IRM 24

Kwando Biyu na ‘Ya’yan Ɓaure

1 Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana’a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.

2 A ɗaya kwandon akwai ɓaure masu kyau, kamar nunan fari. A ɗayan kuwa marasa kyau ne, ba mai iya cinsu.

3 Sai Ubangiji ya ce mini, “Irmiya, me ka gani?”

Sai na ce, “’Ya’yan ɓaure, akwai masu kyau ƙwarai, akwai kuma marasa kyau ƙwarai, har da ba za su ciwu ba.”

4 Sa’an nan Ubangiji ya ce mini,

5 “Haka ni Ubangiji Allah na Isra’ila na ce, kamar kyawawan ɓauren nan, haka nake ganin mutanen Yahuza waɗanda aka kai su bautar talala a ƙasar Kaldiyawa.

6 Zan lura da su da kyau, in kuma komo da su a wannan ƙasa. Zan gina su, ba zan rushe su ba. Zan kafa su, ba zan tumɓuke su ba.

7 Zan ba su zuciyar da za su sani ni ne Ubangiji. Za su kuwa zama jama’ata, ni kuwa zan zama Allahnsu, gama za su komo wurina da zuciya ɗaya.

8 “Ni Ubangiji na ce, zan mai da Zadakiya Sarkin Yahuza, da sarakunansa, da sauran mutanen Urushalima da suka ragu a ƙasar, da mutanen da suka tafi Masar, kamar ruɓaɓɓen ɓauren nan da suka lalace har ba su ciwuwa.

9 Zan maishe su abin ƙyama da masifa ga mulkokin duniya duka. Za su zama abin zargi, da karin magana, da ba’a, da la’ana a dukan wuraren da zan warwatsa su.

10 Zan aika musu da takobi, da yunwa, da annoba har an hallaka su sarai daga cikin ƙasar da na ba su, su da kakanninsu.”