IRM 52

Mulkin Zadakiya

1 Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal, ‘yar Irmiya, wanda yake zaune a Libna.

2 Sarki Zadakiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehoyakim ya yi.

3 Al’amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra’ila da Yahuza, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala.

Faɗuwar Urushalima

Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.

4 A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina garu kewaye da ita.

5 An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zadakiya.

6 A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.

7 Sai aka huda garun birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa’ad da Kaldiyawan take kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.

8 Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki Zadakiya, suka ci masa a filayen Yariko. Dukan sojoji suka yashe shi.

9 Da aka kama Zadakiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babila ya yanke masa shari’a.

10 Ya kuwa kashe ‘ya’yan Zadakiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuza a Ribla.

11 Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zadakiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babila inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.

Yahuza ya Je Zaman Talala

12 A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.

13 Sai ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan manyan gidajen da suke Urushalima.

14 Sojojin Kaldiyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan garun Urushalima.

15 Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babila.

16 Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.

17 Kaldiyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a Haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babila.

18 Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar Haikali.

19 Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe.

20 Tagullar da sarki Sulemanu ya yi waɗannan abubuwa da ita, wato ginshiƙai biyu, da kwatarniyar tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna.

21 Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma taƙi huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki.

22 A kan kowane ginshiƙi, an yi masa dajiyar tagulla, tsayinta kamu biyar. A bisa kan kowace dajiya akwai raga da siffofin rumman na tagulla kewaye da dajiyar. Ginshiƙi na biyu ma haka yake da siffofin rumman.

23 Akwai siffofin rumman tasa’in da shida da ake gani a gyaffan. Dukan siffofin rumman da suke a kan ragar kewaye, guda ɗari ne.

24 Shugaban matsara kuma ya ɗauki Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar Haikali, ya tafi da su.

25 Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai ‘yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su.

26 Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babila a Ribla,

27 Sarkin Babila kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat.

Haka aka tafi da mutanen Yahuza bautar talala.

28 Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta. A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa dubu uku da ashirin da uku (3,023).

29 A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa daga Urushalima ɗari takwas da talatin da biyu.

30 A shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa kuma, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa ɗari bakwai da arba’in da biyar. Jimillarsu duka kuwa dubu huɗu da ɗari shida ne (4.600).

An saki Yekoniya an ba shi Girma a Babila

31 A shekarar da Ewil-merodak ya zama Sarkin Babila, sai ya nuna wa Yekoniya Sarkin Yahuza alheri. Ya fisshe shi daga kurkuku. Wannan ya faru ran ashirin da biyar ga watan goma sha biyu a shekara ta talatin da bakwai bayan da aka kai Yekoniya bauta.

32 Ewil-merodak ya nuna wa Yekoniya alheri, ya ba shi matsayi na daraja fiye da waɗansu sarakunan da aka kai su bautar talala a Babila tare da shi.

33 Yekoniya ya tuɓe tufafin kurkuku, ya riƙa cin abinci kullum a teburin sarki, har dukan sauran kwanakin ransa.

34 Kowace rana akan ba shi kyauta bisa ga umarnin sarki, saboda bukatarsa. Haka aka yi masa har rasuwarsa.