MAR 11

Mutanen Urushalima Sun Marabci Yesu

1 Da suka kusato Urushalima, da Betafaji, da Betanya, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu,

2 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi.

3 Kowa ya ce muku, ‘Don me kuke haka?’ ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa, Zai kuma komo da shi nan da nan.’ ”

4 Sai suka tafi, suka tarar da aholakin a ɗaure a ƙofar gida a bakin hanya, suka kwance shi.

5 Sai waɗanda suke tsaitsaye a gun suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?”

6 Suka faɗa musu abin da Yesu ya ce. Su kuwa suka ƙyale su suka tafi.

7 Suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfiɗa mayafansu a kai, ya hau.

8 Sai mutane da yawa suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka baza ganyen da suka kakkaryo a saura.

9 Da na gaba da na baya suka riƙa sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji!

10 Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na ubanmu Dawuda! Hosanna ga Allah!”

11 Sai ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Da dai ya dudduba kome, da yake magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyun nan.

La’antar da Itacen Ɓaure

12 Kashegari da suka tashi daga Betanya, ya ji yunwa.

13 Da ya hango wani itacen ɓaure mai ganye kore shar, sai ya je ya ga ko ya sami ‘ya’ya. Da ya isa wurinsa bai ga kome ba sai ganye, don ba lokacin ‘ya’yan ɓaure ba ne.

14 Sai ya ce wa ɓauren, “Kada kowa ya ƙara cin ‘ya’yanka har abada!” Almajiransa kuwa suna ji.

Yesu Ya Tsabtace Haikalin

15 Suka iso Urushalima. Ya shiga Haikalin ya fara korar masu saye da sayarwa daga ciki, ya kuma birkice teburorin ‘yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai,

16 ya kuma hana kowa ratsa Haikalin ɗauke da wani abu.

17 Sai ya yi musu gargaɗi ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira masujadata ɗakin addu’a na dukkan al’ummai’? Amma ku kun maishe shi kogon ‘yan fashi.”

18 Da manyan firistoci da malaman Attaura suka ji wannan magana suka kuma nemi hanyar hallaka shi, saboda sun tsorata da shi, don duk jama’a na mamaki da koyarwa tasa.

19 Kowace yamma kuwa Yesu yakan fita gari.

Aya a kan Bushewar Itacen Ɓaure

20 Suna wucewa da safe, sai suka ga ɓauren nan ya bushe har saiwarsa.

21 Bitrus kuwa ya tuna, sai ya ce masa, “Ya Shugaba, dubi! Ɓauren nan da ka la’anta ya bushe!”

22 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku gaskata da Allah.

23 Hakika, ina gaya muku, kowa ya ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku’, bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata abin da ya faɗa zai auku, sai a yi masa shi.

24 Don haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da addu’a, ku gaskata cewa samamme ne, za ku kuwa samu.

25 Koyaushe kuka tsaya yin addu’a, in akwai wanda kuke jin haushinsa, ku yafe masa, domin Ubanku da yake Sama shi ma yă yafe muku laifofinku. [

26 Amma in ba kwa yafewa, haka Ubanku da yake Sama ma ba zai yafe muku laifofinku ba.]”

Ana Shakkar Iznin Yesu

27 Suka koma Urushalima. Yana zaga cikin Haikalin sai manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama’a suka zo wurinsa,

28 suka ce masa, “Da wane izni kake yin waɗannan abubuwa, ko kuwa wa ya ba ka iznin yin haka?”

29 Sai Yesu ya ce musu, “Zan yi muku wata tambaya. Ku ba ni amsa, ni kuwa in gaya muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan.

30 To, baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce? Ku ba ni amsa.”

31 Sai suka yi muhawara da juna, suka ce, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

32 Ma kuwa ce, ‘Ta mutum ce’?” Suna kuwa jin tsoron jama’a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne.

33 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan ba.”