IRM 32

Irmiya Ya Sayi Saura a Anatot

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a shekara ta goma ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza. A lokacin kuwa Nebukadnezzar yana da shekara goma sha takwas da sarauta a Babila.

2 A lokacin nan kuwa sojojin Sarkin Babila sun kewaye Urushalima da yaƙi, annabi Irmiya kuwa yana a tsare a gidan waƙafi, a fādar Sarkin Yahuza.

3 Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi.

4 Zadakiya Sarkin Yahuza kuwa, ba zai tsere wa Kaldiyawa ba, amma za a ba da shi a hannun Sarkin Babila. Zai yi magana da shi fuska da fuska, ya kuma gan shi ido da ido.

5 Sarkin Babila kuwa zai tafi da Zadakiya zuwa Babila. Zai zauna can sai lokacin da na ziyarce shi. Ko da ya yi yaƙi da Kaldiyawa ba zai yi nasara ba.”

6 Irmiya ya ce, “Ubangiji ya yi magana da ni, cewa

7 ga shi, Hanamel, ɗan Shallum kawuna, zai zo wurina ya ce mini, ‘Ka sayi gonata wadda take a Anatot, gama kai ne ka cancanci ka fanshe ta, sai ka saye ta.’ ”

8 Sai Hanamel ɗan kawuna ya zo wurina a gidan waƙafi, bisa ga faɗar Ubangiji, ya ce mini, “Ka sayi gonata wadda take a Anatot a ƙasar Biliyaminu, gama kai ne ka cancanta ka mallake ta, kai ne za ka fanshe ta, sai ka saye ta.” Sa’an nan na sani wannan maganar Ubangiji ce.

9 Sai na sayi gonar a Anatot daga hannun Hanamel ɗan kawuna, na biya shi shekel goma sha bakwai na azurfa.

10 Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna kuɗin da ma’auni.

11 Na ɗauki takardun ciniki waɗanda aka rubuta sharuɗan a ciki da wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba,

12 na ba Baruk, ɗan Neriya, ɗan Ma’aseya, a gaban Hanamel, ɗan kawuna, da gaban shaidun da suka sa hannun a takardar shaidar sayen, da gaban dukan Yahudawa waɗanda suke zaune a gidan waƙafi.

13 Sai na umarci Baruk a gabansu cewa,

14 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya ce, ‘Ka ɗauki waɗannan takardun shaida, wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tukunyar ƙasa domin kada su lalace.’

15 Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya faɗa, ‘Gidaje, da gonaki, da gonakin inabi, za a sāke sayensu a ƙasan nan.’ ”

Addu’ar Irmiya

16 Bayan da na ba Baruk, ɗan Neriya, takardar sharuɗan ciniki, sai na yi addu’a ga Ubangiji, na ce,

17 “Ya Ubangiji Allah, kai ne ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka da ƙarfinka, ba abin da ya fi ƙarfinka.

18 Kakan nuna madawwamiyar ƙauna ga dubbai, amma kakan hukunta wa ‘ya’ya saboda laifin ubanninsu. Ya maigirma Maɗaukaki, Allah, sunanka kuwa Ubangiji Mai Runduna.

19 Kai babban mashawarci ne, mai aikata manyan ayyukanka. Kana ganin dukan ayyukan ‘yan adam. Kakan sāka wa kowa bisa ga halinsa da ayyukansa.

20 Ka aikata alamu da al’ajabai a ƙasar Masar. Har wa yau kuma kana aikata su a Isra’ila da kuma cikin dukan al’ummai, ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.

21 Ta wurin alamu da al’ajabai, da iko, da ƙarfi, da banrazana, ka fito da jama’arka Isra’ila daga ƙasar Masar.

22 Ka kuwa ba su wannan ƙasa wadda ka rantse za ka ba kakanninsu. Ƙasar da take cike da yalwar albarka.

23 Amma sa’ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.

24 “Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani.

25 Duk da haka ya Ubangiji Allah, ka ce mini, ‘Sayi gonar da kuɗi, a gaban shaidu, ko da yake an ba da birnin a hannun Kaldiyawa.’ ”

26 Ubangiji kuwa ya ce wa Irmiya,

27 “Ni ne Ubangiji Allah na dukan ‘yan adam, ba abin da ya fi ƙarfina.

28 Saboda haka, ni Ubangiji, na ce zan ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa da hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, za su ci birnin.

29 Kaldiyawa da suke yaƙi da wannan birni za su zo, za su ƙone wannan birni da wuta ƙurmus, da gidaje waɗanda aka ƙona turare ga Ba’al a kan rufinsu. Aka kuma miƙa hadayu na sha ga gumaka, don su tsokane ni in yi fushi.

30 Gama jama’ar Isra’ila da ta Yahuza, tun daga ƙuruciyarsu, ba su aikata kome a gabana ba sai mugunta, ba abin da jama’ar Isra’ila suka yi, sai tsokanata da gumaka don in yi fushi da ayyukan hannuwansu, ni Ubangiji na faɗa.

31 Wannan birni ya tsokane ni ƙwarai tun lokacin da aka gina shi har zuwa yau, domin haka zan kawar da shi daga gabana.

32 Wannan kuwa saboda muguntar jama’ar Isra’ila ce da ta Yahuza, wadda suka yi don su tsokane ni in yi fushi, su da sarakunansu, da shugabanninsu, da firistocinsu, da annabawansu, da mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima.

33 Sun juya mini baya, ba su fuskance ni ba, ko da yake na yi ta koya musu, amma ba su saurara ga koyarwata ba.

34 Sun kafa gumakansu na banƙyama a cikin Haikalina wanda ake kira da sunana, sun kuwa ƙazantar da shi.

35 Sun gina wa Ba’al masujadai a kwarin ɗan Hinnom don su miƙa ‘ya’yansu mata da maza hadaya ga Molek, ni kuwa ban umarce su ba, ba shi kuwa a tunanina. Ga shi, sun aikata wannan abin banƙyama, don su sa Yahuza ta yi zunubi.”

Alkawari na Sa Zuciya

36 “Domin haka ga abin da ni Ubangiji Allah na Isra’ila na ce a kan wannan birni wanda ka ce, ‘An ba da shi ga Sarkin Babila, da takobi, da yunwa, da annoba.’

37 Ga shi, zan tattaro su daga dukan ƙasashe inda na kora su, da fushina, da hasalata, da haushina. Zan komo da su a wannan wuri, zan sa su su zauna lafiya.

38 Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu.

39 Zan ba su zuciya ɗaya, da tafarki ɗaya domin su yi tsorona har abada, domin amfanin kansu da na ‘ya’yansu a bayansu.

40 Zan yi madawwamin alkawari da su, ba zan fasa nuna musu alheri ba, zan kuwa sa tsorona a zukatansu domin kada su bar bina.

41 Zan ji daɗin yi musu alheri. Zan dasa su a wannan ƙasa da aminci da zuciya ɗaya.”

42 Gama haka Ubangiji ya faɗa, “Daidai kamar yadda na kawo wannan babbar masifa a kan jama’an nan, haka kuma zan kawo musu dukan waɗannan alherai da na alkawarta musu.

43 Za a sayi gonaki a wannan ƙasa wadda kake cewa ta zama kufai, ba mutum, ba dabba a ciki, wadda aka ba da ita ga Kaldiyawa.

44 Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”