MAR 12

Misali na Manoman da Suka Yi Sufurin Garkar Inabi

1 Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata ‘yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa’an nan ya tafi wata ƙasa.

2 Da kakar inabin ta yi, sai ya aiki wani bawansa wurin manoman nan ya karɓo masa gallar garkar.

3 Manoman kuwa suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hanu banza.

4 Sai ya sāke aika musu wani bawa. Shi kuma suka yi masa rotsi, suka wulakanta shi.

5 Ya sāke aiken wani, shi kam, sai suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da waɗansu da yawa, ana dūkan waɗansu, ana kashe waɗansu.

6 Har yanzu dai yana da sauran ɗaya tak, shi ne makaɗaicin ɗansa. Daga ƙarshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’

7 Amma manoman nan suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Ku zo mu kashe shi, gādon yă zama namu.’

8 Sai suka kama shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge.

9 To, me ubangijin garkan nan zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.

10 Ashe, ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba? cewa,

‘Dutsen da magina suka ƙi,

Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.

11 Wannan aikin Ubangiji ne,

A gare mu kuwa abin al’ajabi ne.’ ”

12 Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi misalin, amma suna jin tsoron jama’a. Don haka suka ƙyale shi, suka tafi.

Biyan Haraji ga Kaisar

13 Suka aiko masa da waɗansu Farisiyawa da mutanen Hirudus, don su burma shi cikin magana tasa.

14 Da suka zo, suka ce masa, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, ba ka kuma zaɓen kowa, domin ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?

15 Mu biya, ko kada mu biya?” Shi kuwa da ya gane makircinsu, ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku kawo mini dinari in gani.”

16 Suka kawo masa. Ya ce musu, “Suran nan da sunan nan na wane ne?” Suka ce masa, “Na Kaisar ne.”

17 Sai Yesu ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” Sai suka yi mamakinsa ƙwarai.

Tambaya a kan Tashin Matattu

18 Sai Sadukiyawa (su da suke cewa, wai ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka tambaye shi suka ce,

19 “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan’uwan mutum ya mutu, ya bar mata tasa ba ɗa, sai lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan’uwansa ‘ya’ya.

20 To, an yi waɗansu ‘yan’uwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure, ya mutu bai bar baya ba.

21 Na biyun kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba ɗa. Na ukun ma haka.

22 Haka dai duk bakwai ɗin, ba wanda ya bar ɗa. Daga ƙarshe kuma ita matar ta mutu.

23 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”

24 Sai Yesu ya ce musu, “Ba saboda wannan ne ya sa kuka ɓata ba? Wato don ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba.

25 Domin in an tashi daga matattu, ba a aure, ba a aurarwa, amma kamar mala’ikun da suke Sama ake.

26 Game da tashin matattu kuma, ashe, ba ku taɓa karantawa a Littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa, ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu’?

27 Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Kun ɓata da gaske.”

Umarni Mafi Girma

28 Sai wani malamin Attaura ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu ya ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, “Wane umarni ne mafi girma duka?”

29 Yesu ya amsa masa ya ce, “Mafi girma shi ne, ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

30 Sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka, da kuma dukkan ƙarfinka.’

31 Mabiyinsa shi ne, ‘Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.’ Ba fa sauran wani umarni da ya fi waɗannan girma.”

32 Sai malamin Attaura ya ce masa, “Hakika gaskiyarka Malam, Ubangiji ɗaya ne, ba kuwa wani sai shi.

33 A ƙaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukan hankali, da dukkan ƙarfi, a kuma ƙaunaci ɗan’uwa kamar kai, ai, ya fi dukkan hadayar ƙone-ƙone da yanke-yanke nesa.”

34 Da Yesu ya ga ya yi masa magana da fasaha, sai ya ce masa, “Ba ka nesa da Mulkin Allah.” Bayan wannan kuma ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.

Tambaya a kan Ɗan Dawuda

35 Sa’ad da Yesu yake koyarwa a Haikalin sai ya ce, “Ƙaƙa malaman Attaura za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?

36 Domin Dawuda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce,

‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,

Zauna a damana,

Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’

37 Dawuda da kansa ya kira shi Ubangiji. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?” Babban taron mutane kuwa sun saurare shi da murna.

Yesu Ya Fallashi Malaman Attaura

38 A koyarwa tasa har ya ce, “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishe su a kasuwa,

39 da kuma mafifitan mazaunai a majami’u, da mazaunan alfarma a wurin biki.

40 Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, da yin doguwar addu’a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”

Baiko Wadda aka Zuba

41 Sai ya zauna gaban baitulmalin Haikalin, yana duban yadda jama’a suke zuba kuɗi a ciki. Waɗansu masu arziki da yawa suna zuba kuɗi masu tsoka.

42 Sai ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta zo, ta zuba rabin kobo biyu a ciki, wato kobo ke nan.

43 Sai ya kira almajiransa, ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiya gwauruwan nan ta zuba cikin baitulmalin nan ya fi na sauran duka.

44 Su duk sun bayar daga yalwa tasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk abin da take da shi, duk ma da kuɗinta na abinci.”