ISH 59

Faɗar Muguntar Al’ummar

1 Duba, ikon Ubangiji bai kasa ba, har da ba zai yi ceto ba. Shi ba kurma ba, har da ba zai ji ba.

2 Amma laifofinku suka raba tsakaninku da Allahnku. Zunubanku ne kuma suka sa ya juya daga gare ku don kada ya ji ku.

3 Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma sun ƙazantu da mugunta, leɓunanku kuma suna faɗar ƙarairayi, harsunanku kuwa suna raɗar mugunta.

4 Ba wanda yake kai ƙara ta gaskiya, ba wanda yake yanke shari’a da adalci. Kuna dogara ga shaidar ƙarya, kuna faɗar ƙarya, kuna ɗaukar ciki na ɓarna, ku haifi mugunta.

5 Kuna ƙyanƙyashe ƙwan kāsa, kuna saƙa da saƙar gizogizo. Duk wanda ya ci ƙwayayenku zai mutu, ƙwan da ya fashe zai ƙyanƙyashe kububuwa.

6 Saƙarku ba za ta yi amfani kamar tufa ba, ba za ku yi sutura da abin da kuka yi ba. Ayyukanku ayyukan mugunta ne, kuna aikata ayyukan kama-karya.

7 Kukan sheƙa a guje don ku aikata mugunta, kuna gaggawar zub da jinin marasa laifi. Tunaninku tunanin mugunta ne, lalatarwa da hallakarwa suna a manyan karaukunku.

8 Hanyar salama ba ku san ta ba. Ba adalci a hanyoyinku, kukan karkatar da hanyoyinku, ba wanda zai yi tafiya lafiya a cikinku.

9 Mutane suna cewa, “Don haka ne, yin gaskiya ya yi nisa da mu, adalci kuwa bai iske mu ba. Muna ta neman haske, sai ga duhu, muna neman haske, sai muka yi tafiya cikin duhu.

10 Muna ta lalubar bango kamar makafi, muna ta lalubawa kamar marasa idanu. Da tsakar rana muke ta tuntuɓe, sai ka ce da almuru. A tsakanin waɗanda suke da cikakken ƙarfi, kamar matattu muke.

11 Dukanmu muna gurnani kamar beyar, muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci, amma ina. Muna ta neman ceto, amma ya yi nisa da mu.

12 “Gama laifofinmu sun yi yawa a gabanka, zunubanmu kuwa suna ba da shaida gāba da mu. Laifofinmu suna tare da mu, muna kuwa sane da laifofinmu,

13 wato musun Ubangiji, da ƙin bin Allah, da maganar zalunci, da ta tayarwa, da shirya ƙarairayi a zuciya, da kuma hurta su.

14 Aikata gaskiya ya kawu, adalci ya tsaya daga can nesa, gama gaskiya ta fāɗi a dandali, sahihanci ba zai shiga ba.

15 Gaskiya ba ta, wanda ba ya aikata mugunta ya zama ganima.”

Ubangiji ya gani, bai kuwa ji daɗi ba, da yake gaskiya ba ta.

16 Ya ga ba wani mutum, ba kuwa wanda zai taimaki waɗanda ake zalunta. Sa’an nan da ikon kansa ya yi nasara, adalcinsa ya goyi bayansa.

17 Ya rufe ƙirjinsa da sulken adalci, da kwalkwalin ceto a kansa. Ya sa rigar ɗaukar fansa, ya yafa alkyabbar ikonsa.

18 Bisa ga ayyukansu, haka zai sāka musu hasala, a kan maƙiyansa kuwa ramawa, a kan abokan gābansa, zai rama, da kuma a kan ƙasashen da suke a bakin gāɓa.

19 Saboda haka waɗanda suke yamma za su ji tsoron sunan Ubangiji, waɗanda suke wajen gabas kuma za su ji tsoron ɗaukakarsa, gama zai zo kamar rafi mai tsananin gudu, wanda iskar Ubangiji take korawa.

20 Zai zo Sihiyona ya zama mai fansa ga waɗanda suke na Yakubu, su da suka juya suka bar mugunta.

21 Ubangiji ya ce, “Amma ni, wannan shi ne alkawarina da su, Ruhuna da yake tare da ku, da kalmomina da na sa a bakunanku, ba za su rabu da bakunanku ba, ko daga bakunan ‘ya’yanku, ko na jikokinku, tun daga wannan lokaci har abada.”