LUK 10

Yesu Ya Aiki Saba’in Ɗin

1 Bayan wannan Ubangiji ya zaɓi waɗansu mutum saba’in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi.

2 Ya ce musu, “Girbin na da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi ya turo masu girbi, su yi masa girbi.

3 To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar ‘yan tumaki a tsakiyar kyarketai.

4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko burgami, ko takalma. Kada ku yi doguwar gaisuwa da kowa a hanya.

5 Duk gidan da kuka sauka, ku fara da cewa, ‘Salama alaikun mutanen gidan nan!’

6 In akwai da ɗan salama a gidan, to, salamarku za ta tabbata a gare shi. In kuwa babu, za ta komo muku.

7 Ku zauna a gidan, kuna ci kuna shan duk irin abin da suka ba ku, domin ma’aikaci ya cancanci ladansa. Kada ku riƙa sāke masauki.

8 Duk garin da kuka shiga, in an yi na’am da ku, ku ci duk irin abin da aka kawo muku.

9 Ku warkar da marasa lafiya da suke cikinsa, ku kuma ce musu, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’

10 Amma duk garin da kuka shiga ba a yi na’am da ku ba, sai ku zaga kwararo kwararo, kuna cewa,

11 ‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafunmu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku sani Mulkin Allah ya kusato.’

12 Ina dai gaya muku, a ran nan, za a fi haƙurce wa Saduma a kan garin nan.”

Tsawata wa Garuruwan da ba su Tuba Ba

13 “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu’ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, sun zauna sāye da tsumma, suna hurwa da toka.

14 Amma a Ranar Shari’a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.

15 Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A’a, ƙasƙantar da ke za a yi har Hades.

16 “Duk mai sauraronku, ni yake saurare. Mai ƙinku kuma, ni yake ƙi. Duk mai ƙina kuwa, wanda ya aiko ni ne ya ƙi.”

Komowar Saba’in Ɗin

17 Sai kuma saba’in ɗin nan suka komo da farin ciki, suka ce, “Ya Ubangiji, har aljannu ma suna mana biyayya albarkacin sunanka!”

18 Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya.

19 Ga shi, na ba ku ikon taka macizai da kunamai, ku kuma rinjaye a kan dukan ikon Maƙiyi, ba kuwa abin da zai cuce ku ko kaɗan.

20 Duk da haka, kada ku yi farin ciki aljannu na yi muku biyayya, sai dai ku yi farin cikin an rubuta sunayenku a Sama.”

Yesu Ya Yi Farin Ciki

21 A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al’amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.

22 Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san ko wane ne Ɗan sai dai Uban, ko kuma ya san ko wane ne Uban sai dai Ɗan, da kuma wanda Ɗan yake so ya bayyana wa.”

23 Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a keɓance, “Albarka tā tabbata ga idanun da suka ga abin da kuka gani.

24 Ina gaya muku, annabawa da sarakuna da yawa suna son ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, suna kuma so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”

Basamariyen da Ya Nuna Jinƙai

25 Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?”

26 Yesu ya ce musu, “Me yake rubuce a Attaura? Yaya kake karantawa?”

27 Sai ya amsa ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.”

28 Yesu ya ce masa, “Ka amsa daidai. Ka riƙa yin haka, za ka rayu.”

29 Shi kuwa mutumin, don yana son baratar da kansa, ya ce wa Yesu, “To, wane ne ɗan’uwa nawa?”

30 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ne ya tashi daga Urushalima za shi Yariko. Sai ‘yan fashi suka fāɗa shi, suka tuɓe shi, suka yi masa mugun dūka, suka tafi suka bar shi rai ga Allah.

31 Daga nan ya zamana wani firist ya biyo ta wannan hanya. Da ya gan shi sai ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa.

32 Haka kuma wani Balawe, da ya iso wurin ya gan shi, shi ma ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa.

33 Ana nan sai hanya ta kawo wani Basamariye inda yake. Da ya gan shi, sai tausayi ya kama shi,

34 ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, yana zuba musu mai da ruwan inabi. Sa’an nan ya ɗora shi a kan dabbarsa, ya kai shi masauki, ya yi ta jiyyarsa.

35 Kashegari ya ɗebo dinari biyu ya ba maigidan, ya ce, ‘Ka yi jiyyarsa, duk kuma abin da ka ɓatar bayan wannan, in na dawo sai in biya ka.’

36 To, a cikin ukun nan, wa kake tsammani ya zama ɗan’uwa ga wanda ‘yan fashin suka faɗa wa?”

37 Sai ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Sai Yesu ya ce masa, “Kai ma, ka je ka riƙa yin haka.”

Yesu Ya Ziyarci Marta da Maryamu

38 Suna tafiya, sai ya shiga wani ƙauye, wata mace kuma mai suna Marta ta sauke da shi a gidanta.

39 Tana kuwa da ‘yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana sauraron magana tasa.

40 Marta kuwa yawan hidimomi ya ɗauke mata hankali, sai ta je gunsa, ta ce, “Ya Ubangiji, ba ka kula ba, ‘yar’uwata ta bar ni ina hidima ni kaɗai? Gaya mata ta taimake ni mana.”

41 Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta! Hankalinki a tashe yake, kina kuma damuwa kan abu da yawa.

42 Bukatu kima ne, ta ainihi ɗaya ce. Maryamu ta zaɓi abu mai kyau, ba kuwa za a karɓe mata ba.”