IRM 25

Za a Zama Kufai har Shekara Saba’in

1 A shekara ta huɗu ta mulkin Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi wa Irmiya magana a kan dukan mutanen Yahuza. A shekarar da Nebukadnezzar ya ci sarautar Babila,

2 a shekarar ce, annabi Irmiya ya yi wa dukan mutanen Yahuza da dukan mazaunan Urushalima magana cewa,

3 “Shekaru ashirin da uku ke nan tun daga shekara ta goma sha uku ta mulkin Yosiya, ɗan Amon, Sarkin Yahuza, har zuwa yau, Ubangiji ya yi mini magana, ni kuwa na yi ta faɗa muku, amma ba ku ji ba.

4 Ba ku saurara ba, ba ku kasa kunne don ku ji ba, ko da yake Ubangiji ya yi ta aiko muku da dukan bayinsa annabawa,

5 yana cewa, ‘Sai kowane ɗayanku ya juyo daga mugun halinsa da mugayen ayyukansa don ya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku, ku da kakanninku tun daga zamanin dā har abada.

6 Kada ku bi gumaka, ku bauta musu, ku yi musu sujada, ko ku tsokane ni da ayyukan hannuwanku, sa’an nan ba zan hore ku ba.’

7 Duk da haka ba ku kasa kunne gare shi ba, shi Ubangiji ya faɗa, sai kuka tsokane shi da ayyukan hannuwanku. Wannan kuwa zai cuce ku.

8 “Domin haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Tun da yake kun ƙi yin biyayya da maganata,

9 zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al’umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.

10 Banda haka zan kawar da muryar sowa da ta farin ciki, da ta ango da ta amarya, da amon dutsen niƙa daga gare su. Zan kashe hasken fitilunsu.

11 Ƙasar duka za ta zama kufai marar amfani, waɗannan al’ummai za su bauta wa Sarkin Babila har shekara saba’in.

12 Sa’an nan bayan cikar shekara saba’in ɗin, zan hukunta Sarkin Babila da ƙasarsa, wato ƙasar Kaldiyawa. Zan maishe ta kango har abada, saboda zunubinsa.

13 Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abin da na faɗa gāba da ita. Dukan abin da aka rubuta a wannan littafi, wato dukan abin da Irmiya ya yi annabcinsa gāba da dukan al’umman nan.

14 Al’ummai da yawa da manyan sarakuna za su bautar da su, ni kuwa zan yi musu sakayya bisa ga ayyukan hannuwansu.’ ”

Hukuncin da Allah zai Yi wa Al’ummai

15 Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce mini, “Ka karɓi ƙoƙon ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al’umman da na aike ka gare su, su sha.

16 Za su sha, su yi tangaɗi su yi hauka saboda takobin da zan aiko a cikinsu.”

17 Sai na karɓi ƙoƙon daga wurin Ubangiji, na sa dukan al’umman da Ubangiji ya aike ni gare su, su sha daga cikinsa.

18 Urushalima, da biranen Yahuza, da sarakunanta, da shugabanninta, za su zama kango da abin ƙyama da abin raini, da abin la’ana. Haka yake a yau.

19-26 Ga lissafin sauran da za su sha

ƙoƙon.

Fir’auna Sarkin Masar da kuma

barorinsa, da sarakunansa,

Dukan jama’arsa, da dukan

baƙin da suke tare da su,

dukan sarakunan ƙasar Uz,

dukan sarakunan ƙasar

Filistiyawa, wato Ashkelon, da

Gaza, da Ekron, da saura na

Ashdod,

Edom da Mowab, da ‘ya’yan

Ammon maza,

dukan sarakunan Taya, da dukan

sarakunan Sidon,

dukan sarakunan da suke gaɓar

Bahar Rum da waɗanda suke a

tsibiran tekun,

Dedan, da Tema, da Buz, da

dukan waɗanda suke yi wa

kansu sanƙo,

dukan sarakunan Arabiya,

dukan sarakunan tattarmukan

mutane da suke zaune a

hamada,

dukan sarakunan Zimri, da dukan

sarakunan Elam, da dukan

sarakunan Mediya,

dukan sarakunan arewa, na nesa

da na kusa bi da bi.

Dukan mulkokin da suke fuskar duniya za su sha daga ciki. Daga nan sai Sarkin Babila a bayansu duka, zai sha nasa.

27 “Za ka kuma faɗa musu cewa, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ku sha, ku bugu, ku yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku tashi saboda takobin da zan aiko muku.’

28 Idan kuwa sun ƙi su karɓi ƙoƙon daga hannunka su sha sai ka faɗa musu cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, dole ne ku sha!

29 Gama ga shi, na fara sa masifa ta yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana. To, kuna tsammani ba za a hukunta ku ba? Sai an hukunta ku, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’

30 “Kai Irmiya kuma sai ka yi annabcin dukan waɗannan magana gāba da su, ka faɗa musu cewa,

‘Ubangiji zai yi ruri daga Sama,

Zai yi magana daga wurin zamansa

mai tsarki,

Zai yi wa garkensa ruri da ƙarfi

ƙwarai,

Zai yi ihu kamar masu matse

‘ya’yan inabi,

Zai yi gāba da dukan mazaunan

duniya.

31 Za a ji hayaniya har iyakar duniya,

Gama Ubangiji yana da ƙara game

da al’ummai,

Zai shiga hukunta wa dukan ‘yan

adam,

Zai kashe mugaye da takobi,

Ubangiji ya faɗa.’ ”

32 Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce,

“Ga masifa tana tahowa daga

al’umma zuwa al’umma,

Hadiri kuma yana tasowa daga

dukan manisantan wurare na

duniya.

33 Waɗanda Ubangiji ya kashe a

wannan rana,

Za su zama daga wannan bangon

duniya zuwa wancan.

Ba za a yi makoki dominsu ba,

Ba kuwa za a tattara gawawwakinsu

a binne ba.

Za su zama taki ga ƙasa.

34 “Ku yi makoki, ku yi kuka, ku

makiyaya,

Ku yi ta birgima a cikin toka ku

iyayengijin garke,

Gama ranar da za a yanka ku da

ranar da za a warwatsa ku ta zo,

Za ku fāɗi kamar zaɓaɓɓen kasko.

35 Ba mafakar da ta ragu domin

makiyaya,

Iyayengijin garken ba za su tsira ba.

36 Ji kukan makiyayan,

Da kukan iyayengijin garken,

Gama Ubangiji yana lalatar da wurin

kiwonsu.

37 Garkunan da suke zaune lafiya kuwa,

an yi kaca-kaca da su

Saboda zafin fushin Ubangiji.

38 Ya rabu da wurin ɓuyarsa kamar

zaki,

Gama ƙasarsu ta zama marar

amfani,

Saboda takobin Ubangiji, da kuma

zafin fushinsa.”