IRM 29

Wasiƙar Irmiya Zuwa ga Yahudawan da suke Babila

1 Ga maganar wasiƙar da annabi Irmiya ya aika daga Urushalima zuwa ga dattawa, da firistoci, da annabawa, da dukan mutanen da Nebukadnezzar ya kwaso daga Urushalima zuwa Babila. (

2 Ya rubuta wannan bayan tashin sarki Yekoniya, da uwa tasa, da bābāni, da sarakunan Yahuza, da na Urushalima, da gwanayen aikin hannu, da maƙera daga Urushalima.)

3 Ya aika da wasiƙar ta hannun Elasa ɗan Shafan, da Gemariya ɗan Hilkiya waɗanda Zadakiya Sarkin Yahuza ya aika zuwa Babila, wurin Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Ga abin da wasiƙar ta ce.

4 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce wa dukan waɗanda aka kai bauta, wato waɗanda ya aika da su bauta daga Urushalima zuwa Babila.

5 ‘Ku gina gidaje, ku zauna a ciki, ku dasa gonaki, ku ci amfaninsu.

6 Ku auri mata, ku haifi ‘ya’ya mata da maza. Ku auro wa ‘ya’yanku mata, ku aurar da ‘ya’yanku mata, domin su haifi ‘ya’ya mata da maza, ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.

7 Amma ku nemi zaman lafiyar birni inda na sa aka kai ku zaman talala, ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, gama zaman lafiyar birnin shi ne naku zaman lafiyar.’

8 Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya faɗa. ‘Kada ku yarda annabawanku da malamanku na duba waɗanda suke tare da ku su ruɗe ku, kada ku kasa kunne ga mafarkansu.

9 Gama annabcin da suke yi muku da sunana, ƙarya ne, ni ban aike su ba.’

10 “Ubangiji ya ce, ‘Sa’ad da kuka cika shekara saba’in a Babila, zan ziyarce ku, zan kuwa cika muku alkawarina. Zan komo da ku zuwa wannan wuri.

11 Gama na san irin shirin da na yi muku, ni Ubangiji na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya.

12 Sa’an nan za ku yi kira a gare ni, ku yi addu’a a wurina, zan kuwa ji ku.

13 Za ku neme ni ku same ni, idan kun neme ni da zuciya ɗaya.

14 Za ku same ni, ni Ubangiji na faɗa, zan mayar muku da arzikinku, in tattaro ku daga cikin dukan al’ummai da dukan wurare inda na kora ku, ni Ubangiji na faɗa, zan komo da ku a wurin da na sa a kwashe ku a kai ku zaman talala.’

15 “Domin kun ce, Ubangiji ya ba ku annabawa a Babila,

16 ku ji abin da Ubangiji ya faɗa a kan sarkin da ya hau gadon sarautar Dawuda, da a kan dukan jama’ar da suke zaune a wannan birni, wato a kan danginku waɗanda ba a kwashe su zuwa zaman talala ba.

17 Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Ga shi, zan aiko musu da takobi, da yunwa, da masifa, zan maishe su kamar ruɓaɓɓen ɓaure waɗanda suka lalace ƙwarai, har ba su ciwuwa.

18 Zan fafare su da takobi, da yunwa, da masifa. Zan maishe su abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. Za su zama abin la’ana, da abin razana, da abin raini, da abin zargi, ga dukan al’ummai, inda na kora su.

19 Domin ba su ji maganata wadda ni Ubangiji na faɗa ba, na yi ta aika muku da ita ta wurin bayina annabawa, amma kuka ƙi, ni Ubangiji na faɗa.

20 Ku ji maganar Ubangiji, dukanku da aka kai ku zaman talala waɗanda na kora daga cikin Urushalima zuwa Babila.’

21 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce a kan Ahab ɗan Kolaya, da Zadakiya ɗan Ma’aseya, waɗanda suke yi muku annabcin ƙarya da sunana. ‘Ga shi, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, zai kashe su a kan idonku.

22 Saboda su duka waɗanda aka kai bautar talala daga Yahuza zuwa Babila, za su mori kalman nan suna yin la’ana cewa, “Ubangiji ya maishe ka kamar Zadakiya da Ahab, waɗanda Sarkin Babila ya gasa da wuta!”

23 Gama sun yi wauta a Isra’ila, sun yi zina da matan maƙwabtansu, sun yi ƙarya da sunana, ni kuwa ban umarce su ba. Ni na sani, ni ne kuma shaida, ni Ubangiji na faɗa.

Saƙo ga Shemaiya

24 “Zancen Shemaiya mutumin Nehelam,

25 haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya faɗa. Ga shi, ka aika da wasiƙu da sunanka zuwa ga dukan jama’ar da suke a Urushalima, da zuwa ga Zafaniya ɗan Ma’aseya, firist, da kuma ga dukan firistoci, cewa

26 Ubangiji ya naɗa ka firist a madadin Yehoyada firist, ka lura da Haikalin Ubangiji, ka sa kowane mahaukacin da zai yi annabci a turu, ka sa masa ƙangi.

27 To, me ya sa ba ka tsauta wa Irmiya, mutumin Anatot, wanda yake yin maka annabci ba?

28 Gama ya aiko mana a Babila, cewa za mu daɗe a zaman talala, mu gina wa kanmu gidaje, mu zauna a ciki, mu dasa gonaki mu ci amfaninsu.”

29 Sai Zafaniya firist, ya karanta wasiƙan nan a gaban annabi Irmiya.

30 Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya, ya ce,

31 ya aika wa dukan waɗanda suke zaman talala ya ce, “Haka Ubangiji ya ce a kan Shemaiya mutumin Nehelam, ‘Saboda Shemaiya ya yi muku annabci, alhali ni ban aike shi ba, ya sa ku dogara ga ƙarya,’

32 saboda haka Ubangiji ya ce, ‘ga shi, zan hukunta Shemaiya, mutumin Nehelam, shi da zuriyarsa ba za a bar masa mai rai ko ɗaya a wannan jama’a ba, wanda zai ga irin alherin da zan yi wa jama’ata, gama ya kuta tayarwa ga Ubangiji,’ ” in ji Ubangiji.