LUK 12

Faɗaka a kan Makirci

1 Sa’an nan kuwa da dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, da farko ya yi magana da almajiransa. Ya fara cewa, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, makirci.

2 Ba abin da yake rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba.

3 Don haka, kome kuka faɗa a asirce, za a ji shi a sarari. Abin kuma da kuka yi raɗa a loloki, za a yi shelarsa daga kan soraye

Wanda za a Ji Tsoro

4 “Ya ku masoyana, ina dai gaya muku, kada ku ji tsoron masu kisan mutum, bayan sun kashe kuwa, ba abin da za su iya yi.

5 Amma zan gaya muku wanda za ku tsorata. Ku ji tsoron wannan da in ya kashe, yana da ikon jefawa a cikin Gidan Wuta. Hakika, ina gaya muku, shi za ku ji tsoro!

6 Ashe, ba gwara biyar ne kobo biyu ba? Ko ɗayarsu kuwa Allah bai manta da ita ba.

7 Kai! ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake. Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”

Bayyana Yarda da Almasihu a gaban Mutane

8 “Ina kuma gaya muku, kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai bayyana yarda a gare shi a gaban mala’ikun Allah.

9 Wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, za a yi musun saninsa a gaban mala’ikun Allah.

10 Kowa ya kushe wa Ɗan Mutum, ā gafarta masa, amma wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.

11 Sa’ad da suka kai ku gaban majami’u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa,

12 domin Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya kamata ku faɗa a lokacin.”

Misali na Mai Arziki Marar Azanci

13 Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, kă ce wa ɗan’uwana ya raba gādo da ni.”

14 Amma Yesu ya ce masa, “Haba kai kuwa, wa ya sa ni in zama muku alƙali, ko in raba muku gādo?”

15 Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.”

16 Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta yi albarka ƙwarai.

17 Sai ya ce a ransa, ‘To, ƙaƙa zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’

18 Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina waɗansu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki.

19 Zan kuma ce wa raina, “Lalle ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagali.” ’

20 Amma Allah ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’

21 Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba shi kuwa da wani tanadi a gun Allah.”

Damuwa da Alhini

22 Sai ya ce wa almajiransa, “Don haka, ina gaya muku, kada ku damu da batun rayuwarku game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura.

23 Domin rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi.

24 Ku dubi dai hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah yana cishe su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!”

25 Wane ne a cikinku don damuwarsa zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa?

26 To, in ba za ku iya yin ƙaramin abu irin wannan ba, don me kuke damuwa da sauran?

27 Ku dubi dai furanni yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, duk da haka, ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba.

28 To, ga shi Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke a raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!

29 Ku ma kada ku damu a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada kuwa ku yi alhini.

30 Ai, al’umman duniya suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, ku kuwa, Ubanku ya san kuna bukatarsu.

31 Ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah, sai a ƙara muku da waɗannan abubuwa kuma.

Tara Dukiya a Sama

32 “Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin.

33 Ku sayar da mallakarku, ku bayar taimako. Ku samar wa kanku jakar kuɗi da ba ta tsufa, wato, dukiya marar yankewa ke nan a Sama, inda ba ɓarawon da zai gabato, ba kuma asun da zai ɓāta,

34 don kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”

Bayin da suke a Faɗake

35 “Ku yi ɗamara, fitilunku na kunne.

36 Ku dai zama kamar mutane masu jiran ubangijinsu ya dawo daga gidan biki, da zarar ya ƙwanƙwasa su buɗe masa.

37 Albarka tā tabbata ga bayin nan waɗanda ubangijinsu da zuwansa zai same su a faɗake. Hakika, ina gaya muku, zai yi ɗamara, ya ce su zauna cin abinci, sa’an nan ya bi ta kan kowannensu yana yi masa hidima.

38 In kuwa ya zo da tsakar dare ne, ko kuwa bayan tsakar dare, ya same su a faɗake, bayin nan masu albarka ne.

39 Amma dai ku sani, da maigida zai san lokacin da ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake, ya hana a shiga masa gida.

40 Ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba Ɗan Mutum zai zo.”

Amintaccen Bawa ko Marar Aminci

41 Sai Bitrus ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa na kowa da kowa ne?”

42 Ubangiji ya ce, “Wane ne amintaccen wakilin nan mai hikima, da ubangidansa zai ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?

43 Albarka tā tabbata ga bawan da, in ubangidansa ya dawo, zai samu yana yin haka.

44 Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallaka tasa.

45 In kuwa bawan nan ya ce a ransa, ‘Ubangijina ya jinkirta zuwansa,’ sa’an nan ya soma dūkan barori, maza da mata, ya shiga ci da sha har yana buguwa,

46 ai, ubangijin wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a lokacin kuma da bai sani ba, yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da marasa riƙon amana.

47 Bawan nan kuma wanda ya san nufin ubangijinsa, bai yi shiri ba, bai kuma bi nufinsa ba, za a yi masa matsanancin dūka,

48 Wanda kuwa bai san nufin ubangijinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”

Yesu Ya Kawo Rabuwa

49 “Wuta ce na zo in zuba wa duniya. Sona fa? A ce ta huru!

50 Ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa ɗokanta ƙwarai har a yi mini ita!

51 Kuna tsammani na zo ne in kawo salama a duniya? A’a, ina gaya muku, sai dai rabuwa.

52 Nan gaba, a gida guda mutum biyar za su kasu biyu, uku na gāba da biyu, biyu kuma na gāba da uku.

53 Ta haka, za su rabu. Uba yana gāba da ɗansa, ɗan kuma yana gāba da ubansa, uwa tana gāba da ‘ya tata, ‘yar kuma tana gāba da uwa tata, suruka tana gāba da matar ɗanta, matar ɗan kuma tana gāba da suruka tata.”

Gane Yanayin Lokatai

54 Ya kuma ce wa taron, “In kun ga girgije yana tasowa daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwa.’ Sai kuwa a yi.

55 In kuwa kun ga iskar kudu tana busowa, kukan ce, ‘Za a yi matsanancin zafi.’ Sai kuwa a yi.

56 Munafukai! Kuna iya gane yanayin ƙasa da na sararin sama, amma me ya sa ba ku iya gane alamun zamanin ba?”

Yi Jiyayya da Mai Ƙararka

57 “Me ya sa ku da kanku ma ba kwa iya rarrabewa da abin da yake daidai?

58 Misali, in kuna tafiya zuwa gaban shari’a da mai ƙararku, sai ku yi ƙoƙari ku yi jiyayya da shi tun a hanya, don kada ya ja ku zuwa gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa wa ɗan doka, ɗan doka kuma ya jefa ku a kurkuku.

59 Ina gaya muku, lalle ba za ku fita ba, sai kun biya duka, ba sauran ko anini.”