Assuriyawa Sun Kai Hari a Urushalima
1 A shekara ta goma sha huɗu da Hezekiya yake sarautar Yahuza, sai Sennakerib Sarkin Assuriya ya tasar wa birane masu kagara na Yahuza, ya kame su.
2 Sa’an nan ya umarci babban shugaban yaƙinsa ya tashi daga Lakish ya tafi Urushalima tare da babbar rundunar mayaƙa don su sa sarki Hezekiya ya ba da kai. Sai shugaban ya mamaye hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a daidai magudanar da yake kawo ruwa daga kududdufin da yake daga can bisa.
3 Mutanen Yahuza su uku suka fito don su tarye shi, shugaba mai lura da fāda, wato Eliyakim ɗan Hilkiya, da marubucin ɗakin shari’a, wato Shebna, da shugaban da yake kula da tarihin da aka rubuta, wato Yowa ɗan Asaf.
4 Sai shugaban Assuriyawa ya faɗa musu, cewa babban sarki yana so ya san ko me ya sa sarki Hezekiya yake dogara ga kansa.
5 Ya ce, “Kana tsammani magana da baki kawai ta isa ta yi aiki da gwanayen sojoji, da kuma masu ƙarfi? Wa kake tsammani zai taimake ka, har da za ka yi mini tawaye?
6 Kana sa zuciya Masar za ta taimake ka, to, wannan ya zama kamar ka ɗauki kyauro ya zama sandan dogarawa, zai karye, ya yi wa hannunka sartse. Haka Sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara gare shi.”
7 Ya ci gaba ya ce, “Ko za ka ce mini kana dogara ga Ubangiji Allahnka? Shi ne wannan da Hezekiya ya lalatar masa da wuraren sujada da bagadai, sa’an nan ya faɗa wa jama’ar Yahuza da na Urushalima su yi sujada ga bagade ɗaya kurum.
8 Zan yi ciniki da kai da sunan babban sarki, wato Sennakerib. Zan ba ka dawakai dubu biyu idan za ka iya samun yawan mutanen da za su hau su!
9 Ba ka yi daidai da ka ƙi ko wani marar maƙami a shugabannin Assuriya ba, duk da haka kana sa rai ga Masarawa su aiko maka da karusai, da mahayan dawakai!
10 Kana tsammani na tasar wa ƙasarka na kuma lalatar da ita ba tare da taimakon Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya faɗa mini in tasar wa ƙasarka in lalatar da ita.”
11 Sa’an nan sai Eliyakim, da Shebna, da Yowa suka ce wa shugaba na Assuriya, “Ka yi mana magana da harshen Aramiyanci, muna jinsa. Kada ka yi da Ibrananci, dukan jama’ar da suke a kan garu suna saurare.”
12 Ya amsa ya ce, “Kuna tsammani babban sarki ya aiko ni don in daɗa wa ku da sarki kurum dukan magana? Sam, ina magana ne da jama’ar da suke a kan garu, waɗanda za su ci kāshinsu su kuma sha fitsarinsu, kamar yadda ku kanku za ku yi.”
13 Sa’an nan ya tsaya ya ta da murya da harshen Ibrananci, ya ce, “Ku saurara ga abin da Sarkin Assuriya yake faɗa muku.
14 Yana muku kashedi, cewa kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, Hezekiya ba zai iya cetonku ba.
15 Kada kuma ku bari ya rinjaye ku ku dogara ga Ubangiji, har ku sa tsammani Ubangiji zai cece ku, ya hana sojojinmu na Assuriya su cinye birninku.
16 Kada ku kasa kunne ga Hezekiya. Sarkin Assuriya yana umartarku ku fito daga cikin birni ku sallama. Za a yardar muku duka ku ci ‘ya’yan inabi daga gonakinku, da ‘ya’yan ɓaure na itatuwan ɓaurenku, ku kuma sha ruwa daga rijiyoyinku na kanku,
17 har babban sarki ya sāke zaunar da ku a wata ƙasa mai kama da taku, inda akwai gonakin inabi da za su ba da ruwan inabi, da hatsi don yin gurasa.
18 Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku, da cewa Ubangiji zai kuɓutar da ku. Ko gumakan waɗansu al’ummai sun ceci ƙasashensu daga Sarkin Assuriya?
19 Ina suke yanzu, wato gumakan Hamat da na Arfad? Ina gumakan Sefarwayim? Ba ko ɗaya da ya ceci Samariya, ko ba haka ba?
20 A yaushe ko gunki ɗaya na dukan waɗannan ƙasashe ya taɓa ceton ƙasarsa daga babban sarkinmu? To, yanzu me ya sa kuke tsammani Ubangiji zai ceci Urushalima?”
21 Jama’a suka yi tsit, kamar dai yadda sarki Hezekiya ya faɗa musu, ba su amsa da kome ba.
22 Sa’an nan Eliyakim, da Shebna, da Yowa suka kyakkece tufafinsu don baƙin ciki, suka tafi, suka faɗa wa sarki abin da shugaban mayaƙan Assuriya ya yi ta farfaɗa.