IRM 42

Jawabin Irmiya ga Yohenan

1 Shugabannin sojoji, da Yohenan ɗan Kareya, da Yazaniya ɗan Hoshaiya, da jama’a duka, daga ƙarami zuwa babba, suka zo,

2 suka ce wa annabi Irmiya, “Muna roƙonka, ka roƙi Ubangiji Allahnka dominmu, dukanmu da muka ragu, gama mu kima muka ragu daga cikin masu yawa, kamar yadda kake ganinmu da idonka.

3 Ka yi mana addu’a domin Ubangiji Allahnka ya nuna mana hanyar da za mu bi, da kuma abin da za mu yi.”

4 Annabi Irmiya kuwa ya ce musu, “Na ji abin da kuka ce. Ga shi kuwa, zan yi addu’a ga Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka roƙa. Kowace irin amsa da Ubangiji ya bayar, zan faɗa muku, ba zan ɓoye muku kome ba.”

5 Sa’an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji mai gaskiya, mai aminci ya zama shaida a tsakaninmu, idan ba mu yi duk yadda Ubangiji Allahnka ya aiko ka gare mu ba.

6 Ko nagari ne ko mugu ne, za mu yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu wanda muka aike ka wurinsa, gama zai zama alheri a gare mu idan mun yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu.”

7 Bayan kwana goma sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya.

8 Sai Irmiya ya kira Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi, da dukan jama’a tun daga ƙarami har zuwa babba.

9 Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kuka aike ni da koke-kokenku wurinsa ya ce,

10 ‘Idan za ku zauna a ƙasan nan, to, zan gina ku, ba zan rushe ku ba. Zan dasa ku, ba zan tumɓuke ku ba, gama zan janye masifar da na aukar muku.

11 Kada ku ji tsoron Sarkin Babila, shi wanda kuke jin tsoronsa. Kada ku ji tsoronsa,’ in ji Ubangiji, ‘gama ina tare da ku, zan cece ku, in kuɓutar da ku daga hannunsa.

12 Zan yi muku jinƙai in sa sarkin ya ji ƙanku, ya bar ku ku zauna a ƙasarku.’

13 “Amma idan kuka ce ba za ku zauna a wannan ƙasa ba, kuka ƙi yin biyayya da muryar Ubangiji Allahnku,

14 kuna cewa, ‘Mun ƙi, mu, ƙasar Masar za mu tafi, inda ba za mu ga yaƙi ba, ba za mu ji ƙarar ƙahon yaƙi ba, yunwa kuma ba za ta same mu ba, a can za mu zauna.’

15 To, sai ku ji maganar Ubangiji, ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Idan zuwa Masar kuka sa gaba don ku tafi ku zauna a can,

16 to, takobin nan da kuke jin tsoro, zai ci muku can a ƙasar Masar, yunwan nan kuma da kuke jin tsoro za ta bi ku zuwa Masar ta tsananta muku, a can za ku mutu.

17 Duk waɗanda suka sa gaba zuwa Masar domin su zauna can, da takobi, da yunwa, da annoba su ne ajalinsu. Ba wanda zai ragu, ba wanda zai tsira daga masifar da zan aukar musu.’

18 “Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya ce, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa’ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la’ana, da abin ba’a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.’

19 “Ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji ya ce, ‘Kada ku tafi Masar.’ Ku tabbata fa na faɗakar da ku yau,

20 cewa in kun ratse, to, a bakin ranku. Gama kun aike ni wurin Ubangiji Allah cewa, ‘Ka roƙar mana Ubangiji Allahnmu. Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya ce ka faɗa mana kuma za mu aikata.’

21 A wannan rana kuwa na faɗa muku abin da ya ce, amma ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku a kan kowane abin da ya aiko ni in faɗa muku ba.

22 Domin haka yanzu fa ku sani takobi, da yunwa, da annoba, su ne ajalinku a wurin can da kuke sha’awar ku zauna.”