ISH 64

1 Don me ba za ka kware sararin sama, ka sauko ba? Duwatsu za su gan ka, su girgiza saboda tsoro!

2 Za su karkaɗu kamar ruwan da yake tafasa a wuta. Ka zo ka bayyana ikonka a kan abokan gābanka, ka sa al’ummai su yi rawar jiki a gabanka.

3 Ka taɓa zuwa ka yi abubuwan banrazana waɗanda ba mu sa tsammani ba, duwatsu suka ganka suka kaɗu domin tsoro.

4 Ba wanda ya taɓa gani ko jin labarin wani Allah kamarka, wanda ya yi waɗannan ayyuka ga waɗanda suka sa zuciyarsu gare shi.

5 Ka amince da waɗanda suke murna su aikata abin da yake daidai, su waɗanda suka tuna da yadda kake so su yi zamansu. Ka yi fushi da mu, amma muka ci gaba da yin zunubi, har da fushin da ka yi ƙwarai, muka ci gaba da aikata abin da ba daidai ba, tun daga zamanan dā.

6 Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su.

7 Ba wanda ya juyo gare ka ya yi addu’a, ba wanda ya je gare ka neman taimako. Ka ɓuya mana, ka kuwa yashe mu saboda zunubanmu.

8 Amma kai ne Ubanmu, ya Ubangiji. Mu kamar yumɓu ne, kai kuwa kamar maginin tukwane. Kai ka halicce mu,

9 saboda haka kada ka yi fushi da mu ainun, ko ka riƙe da zunubanmu har abada, mu dai mutanenka ne, ka yi mana jinƙai.

10 Keɓaɓɓun biranenka suna kama da hamada, aka kuma ƙaurace wa kufan Urushalima.

11 Haikalinmu, kyakkyawan keɓaɓɓen wuri inda kakanninmu suka yi yabonka, aka lalatar da shi da wuta, dukan wuraren da muka ƙauna aka lalatar da su.

12 Ya Ubangiji, dukan wannan bai sa ka yi wani abu ba? Ba za ka yi kome ba, kana kuwa sa mu yi ta shan wuya, har fiye da yadda muke iya daurewa?