IRM 51

Hukuncin Ubangiji a kan Babila

1 Ubangiji ya ce,

“Ga shi, zan kawo iskar ɓarna a

kan Babila

Da mazaunan Kaldiya.

2 Zan aika da masu casawa zuwa

Babila, za su casa ta,

Su bar ƙasarta kango.

Za su kewaye ta a kowane sashi

A wannan ranar masifa.

3 Kada ku bar maharbi ya yi harbi da

bakansa,

Kada kuma ya sa kayan yaƙinsa,

Kada ku rage samarinta,

Ku hallaka dukan sojojinta.

4 Za su fāɗi matattu a ƙasar

Kaldiyawa,

Za a sassoke su a titunansu.”

5 Allah na Isra’ila da Yahuza,

Ubangiji Mai Runduna, bai yashe

su ba,

Ko da yake sun yi wa Mai Tsarki na

Isra’ila zunubi.

6 Ku gudu daga cikin Babila,

Bari kowa ya ceci ransa,

Kada a hallaka ku tare da ita,

Gama a wannan lokaci Ubangiji zai

sāka mata,

Zai sāka mata bisa ga alhakinta.

7 Babila ta zama ƙoƙon zinariya a

hannun Ubangiji,

Ta sa dukan duniya ta yi maye.

Ƙasashen duniya sun sha ruwan

inabinta, suka haukace.

8 Farat ɗaya, Babila ta fāɗi, ta

kakkarye,

Ku yi kuka dominta!

Ku samo mata magani domin azabar

da take sha, watakila ta warke.

9 Mun ba Babila magani, amma ba ta

warke ba.

Bari mu ƙyale ta, kowannenmu ya

koma garinsu,

Gama hukuncinta ya kai sammai, ya

yi tsawo har samaniya.

10 Ubangiji ya baratar da mu a fili,

Bari mu tafi mu yi shelar aikin

Ubangiji Allahnmu a cikin

Sihiyona.

11 Ku wasa kibau, ku cika

kwaruruwanku!

Ubangiji ya ta da ruhun sarakunan

Mediyawa,

Domin yana niyyar hallaka Babila.

Gama Ubangiji zai yi ramuwa

saboda Haikalinsa.

12 Ku ta da tuta don a faɗa wa garun

Babila,

Ku ƙarfafa matsara,

Ku sa su su yi tsaro,

Ku kuma sa ‘yan kwanto!

Ga shi, Ubangiji ya yi niyya, ya kuwa

aikata

Abin da ya faɗa a kan mazaunan

Babila.

13 Ƙarshenki ya zo,

Ke mai zama kusa da ruwa mai yawa,

Mai yawan dukiya.

Ajalinki ya auka.

14 Ubangiji Mai Runduna ya rantse da

zatinsa, ya ce,

“Hakika zan cika Babila da mutane

kamar fāra,

Za su kuwa raira waƙar nasara a

kanta.”

15 Ubangiji ne ya halicci ƙasa da

ikonsa,

Ya kafa duniya da hikimarsa,

Ya kuma shimfiɗa sammai da

fahiminsa.

16 Bisa ga umarninsa ruwan da yake

samaniya yakan yi ruri,

Yakan sa gajimare su tashi daga

ƙarshen duniya,

Yakan sa walƙiya ta walƙata cikin

ruwan sama,

Yakan sa iska ta haura daga cikin

taskokinsa.

17 Kowane ɗan adam wawa ne, marar

ilimi,

Kowane maƙerin zinariya kuma zai

sha kunya daga wurin gumakansa,

Gama siffofinsa na ƙarya ne, ba

numfashi a cikinsu.

18 Su marasa amfani ne, aikin ruɗarwa

ne kawai,

Za su lalace a lokacin da za a

hukunta su.

19 Amma wanda yake wajen Yakubu ba

haka yake ba,

Domin shi ne ya halicci dukan

abu,

Isra’ila kuwa abin mallakarsa ne,

Ubangiji Mai Runduna ne sunansa.

20 Ubangiji ya ce,

“Kai ne guduma da kayan yaƙina,

Da kai ne na farfasa ƙasashen

duniya,

Da kai ne na hallaka mulkoki.

21 Da kai ne na karya doki da

mahayinsa,

22 Da kai ne na farfasa karusa da

mahayinsa.

Da kai ne na kakkarya mace da

namiji,

Da kai ne na kakkarya tsoho da

saurayi,

Da kai ne na kakkarya saurayi da

budurwa,

23 Da kai ne na kakkarya makiyayi da

garkensa,

Da kai ne na kakkarya manoma da

dawakan nomansa,

Da kai ne na kakkarya masu mulki

da shugabanni.”

24 Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona.

25 Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse mai

hallakarwa,

Wanda ya hallaka duniya duka.

Zan miƙa hannuna gāba da kai,

Zan mirgino da ƙasa daga

ƙwanƙolin dutse,

Zan maishe ka ƙonannen dutse.

26 Ba za a sami dutsen yin kusurwa, ko

na kafa harsashen gini a cikinka

ba,

Amma za ka zama marar amfani har

abada.”

27 Ku ta da tuta a duniya,

Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho,

Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙi

da ita,

Ku kirawo mulkokin Ararat, da na

Minni, da na Ashkenaz, su yi yaƙi

da ita.

Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zai

shugabanci yaƙin da za a yi da ita,

Ku kawo dawakai kamar fāra.

28 Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita,

Sarakunan Mediyawa, da masu

mulkinsu, da shugabanninsu,

Da kowace ƙasar da take ƙarƙashin

mulkinsu.

29 Duniya ta girgiza, tana makyarkyata

saboda azaba,

Gama nufin Ubangiji na gāba da

Babila ya tabbata,

Nufinsa na mai da ƙasar Babila

kufai, inda ba kowa.

30 Sojojin Babila sun daina yaƙi, suna

zaune a cikin kagaransu.

Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata,

An sa wa wuraren zamanta wuta,

An karya ƙyamaren ƙofofin

garinta.

31 Maguji yana biye da maguji a guje,

Jakada yana biye da jakada,

Don su faɗa wa Sarkin Babila, cewa

an ci birninsa a kowane gefe.

32 An ƙwace mashigai

An ƙone fadamu da wuta,

Sojoji sun gigice.

33 Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na

Isra’ila na ce,

“Mutanen Babila sun zama kamar

daɓen masussuka

A lokacin da ake sussuka,

Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbe

ta zai zo.”

34 Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya

cinye Urushalima,

Ya ragargaza ta,

Ya maishe ta kufai,

Ya haɗiye ta kamar yadda dodon

ruwa yakan yi,

Ya cika cikinsa da kayan

marmarinta,

Ya tatse ta sarai.

35 Bari mutanen Sihiyona su ce,

“Allah ya sa muguntar da mutanen

Babila suka yi mana ta koma

kansu!”

Bari kuma mutanen Urushalima su

ce,

“Allah ya sa hakkin jininmu ya koma

kan Kaldiyawa!”

36 Ubangiji ya ce,

“Zan tsaya muku,

Zan ɗaukar muku fansa,

Zan sa tekunsu da maɓuɓɓugarsu su

ƙafe.

37 Babila za ta zama tarin juji, wurin

zaman diloli,

Abar ƙyama da abar ba’a, inda ba

kowa.

38 Mutanen Babila za su yi ruri kamar

zakuna,

Su yi gurnani kamar ‘ya’yan zaki.

39 Sa’ad da suke cike da haɗama zan yi

musu biki,

In sa su sha, su yi maye, su yi

murna.

Za su shiga barcin da ba za su farka

ba.

40 Zan kai su mayanka kamar ‘yan

raguna, da raguna, da bunsurai.

41 “An ci Babila,

Ita wadda duniya duka take yabo an

cinye ta da yaƙi,

Ta zama abar ƙyama ga sauran

al’umma!

42 Teku ta malalo a kan Babila,

Raƙuman ruwa masu hauka sun

rufe ta.

43 Garuruwanta sun zama abin

ƙyama,

Ta zama hamada, inda ba ruwa,

Ƙasar da ba mazauna,

Ba kuma mutumin da zai ratsa ta

cikinta.

44 Zan hukunta Bel, gunkin Babila,

Zan sa ya yi aman abin da ya

haɗiye,

Ƙasashen duniya ba za su ƙara

bumbuntowa wurinsa ba.

Garun Babila ya rushe!”

45 “Ku fito daga cikinta, ya jama’ata,

Kowa ya tsere da ransa daga zafin

fushin Ubangiji.

46 Kada zuciyarku ta yi suwu,

Kada kuma ku ji tsoro saboda

labarin da ake ji a ƙasar,

Labari na wannan shekara dabam,

na wancan kuma dabam,

A kan hargitsin da yake a ƙasar,

Mai mulki ya tasar wa mai mulki.

47 Saboda haka kwanaki suna zuwa,

Sa’ad da zan hukunta gumakan

Babila,

Za a kunyatar da dukan ƙasar

Babila,

Dukan matattunta za su faɗi a

tsakiyarta.

48 Sa’an nan sama da duniya, da dukan

abin da take cikinsu,

Za su raira waƙar farin ciki,

Domin masu hallakarwa daga arewa

da za su auko mata,

Ni Ubangiji na faɗa.”

49 Babila za ta fāɗi,

Saboda mutanen Isra’ila da dukan

mutanen duniya waɗanda ta

kashe.

50 Ku waɗanda kuka tsere wa takobi!

Ku gudu! Kada ku tsaya!

Ku tuna da Ubangiji a can nesa inda

kuke,

Ku kuma yi ta tunawa da

Urushalima.

51 Mun sha kunya saboda zargin da ake

yi mana,

Kunya ta rufe mu,

Gama baƙi sun shiga tsarkakan

wurare na Haikalin Ubangiji.

52 “Domin haka kwanaki suna zuwa,”

in ji Ubangiji,

“Sa’ad da zan hukunta gumakan

Babila, da dukan ƙasarta,

Waɗanda aka yi wa rauni, za su yi

nishi.

53 Ko da Babila za ta hau samaniya,

Ta gina kagara mai ƙarfi a can,

Duk da haka zan aiki masu

hallakarwa a kanta,

Ni Ubangiji na faɗa.”

54 Ku ji muryar kuka daga Babila,

Da hargowar babbar hallakarwa

daga ƙasar Kaldiyawa!

55 Gama Ubangiji yana lalatar da

Babila,

Yana kuma sa ta kame bakinta na

alfarma,

Sojoji suna kutsawa kamar raƙuman

ruwa,

Suna ta da muryoyinsu.

56 Gama mai hallakarwa ya auka wa

Babila,

An kama sojojinta,

An kuma kakkarya bakunansu,

Gama Ubangiji shi Allah ne, mai

sakayya,

Zai yi sakayya sosai.

57 “Zan sa mahukuntanta, da masu

hikimarta,

Da masu mulkinta, da

shugabanninta,

Da sojojinta su sha su yi maye.

Za su dinga yin barcin da ba za su

farka ba,”

In ji Sarkin, mai suna Ubangiji Mai

Runduna.

58 “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce,

Za a baje garun nan na Babila mai

fāɗi

Za a kuma ƙone dogayen

ƙyamarenta da wuta.

Mutane sun wahalar da kansu a

banza.

Sauran al’umma sun yi wahala kawai

domin wutar lalata.”

59 Jawabin da annabi Irmiya ya ba Seraiya, ɗan Neriya, wato jikan Ma’aseya, lokacin da ya tafi tare da Zadakiya, Sarkin Yahuza, zuwa Babila a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Seraiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi.

60 Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babila, wato dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babila.

61 Irmiya kuwa ya ce wa Seraiya, “Lokacin da ka kai Babila, sai ka karanta dukan maganan nan.

62 Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’

63 Sa’ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa’an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yufiretis.

64 Sa’an nan ka ce, ‘Haka Babila za ta nutse, ba za ta ƙara tashi ba saboda masifar da Ubangiji zai kawo mata.’ ”

Wannan shi ne ƙarshen maganar Irmiya.