IRM 46

Annabci a kan Masar

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan sauran al’umma.

2 Ya yi magana game da sojojin Fir’auna, Sarkin Masar, waɗanda suke a bakin Kogin Yufiretis a Karkemish, waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya ci su da yaƙi a shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza.

3 Masarawa suka yi ihu, suka ce,

“Ku shirya kutufani da garkuwa,

Ku matso zuwa wurin yaƙi!

4 Ku ɗaura wa dawakanku sirdi, ku

hau!

Ku tsaya a wurarenku da kwalkwali

a ka!

Ku wasa māsunku!

Ku sa kayan yaƙi!”

5 Ubangiji ya yi tambaya ya ce,

“Me nake gani?

Sun tsorata, suna ja da baya,

An ci sojojinsu, suna gudu,

Ba su waiwayen baya, akwai tsoro a

kowane sashi.”

6 Masu saurin gudu ba za su tsere ba,

Haka nan kuma jarumi,

A arewa a gefen Kogin Yufiretis,

Sun yi tuntuɓe, sun fādi.

7 Wane ne wannan mai tashi kamar

Kogin Nilu,

Kamar kogunan da ruwansu yake

ambaliya?

8 Masar tana tashi kamar Nilu,

Kamar kogunan da ruwansu yake

ambaliya.

Masar ta ce, “Zan tashi, in rufe

duniya,

Zan hallaka birane da mazauna

cikinsu.”

9 Ku haura, ku dawakai,

Ku yi sukuwar hauka, ku karusai!

Bari sojoji su fito,

Mutanen Habasha da Fut masu

riƙon garkuwoyi,

Da mutanen Lud, waɗanda suka iya

riƙon baka.

10 Wannan rana ta Ubangiji, Allah Mai

Runduna ce,

Ranar ɗaukar fansa ce don ya rama

wa maƙiyansa.

Takobi zai ci, ya ƙoshi,

Ya kuma sha jininsu, ya ƙoshi,

Gama Ubangiji Allah Mai Runduna

zai hallaka maƙiyansa,

A arewa, a bakin Kogin Yufiretis.

11 Ku mutanen Masar, ku haura zuwa

Gileyad

Don ku samo ganye!

A banza kuke morar magunguna,

Ba za ku warke ba.

12 Kunyarku ta kai cikin sauran

al’umma,

Kukanku kuma ya cika duniya.

Soja na faɗuwa bisa kan soja.

Dukansu biyu sun faɗi tare.

13 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan zuwan Nebukadnezzar, Sarkin Babila, don ya yi yaƙi da ƙasar Masar.

14 “Ku yi shelarsa cikin garuruwan

Masar,

Cikin Migdol, da Memfis, da

Tafanes,

Ku ce, ‘Ku tsaya, ku yi shiri,

Gama takobi yana cin waɗanda suke

kewaye da ku!’

15 Me ya sa gunkinka, Afis, ya fāɗi,

Wato bijimi, gunkinka bai tsaya ba?

Domin Ubangiji ya tunkuɗe shi

ƙasa!

16 Sun yi ta fāɗuwa,

Suna faɗuwa a kan juna,

Sai suka ce, ‘Mu tashi mu koma

wurin mutanenmu,

Zuwa ƙasar haihuwarmu, mu gudu

daga takobin azzalumi!’

17 “Ku ba Fir’auna Sarkin Masar

sabon suna,

‘Mai yawan surutu, wanda bai rifci

zarafi ba!’

18 Ni wanda sunana Ubangiji Mai

Runduna Sarki ne,

Na rantse da raina, wani zai ɓullo,

Kamar Tabor a cikin tsaunuka,

Ko kuwa kamar Karmel a bakin

teku.

19 Ya ku mazaunan Masar,

Ku shirya kayanku don zuwa bauta,

Gama Memfis za ta lalace, ta zama

kufai,

Ba mai zama a ciki.

20 “Masar kyakkyawar karsana ce,

Amma bobuwa daga arewa ta aukar

mata!

21 Sojojin ijararta kamar ‘yan maruƙa

ne, masu yawan kitse,

Sun ba da baya, sun gudu, ba su

tsaya ba,

Domin ranar masifarsu ta zo,

Lokacin halakarsu ya yi.

22 Masar tana gudu, tana huci kamar

maciji,

Gama abokan gābanta suna zuwa da

ƙarfi,

Za su faɗo mata da gatura kamar

masu saran itatuwa.

23 Ni Ubangiji na ce, za su sari

kurminta,

Ko da yake ba su ƙirguwa,

Gama suna da yawa kamar fara,

Ba su lasaftuwa.

24 Za a kunyatar da mutanen Masar,

An bashe su a hannun mutanen

arewa.”

25 Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya ce, “Ga shi, zan hukunta Amon na No, da Fir’auna, da Masar, tare da allolinta, da sarakunanta, wato Fir’auna, tare da waɗanda suke dogara gare shi.

26 Zan bashe su a hannun waɗanda suke neman ransu, wato a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da shugabanninsa. Daga baya kuma mutane za su zauna a Masar kamar dā. Ni Ubangiji na faɗa.

27 “Ya bawana Yakubu, kada ka ji

tsoro,

Kada ka firgita, ya Isra’ila.

Gama zan cece ka daga ƙasa mai

nisa,

Zan ceci zuriyarka daga ƙasar

bautarsu.

Yakubu zai komo, ya yi zamansa da

rai kwance,

Ba wanda zai razanar da shi.

28 Ni Ubangiji na ce,

Kada ka ji tsoro, ya bawana

Yakubu,

Gama ina tare da kai.

Zan hallaka dukan sauran al’umma

sarai inda na kora ka.

Amma ba zan hallaka ka sarai ba.

Zan hukunta ka yadda ya kamata,

Ba zan bar ka ba hukunci ba.”