ISH 65

Hukuncin Allah a kan Masu Tawaye

1 Ubangiji ya ce, “Na shirya in amsa addu’o’in mutanena, amma ba su yi addu’a ba. Na yi shiri domin su same ni, amma ba su ko yi ƙoƙarin nemana ba. Al’ummar ba ta yi addu’a a gare ni ba, ko da yake a koyaushe ina a shirye domin in amsa cewa, ‘Ga ni nan, zan taimake ku.’

2 Kullum ina a shirye domin in marabci waɗannan mutane, waɗanda saboda taurinkansu suka yi ta aikata abin da ba daidai ba, suka bi hanyoyin kansu.

3 Suka yi ta ƙara sa ni fushi ta wurin rashin kunyarsu. Suka miƙa hadayu irin na arna a ɗakunan tsafi da suke a lambu, suka kuma ƙona turare a kan bagadan arna.

4 Da dare sukan tafi cikin kogwanni da kaburbura, suna neman shawarar kurwar matattu. Waɗannan mutane sukan ci naman alade, su kuma sha romon naman da aka miƙa hadaya irin ta arna.

5 Sa’an nan su riƙa ce wa sauran mutane, ‘Ku yi nesa da mu gama muna da tsarki da yawa, har da ba za mu taɓa ku ba.’ Ba zan daure da irin waɗannan mutane ba, fushina a kansu kamar wuta ce wadda ba za ta taɓa mutuwa ba.

6 “Na riga na ƙudura hukuncinsu, shari’ar da aka yanke kuwa an rubuta ta. Ba zan ƙyale abin da suka aikata ba, amma zan sāka musu

7 saboda zunubansu da zunuban kakanninsu. Gama suka ƙona turare a ɗakunan tsafin arna na kan tuddai, suka kuwa faɗi mugun abu a kaina. Saboda haka zan hukunta su yadda ya cancance su.”

8 Ubangiji ya ce, “Ba wanda ya lalatar da ‘ya’yan inabi, maimakon haka sai suka yi ruwan inabi da su. Ni kuwa ba zan hallakar da dukan mutanena ba, zan ceci waɗanda suke bauta mini.

9 Zan sa wa Isra’ilawa waɗanda suke na kabilar Yahuza albarka, zuriyarsu kuma za su mallaki ƙasata da duwatsuna. Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda suke bauta mini za su zauna a can.

10 Za su yi mini sujada, za su kai tumakinsu da shanunsu wurin kiwo a kwarin Sharon a wajen yamma, da kuma a kwarin Akor a wajen gabas.

11 “Amma ba haka zai zama ba, ga ku da kuka rabu da ni, ku waɗanda kuka yi watsi da Sihiyona, tsattsarkan dutsena, kuka yi sujada ga Gad da Meni, wato allolin sa’a da na ƙaddara.

12 Mutuwa ta ƙarfi da yaji za ku yi, gama sa’ad da na yi kiranku ba ku amsa ba, ba ku kasa kunne ba kuwa sa’ad da nake magana da ku. Kuka zaɓa ku yi mini rashin biyayya, ku kuma aikata mugunta.

13 Saboda haka ina faɗa muku, cewa su waɗanda suke yin sujada gare ni suna kuwa yi mini biyayya, za su sami wadataccen abinci da abin sha, amma ku za ku sha yunwa da ƙishi. Su za su yi murna, amma ku za ku sha kunya.

14 Za su raira waƙa don farin ciki, amma ku za ku yi kuka da karayar zuci.

15 Zaɓaɓɓun mutane ne za su mori sunayenku wajen la’antarwa. Ni, Ubangiji, zan kashe ku. Amma zan ba da sabon suna ga waɗanda suke yi mini biyayya.

16 Dukan wanda yake so ya roƙi albarka, sai ya roƙi Allah ya sa masa albarka, Allah da yake mai aminci ne. Dukan wanda zai sha rantsuwa, sai ya rantse da sunan Allah, Allah da yake mai aminci ne. Wahalan dā za su ƙare, za a kuwa manta da su.”

Sabuwar Sama da Sabuwar Duniya

17 Ubangiji ya ce, “Ina yin sabuwar duniya da sabon sararin sama. Abubuwa na dā za a manta da su ɗungum.

18 Ku yi murna da farin ciki a kan abin da na halitta. Sabuwar Urushalima da nake halittawa za ta cika da murna, jama’arta kuma za su yi farin ciki.

19 Ni kaina kuma zan cika da murna saboda Urushalima da jama’arta. Ba kuka a can, ba bukatar neman taimako.

20 Jarirai ba za su mutu tun suna jarirai ba, ko wanne zai cika yawan kwanakinsa kafin ya mutu. Waɗanda suke masu shekara ɗari da haihuwa su ne samari. Waɗanda suka mutu kafin wannan lokaci, to, alama ce, ta cewa na hukunta su.

21-22 Mutane za su gina gidaje su kuwa zauna a cikinsu, ba waɗansu dabam za su mori gidajen ba. Za su dasa gonakin inabi su kuwa ji daɗin ruwan inabi, ba waɗansu dabam za su sha shi ba. Mutanena za su yi tsawon rai kamar itatuwa. Za su ci cikakkiyar moriyar abubuwan da suka yi aikinsu.

23 Aikin da suka yi zai yi nasara, ‘ya’yansu ba za su gamu da bala’i ba, zan sa musu albarka duk da zuriyarsu har dukan zamanai.

24 Zan amsa addu’o’insu tun ma kafin su gama yin addu’a gare ni.

25 Kyarketai da ‘yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci budu kamar yadda shanu suke yi. Maciji ba zai ƙara zama abu mai hatsari ba. A kan Sihiyona tsattsarkan dutsena, ba za a sami wani abu da zai cutar ba, ko wani mugun abu.”