ISH 60

Darajar Urushalima a Gaba

1 Ki tashi, ya Urushalima, ki haskaka kamar rana,

Daukakar Ubangiji tana haskakawa a kanki kamar rana!

2 Duhu zai rufe sauran al’umma,

Amma hasken Ubangiji zai haskaka a kanki,

Daukakarsa za ta kasance tare da ke!

3 Za a jawo al’ummai zuwa ga haskenki,

Sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.

4 Ki duba kewaye da ke, ki ga abin da yake faruwa,

Mutanenki suna ta tattaruwa domin su komo gida!

‘Ya’yanki maza za su taho daga nesa,

Za a ɗauki ‘ya’yanki mata kamar yara.

5 Za ki ga wannan, ki cika da farin ciki,

Za ki yi rawar jiki saboda jin daɗi.

Za a kawo miki dukiyar al’ummai,

Wato waɗanda suke a ƙasashen hayi.

6 Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa.

Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi.

Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi!

7 Dukan tumaki na Kedar da Nebayot,

Za a kawo miki su hadaya,

A kuwa miƙa su a kan bagade domin Ubangiji ya ji daɗi.

Ubangiji zai darajanta Haikalinsa fiye da dā.

8 Waɗannan jiragen ruwa fa? Suna tafe kamar gizagizai,

Kamar kurciyoyi suna komowa gida.

9 Jiragen ruwa ne suke zuwa daga manisantan ƙasashe,

Suna kawo mutanen Allah gida.

Suna tafe da azurfa da zinariya,

Domin su girmama sunan Ubangiji,

Allah Mai Tsarki na Isra’ila,

Wanda ya sa dukan al’ummai su girmama mutanensa.

10 Ubangiji ya ce wa Urushalima,

“Baƙi ne za su sāke gina garukanki,

Sarakunansu kuma za su bauta miki.

Na hukunta ki da fushina,

Amma yanzu zan nuna miki alheri da jinƙai.

11 Ƙofofinki za su kasance a buɗe dare da rana,

Domin sarakunan al’ummai su kawo miki dukiyarsu.

12 Amma al’umman da ba su bauta miki ba,

Za a hallakar da su.

13 “Itatuwan fir da irinsu

Mafi kyau daga jejin Lebanon,

Za a kawo su domin a sāke gina ki, ke Urushalima,

Domin a ƙawata Haikalina,

A darajanta birnina.

14 ‘Ya’ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo,

Su rusuna, su nuna bangirma.

Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki.

Za su ce da ke, ‘Birnin Ubangiji,’

‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra’ila.’

15 “Ba za a ƙara ƙinki, a yashe ki ba,

Ki zama birnin da aka fita aka bari ba kowa ciki.

Zan sa ki zama babba, mai ƙayatarwa kuma,

Wurin yin farin ciki har abada abadin.

16 Al’ummai da sarakuna za su lura da ke

Kamar yadda uwa take lura da ɗanta.

Za ki sani, ni Ubangiji, na cece ki,

Allah Mai Iko Dukka na Isra’ila ya fanshe ki.

17 “Zan kawo miki zinariya maimakon tagulla,

Azurfa maimakon baƙin ƙarfe,

Tagulla kuma maimakon itace.

Za ki sami baƙin ƙarfe maimakon dutse.

Masu mulkinki ba za ƙara zaluntarki ba,

Zan sa su yi mulki da gaskiya da salama.

18 Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali ba,

Ba za a ƙara aukar wa ƙasar da ɓarna ba.

Zan kiyaye ki, in kāre ki kamar garu,

Za ki yi yabona domin na cece ki.

19 “Rana ba za ta ƙara zama haskenki da rana ba,

Ko wata ya zama haskenki da dare.

Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki,

Hasken ɗaukakata zai haskaka a kanki.

20 Kwanakin baƙin cikinki za su ƙare.

Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki,

Mai daɗewa fiye da na rana da na wata.

21 Dukan mutanenki za su yi abin da yake daidai,

Za su kuwa mallaki ƙasar har abada.

Ni na dasa su, ni na yi su

Domin su bayyana girmana ga duka.

22 Har ma da iyalin da suka fi ƙanƙanta da ƙasƙanci,

Za su zama babbar al’umma,

Kamar al’umma mai iko.

Zan sa wannan ya faru nan da nan

Sa’ad da lokacin da ya dace ya yi.

Ni ne Ubangiji!”