MAK 4

Bayan Faɗuwar Urushalima

1 Ƙaƙa zinariya ta zama duhu!

Ƙaƙa zinariya tsantsa ta sāke!

Tsarkakakkun duwatsu kuma suna zube

A kowane magamin titi.

2 Darajar samarin Sihiyona

Ta kai tamanin zinariya tsantsa.

To, ƙaƙa ake lissafinsu kamar tukwanen ƙasa,

Aikin hannun maginin tukwane?

3 Ko diloli ma sukan ba ‘ya’yansu mama,

Su shayar da su.

Amma mutanena sun zama kamar jiminai cikin jeji.

4 Harshen jinjiri ya liƙe a dasashinsa saboda ƙishi,

‘Yan yara suna roƙon abinci,

Amma ba wanda ya ba su.

5 Su waɗanda suka ci abubuwa masu daɗi,

Sun halaka a titi.

Su waɗanda aka goye su da alharini,

Yanzu suna kwance a kan tsibin toka.

6 Gama zunubin mutanena

Ya fi zunubin Saduma,

Wadda Ubangiji ya hallakar da ita nan da nan.

7 Keɓaɓɓunta sun fi dusar ƙanƙara tsabta,

Sun kuma fi madara fari.

Jikunansu sun fi murjani ja.

Kyan tsarinsu yana kama da shuɗin yakutu.

8 Yanzu fuskokinsu sun fi kukunniya baƙi,

Ba a iya fisshe su a titi ba,

Fatar jikinsu ta liƙe wa ƙasusuwansu,

Sun bushe kamar itace.

9 Gara ma waɗanda takobi ya kashe

Da waɗanda yunwa ta kashe,

Gama sun rame sarai saboda rashin abinci.

10 Mata masu juyayi, da hannuwansu

Suka ɗauki ‘ya’yansu, suka dafa,

Suka zama musu abinci a lokacin halakar mutanena.

11 Ubangiji ya saki fushinsa,

Ya zuba fushinsa mai zafi.

Ya kunna wa Sihiyona wuta

Wadda ta cinye harsashin gininta.

12 Sarakunan duniya da mazaunanta ba su gaskata,

Cewa abokan gaba ko maƙiya

Za su iya shiga ƙofofin Urushalima ba.

13 Dalili kuwa saboda zunuban annabawa ne,

Da muguntar firistoci,

Waɗanda suka kashe adalai.

14 Sun yi ta kai da kawowa a titi kamar makafi,

Sun ƙazantu da jini

Har ba wanda zai taɓa rigunansu.

15 Mutane suka yi ta yi musu ihu,

Suna cewa, “Ku tafi, ku ƙazamai,

Ku tafi, ku tafi, kada ku taɓa mu!”

Don haka suka zama korarru, masu kai da kawowa.

A cikin sauran al’umma mutane suna cewa,

“Ba za su ƙara zama tare da mu ba.”

16 Ubangiji kansa ya watsar da su,

Ba zai ƙara kulawa da su ba.

Ba su darajanta firistoci ba,

Ba su kuma kula da dattawa ba.

17 Idanunmu sun gaji

Da zuba ido a banza don samun taimako,

Mun zuba ido

Ga al’ummar da ba za ta iya cetonmu ba.

18 Ana bin sawayenmu,

Don haka ba mu iya tafiya a titunanmu ba.

Ƙarshenmu ya yi kusa,

Kwanakinmu sun ƙare,

Gama ƙarshenmu ya zo.

19 Masu runtumarmu sun fi gaggafar da take tashi sama sauri.

Sun fafare mu a kan duwatsu,

Suna fakonmu a cikin jeji.

20 Shi wanda muke dogara gare shi,

Wato zaɓaɓɓe na Ubangiji, ya auka cikin raminsu,

Shi wanda muka ce,

“A ƙarƙashin inuwarsa ne za mu zauna a cikin sauran al’umma.”

21 Ki yi farin ciki, ki yi murna, ke Edom,

Wadda kike zaune cikin ƙasar Uz.

Amma fa za a ba ki ƙoƙo ki sha,

Ki bugu har ki yi tsiraici.

22 Ya Sihiyona, hukunci a kan muguntarki ya ƙare,

Ba zai ƙara barinki a ƙasar bauta ba.

Amma zai hukunta ki saboda muguntarki, ya Edom,

Zai tone zunubanki.