IRM 43

Tafiya zuwa Masar

1 Sa’ad da Irmiya ya gama faɗa wa dukan jama’a maganar da Ubangiji Allahnsu ya aiko musu da ita,

2 sai Yazaniya ɗan Hoshaiya, da Yohenan ɗan Kareya, da dukan ‘yan tsagera, suka ce wa Irmiya, “Ƙarya kake yi, Ubangiji Allahnmu bai aiko ka da cewa kada mu tafi, mu zauna a Masar ba!

3 Amma Baruk ɗan Neriya shi ne ya sa ka faɗi wannan magana gāba da mu, don ka bashe mu a hannun Kaldiyawa domin su kashe mu, ko kuwa su kai mu bauta a Babila.”

4 Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji, da dukan jama’a, ba su yi biyayya da umarnin Ubangiji, su zauna a ƙasar Yahuza ba.

5 Amma Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe sauran mutanen Yahuza duka waɗanda suka komo suka zauna a ƙasar Yahuza, daga wurin al’ummai, inda aka kora su,

6 mata, da maza, da yara, da gimbiyoyi, da kowane mutum da Nebuzaradan shugaban matsara ya bar wa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da annabi Irmiya, da Baruk ɗan Neriya.

7 Suka zo ƙasar Masar, gama ba su yi biyayya da muryar Ubangiji ba. Suka sauka a Tafanes.

8 Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya a Tafanes ya ce,

9 “Kwashi manyan duwatsu da hannunka, ka ɓoye su a ƙofar shiga fādar Fir’auna a Tafanes a idon mutanen Yahuza,

10 ka kuma ce musu, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ga shi, zan aika wa bawana Nebukadnezzar ya zo ya kafa kursiyin sarautarsa a kan duwatsun nan waɗanda na ɓoye. Zai buɗe babbar alfarwarsa a wurin.

11 Nebukadnezzar zai zo ya buga ƙasar Masar. Zai ba annoba waɗanda aka ƙaddara su ga annoba, waɗanda aka ƙaddara ga bauta, za a kai su bauta. Waɗanda aka ƙaddara ga takobi, za su mutu ta takobi.

12 Zai cinna wa gidajen gumakan Masar wuta, zai ƙone su, ya tafi da waɗansu, zai tsabtace ƙasar Masar kamar yadda makiyayi yakan kakkaɓe ƙwarƙwata daga cikin tufafinsa, zai kuwa tashi daga wurin lafiya.

13 Zai kuma farfashe al’amudan duwatsu na On a ƙasar Masar. Zai ƙone gidajen gumakan Masar da wuta.’ ”