IRM 47

Jawabin Ubangiji a kan Filistiyawa

1 Kafin Fir’auna ya ci Gaza da yaƙi Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan Filistiyawa.

2 Ubangiji ya ce,

“Ga shi, ruwa yana tasowa daga

arewa,

Zai zama kogi da yake ambaliya.

Zai malala bisa ƙasa da dukan abin

da yake cikinta,

Da birni da mazauna cikinsa,

Maza za su yi kuka,

Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.

3 Da jin takawar kofatan dawakai,

Da amon karusai da ƙafafun karusai,

Ubanni ba su juya, su dubi

‘ya’yansu ba,

Domin hannuwansu sun yi laƙwas,

4 Domin lokacin hallaka dukan

Filistiyawa ya yi.

Za a datse wa Taya da Sidon kowane

taimakon da ya ragu,

Gama Ubangiji zai hallaka

Filistiyawa

Waɗanda suke baƙin teku na Kaftor.

5 Baƙin ciki zalla ya sami Gaza,

Ashkelon ta lalace.

Ya ƙattin mutane, yaushe za ku

daina tsattsage kanku?

6 Ya takobin Ubangiji, yaushe za ka

huta?

Sai ka koma ƙubenka,

Ka huta, ka yi shiru!

7 Ƙaƙa zai huta, tun da ni Ubangiji ne

na umarce shi?

Ni Ubangiji na umarce shi ya yi yaƙi

da Ashkelon

Da mazauna a bakin teku.”