ISH 34

Ubangiji Zai Hukunta Edom

1 Ku zo, ku jama’ar dukan al’ummai! Ku tattaru ku kasa kunne. Bari dukan duniya, da kowane mai zama cikinta, ya zo nan ya kasa kunne.

2 Ubangiji yana fushi da al’ummai duka, da kuma dukan sojojinsu. Ya zartar musu da hukuncin hallaka.

3 Ba za a binne gawawwakinsu ba, amma za a bar su can, su ruɓe, su yi ɗoyi, duwatsu kuma za su yi ja wur da jini.

4 Za a murtsuke rana, da wata, da taurari su zama ƙura. Sararin sama zai shuɗe kamar yadda ake naɗe littafi, taurari kuma su faɗo kamar yadda ganyaye suke karkaɗewa daga itacen inabi ko na ɓaure.

5 Ubangiji ya shirya takobinsa a can Sama, yanzu kuwa zai buga Edom, wato mutanen can da ya zartar musu da hukuncin hallaka.

6 Jininsu da kitsensu za su rufe takobinsa, kamar jini da kitsen raguna, da na awaki, da aka miƙa hadaya. Ubangiji zai yi wannan hadaya a birnin Bozara, zai sa wannan ya zama babban kisa a ƙasar Edom.

7 Mutane za su fāɗi kamar bijiman jeji da ‘yan bijimai, ƙasar za ta yi ja wur da jini, kitse kuma zai rufe ta.

8 Wannan shi ne lokacin da Ubangiji zai kuɓutar da Sihiyona, ya kuma ɗauki fansa a kan abokan gābanta.

9 Kogunan Edom za su zama kalo, wato kwalta, ƙasar za ta zama kibritu, wato farar wuta. Dukan ƙasar za ta ƙone kamar kalo.

10 Za ta yi ta ci dare da rana, hayaƙi zai yi ta tashi sama har abada. Ƙasar za ta zama marar amfani shekara da shekaru, ba wanda zai iya ƙara bi ta cikinta.

11 Mujiyoyi da hankaki su ne za su gāji ƙasar. Ubangiji zai maishe ta marar amfani, kamar yadda take tun kafin halitta.

12 Ba sarkin da zai yi mulkin ƙasar, dukan shugabanni kuma za su ƙare.

13 Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su tsiro su yi girma a cikin dukan fādodi da garuruwa masu garuka, diloli da mujiyoyi za su zauna a cikinsu.

14 Namomin jeji za su yi ta kaiwa da komowa a can suna kiran juna. Mugun naman jeji zai je can ya nemi wurin hutawa.

15 Mujiyoyi za su yi sheƙarsu a can, su nasa ƙwayaye, su ƙyanƙyashe ‘ya’yansu, su kuma lura da su a can. Ungulai za su tattaru a can a kai a kai.

16 Bincika cikin Littafin Ubangiji ka karanta abin da yake faɗa. Ba ko ɗaya cikin halittattun nan da zai ɓata ba, ba kuwa wanda zai rasa ɗan’uwansa. Ubangiji ne ya umarta ya zama haka, shi kansa zai kawo su tare.

17 Ubangiji ne zai rarraba musu ƙasar, ya kuma ba ko wannensu nasa rabo. Za su zauna a ƙasar shekara da shekaru, za ta kuwa zama tasu har abada.