabawa,

“Ga shi, zan ciyar da su da abinci

mai ɗaci,

In shayar da su da ruwan dafi.

Daga wurin annabawan Urushalima

Rashin tsoron Allah ya fito ya

mamaye dukan ƙasar.”

16 Ubangiji Mai Runduna ya ce wa

mazaunan Urushalima,

“Kada ku kasa kunne ga maganar

annabawa,

Gama sukan cika kunnuwanku da

ƙarairayi.

Suna faɗar ganin damarsu,

Ba faɗar Ubangiji ba.

17 Suna ta faɗa wa waɗanda suke raina

maganar Ubangiji cewa,

‘Za ku zauna lafiya!’

Ga kowane mai bin nufin tattaurar

zuciyarsa,

‘Ba masifar da za ta same ka.’ ”

18 Irmiya ya ce, “Gama wane ne a cikin annabawan nan ya taɓa neman shawarar Ubangiji don ya fahimci maganarsa, ko kuwa wane ne ya taɓa kasa kunne don ya ji maganarsa?

19 Ga shi, hadirin hasalar Ubangiji ya

taso,

Kamar iskar guguwa,

Zai tashi a bisa kan mugaye.

20 Ubangiji ba zai huce ba,

Sai ya aikata nufin zuciyarsa.

Amma sai daga baya za ku gane

sarai.”

21 Ubangiji ya ce,

“Ni ban aiki waɗannan annabawa

ba,

Duk da haka sun tafi,

Ban kuwa yi musu magana ba,

Amma sun yi annabci.

22 Amma da a ce sun tsaya cikin

shawarata,

Da sun yi shelar maganata ga

jama’ata,

Da sun juyar da su daga muguwar

hanyarsu,

Da mugayen ayyukansu.

23 “Ni Allah na kusa ne kaɗai,

Banda na nesa?” In ji Ubangiji.

24 “Mutum ya iya ɓoye kansa a wani

lungu

Inda ba zan iya ganinsa ba?” In ji

Ubangiji.

“Ashe, ban cika sammai da duniya

ba?

25 Na ji abin da annabawan nan suka ce, su da suke annabcin ƙarya da sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki!’

26 Har yaushe ƙarya za ta fita daga zuciyar annabawan nan masu annabcin ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗin da yake a zuciyarsu?

27 Suna zaton za su sa mutanena su manta da sunana ta wurin mafarkansu da suke faɗa wa junansu, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana saboda Ba’al.

28 Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.

29 Maganata kamar wuta ce, kamar guduma mai farfashe dutse. Ni Ubangiji na faɗa.

30 Domin haka, ga shi, ina gāba da annabawan da suke satar maganata daga wurin junansu. Ni Ubangiji na faɗa.

31 Ina kuma gāba da annabawan da suke faɗar ra’ayin kansu, sa’an nan su ce, ‘Ubangiji ne ya faɗa.’

32 Ina kuma gāba da annabawan da suke annabcin mafarkansu na ƙarya, suna kuwa faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu, saboda rashin hankalinsu. Ni ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan jama’a ba ko kaɗan, ni Ubangiji na faɗa.”

33 “Kai Irmiya, sa’ad da wani mutum daga cikin mutanen nan, ko annabi, ko firist ya tambaye ka cewa, ‘Mece ce nawayar Ubangiji?’ Sai ka ce masa, ‘Ku ne nawayar, zan kuwa rabu da ku,’ ni Ubangiji na faɗa.

34 Idan annabi ko firist, ko wani daga cikin jama’a, ya ce, ‘Nawayar Ubangiji,’ zan hukunta shi duk da iyalin gidansa.

35 Haka kowannenku zai ce wa maƙwabcinsa da ɗan’uwansa, ‘Wace amsa Ubangiji ya bayar? Me Ubangiji ya faɗa?’

36 Amma ba za ku ƙara ambatar nawayar Ubangiji ba, gama maganar kowane mutum za ta zama nawaya, ga shi, kun ɓata maganar Allah mai rai, Ubangiji Mai Runduna, Allahnmu.

37 Haka za ka faɗa wa annabi, ‘Wace amsa Ubangiji ya bayar? Me Ubangiji ya faɗa?’

38 Amma idan kun ce, ‘Nawayar Ubangiji,’ ga abin da ni Ubangiji na ce, tun da yake kun faɗi wannan magana, wato ‘Nawayar Ubangiji,’ alhali kuwa na aika muku cewa, kada ku ce, ‘Nawayar Ubangiji,’

39 saboda haka, hakika zan ɗaga in jefar da ku daga gabana, da ku da birni wanda na ba ku, ku da kakanninku.

40 Zan sa ku zama abin zargi da abin kunya har abada, ba kuwa za a manta da wannan ba.”