MAK 5

Addu’ar Neman Jinƙai

1 Ya Ubangiji, ka tuna da abin da ya same mu.

Ka duba, ka ga yadda muka zama abin kunya!

2 An ba baƙi gādonmu,

Gidajenmu kuwa an ba bare.

3 Mun zama marayu, marasa ubanni,

Uwayenmu sun zama kamar matan da mazajensu sun mutu.

4 Dole ne mu biya ruwan da za mu sha,

Dole ne kuma mu sayi itace.

5 Masu binmu a ƙyeyarmu suke, suna korarmu da zafi,

Mun gaji, ba a yarda mu huta.

6 Mun miƙa hannu ga Masar da Assuriya

Don mu sami abinci.

7 Ubanninmu sun yi zunubi, ga shi kuwa, ba su,

Mu kuwa muna ɗaukar alhakin muguntarsu.

8 Bayi suke mulkinmu,

Ba kuwa wanda zai cece mu daga hannunsu.

9 Sai mun yi kasai da ranmu kafin mu sami abinci,

Domin akwai masu kisa a jeji.

10 Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu,

Saboda tsananin yunwa.

11 An yi wa mata faɗe a cikin Sihiyona,

Haka kuma aka yi wa budurwai a garuruwan Yahuza.

12 An rataye shugabanni da hannuwansu,

Ba a kuma girmama dattawa ba.

13 An tilasta wa samari su yi niƙa,

Yara kuma suna tagataga da kayan itace.

14 Tsofaffi sun daina zama a dandalin ƙofar birni,

Samari kuma sun daina bushe-bushe.

15 Farin cikinmu ya ƙare,

Raye-rayenmu sun zama makoki.

16 Rawani ya fāɗi daga kanmu,

Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!

17 Saboda wannan zuciyarmu ta ɓaci,

Idanunmu kuma suka duhunta.

18 Gama Dutsen Sihiyona ya zama kufai,

Wurin yawon diloli.

19 Amma ya Ubangiji, kai ne kake mulki har abada,

Kursiyinka ya dawwama har dukan zamanai.

20 Don me ka manta da mu har abada?

Don me ka yashe mu da daɗewa haka?

21 Ya Ubangiji, ka komo da mu zuwa gare ka!

Mu kuwa za mu koma.

Ka sabunta kwanakinmu su zama kamar na dā.

22 Ko ka ƙi mu ne, sam sam?

Ko kuwa ka husata da mu?