ISH 35

Mayarwar Mutanen Allah

1 Hamada za ta yi farin ciki.

Furanni za su hudo a ƙasa da ba ta da amfani.

2 Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna,

Za ta zama kyakkyawa kamar Dutsen Lebanon,

Da dausayi kamar filayen Karmel da Sharon.

Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah,

Ya ga girmansa da ikonsa.

3 Ku ƙarfafa hannuwan da suka gaji,

Da gwiwoyin da suke fama da rashin ƙarfi.

4 Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce,

“Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro!

Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai,

Yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka.”

5 Makaho zai iya ganin gari,

Kurma kuma zai iya ji.

6 Gurgu zai yi tsalle ya yi rawa,

Waɗanda ba su iya magana za su yi sowa don murna.

Rafuffukan ruwa za su yi gudu a cikin hamada,

7 Yashi mai ƙuna kuma zai zama tafki,

Ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za ta cika da maɓuɓɓugai.

Inda diloli suka yi zama,

Ciyawar fadama da iwa za su tsiro.

8 Za a yi babbar karauka a can,

Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.”

Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya,

Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.

9 Ba za a sami zakoki a can ba,

Mugayen namomin jeji ba za su bi ta can ba.

Waɗancan da Ubangiji ya fansar

Su za su zo gida ta wannan hanya.

10 Za su kai Urushalima da murna,

Suna raira waƙa suna sowa don murna.

Za su yi farin ciki har abada,

Ba damuwa da ɓacin rai har abada.