LUK 11

Koyarwar Yesu a kan Addu’a

1 Wata rana Yesu yana addu’a a wani wuri. Bayan da ya gama, sai wani a cikin almajiransa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka koya mana addu’a, kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa.”

2 Sai ya ce musu, “In kuna addu’a ku ce,

‘Ya Uba, a kiyaye sunanka da tsarki,

Mulkinka yă zo,

3 Ka ba mu abincin yau da na kullum.

4 Ka gafarta mana zunubanmu, gama mu ma muna gafarta wa duk wanda yake yi mana laifi.

Kada ka kai mu wurin jaraba.’ ”

5 Ya kuma gaya musu, “Misali, idan waninku yana da amini, ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, ‘Wāne, ranta mini gurasa uku mana,

6 ga shi, wani abokina matafiyi ya sauka a wurina yanzu, ba ni kuwa da abincin da zan ba shi,’

7 sa’an nan aminin ya amsa masa daga ciki ya ce, ‘Kada ka dame ni, ai, an kulle ƙofa, da ni da ‘ya’yana duk mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka wani abu ba.’

8 Ina gaya muku, ko da yake ba zai tashi ya ba shi wani abu don yana amininsa ba, amma saboda nacinsa zai tashi ya ba shi ko nawa yake bukata.

9 Ina dai gaya muku, ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.

10 Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.

11 Wane uba ne a cikinku, da ɗansa zai roƙe shi [gurasa, ya ba shi dutse? Ko ya roƙe shi] kifi, ya ba shi maciji?

12 Ko kuwa ya roƙe shi ƙwai, ya ba shi kunama?

13 To, ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba ‘ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.”

Yesu da Ba’alzabul

14 Wata rana Yesu yana fitar da beben aljan. Da aljanin ya fita, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.

15 Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Ba’alzabul sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”

16 Waɗansu kuwa, don su gwada shi, suka nema ya nuna musu wata alama daga Sama.

17 Shi kuwa da ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Haka kuma, in gida ya rabu a kan gāba, zai baje.

18 In kuma Shaiɗan ya rabu a kan gāba, yaya mulkinsa zai ɗore? Ga shi, kun ce da ikon Ba’alzabul nake fitar da aljannu.

19 In kuwa da ikon Ba’alzabul nake fitar da aljannu, to, ‘ya’yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.

20 Ni kuwa in da ikon Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan.

21 In ƙaƙƙarfan mutum ya yi ɗamara sosai, yana tsaron gidansa, kayan gidansa lafiya suke.

22 In kuwa wanda ya fi shi ƙarfi ya fāɗa masa, ya kuma rinjaye shi, sai ya ƙwace duk makaman da ya dogara da su, ya kuma rarraba kayansa ganima,

23 Wanda ba nawa ba ne, gāba yake yi da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.”

Komawar Baƙin Aljan

24 “Baƙin aljan, in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa, yana neman hutawa. In ya rasa, sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’

25 Sa’ad da kuwa ya komo gidan ya tarar da shi shararre, ƙawatacce,

26 Daga nan sai ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum kuwa ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa.”

Tabbatacciyar Albarka

27 Yana faɗar haka, sai wata mace a taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Albarka tā tabbata ga wadda ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”

28 Amma ya ce, “I, amma albarka tā fi tabbata ga waɗanda suke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”

‘Yan Zamani Mugaye suna Neman Alama

29 Da taro ya riƙa ƙaruwa a wurinsa, sai ya fara cewa, “Wannan zamani mugun zamani ne. Suna neman ganin wata alama, amma ba wata alamar da za a nuna musu sai dai ta Yunusa.

30 Wato, kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Nineba, haka kuma, Ɗan Mutum zai zamar wa zamanin nan.

31 A Ranar Shari’a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan ta kā da su. Don ta zo ne daga bangon duniya tă ga hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.

32 A Ranar Shari’a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan su kā da su. Don sun tuba saboda wa’azin Yunusa. To, ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.”

Fitilar Jiki

33 “Ba mai kunna fitila ya ɓoye ta a rami, ko ya rufe ta da masaki. A’a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken.

34 Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka zai cika da haske. In kuwa idonka da lahani, sai jikinka ya cika da duhu.

35 Saboda haka, sai ka lura ko hasken da yake a gare ka duhu ne.

36 In kuwa duk jikinka ya cika da haske, ba inda ke da duhu, ai, duk sai ya haskaka gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila take haskaka maka.”

Yesu Ya Fallashi Farisiyawa da Masanan Attaura

37 Yesu yana magana, sai wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Ya shiga cin abincin.

38 Sai Bafarisiyen ya yi mamakin ganin yadda Yesu zai ci abinci ba da fara wanke hannu ba.

39 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ku Farisiyawa kam, kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike kuke da zalunci da mugunta.

40 Ku marasa azanci! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ya yi cikin ba?

41 Gara ku tsarkake cikin, sa’an nan kome zai tsarkaka a gare ku.

42 “Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna fitar da zakkar na’ana’a da karkashi, da kuma kowane ganyen miya. Amma kun ƙi kula da aikata gaskiya da ƙaunar Allah. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da waɗancan ba.

43 Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna son mafifitan mazaunai a majami’u, da kuma gaisuwa a kasuwa.

44 Kaitonku! Kuna kama da kaburburan da ba a gani, waɗanda mutane suke takawa da rashin sani.”

45 Sai wani a cikin masanan Attaura ya amsa masa ya ce, “Malam, faɗar haka fa, mu ma, ai, ka ci mutuncinmu.”

46 Sai Yesu ya ce, “Ku kuma kaitonku, masanan Attaura! Don kuna jibga wa mutane kaya masu wuyar ɗauka, ku da kanku ko ɗan yatsa ba kwa sawa ku tallafa musu!

47 Kaitonku! Don kuna gina gubbobin annabawan da kakanninku suka kashe.

48 Wato, ku shaidu ne a kan kun yarda da ayyukan kakanninku, ga shi, su ne fa suka kashe su, ku kuwa wai har kuka gina musu gubbobin!

49 Shi ya sa hikimar Allah ta ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni, su kashe waɗansu,’

50 don alhakin jinin dukan annabawa da aka zubar tun daga farkon duniya, a bi shi a kan mutanen wannan zamani,

51 wato, tun daga jinin Habila, har ya zuwa na Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagaden hadaya da Wuri Mai Tsarki. Hakika, ina gaya muku, duk za a bi shi kan mutanen wannan zamani.

52 Kaitonku, masanan Attaura! Don kun ɗauke mabuɗin ilimi, ku kanku ba ku shiga ba, kun kuma hana masu son shiga su shiga.”

53 Da ya fito daga wurin, sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara matsa masa ƙwarai, suna tsokanarsa ya yi maganar abubuwa da yawa,

54 suna haƙwansa su burma shi a cikin maganarsa.