MAR 10

Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure

1 Sai Yesu ya tashi daga nan, ya tafi ƙasar Yahudiya, da kuma hayin Kogin Urdun. Taro kuma ya sāke haɗuwa wurinsa, ya kuma sāke koya musu kamar yadda ya saba.

2 Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wajensa don su gwada shi, suka tambaye shi suka ce, “Halal ne mutum ya saki mata tasa?”

3 Sai ya amsa musu ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”

4 Suka ce, “Musa ya ba da izini a rubuta takardar kisan aure, a kuma saki matar.”

5 Yesu ya ce musu, “Don taurinkanku ne Musa ya rubuta muku wannan umarni.

6 Amma tun farkon halitta ‘Allah ya halicce su, namiji da tamata.’

7 ‘Don haka fa sai mutum yă bar uwa tasa da ubansa, yă manne wa mata tasa.

8 Haka su biyun nan su zama jiki guda.’ Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne.

9 Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”

10 A cikin gida kuma sai almajiransa suka sāke tambayarsa wannan magana.

11 Sai ya ce musu, “Kowa ya saki mata tasa, ya auri wata, zina yake yi da ta biyun.

12 In kuma matar ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

Yesu Ya Sa wa ‘Yan Yara Albarka

13 Suna kawo masa waɗansu yara ƙanana domin ya taɓa su, sai almajiransa suka kwaɓe su.

14 Da Yesu ya ga haka, sai ya ji haushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne.

15 Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na’am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”

16 Sai Yesu ya rugume su, yana ɗora musu hannu, yana sa musu albarka.

Saurayi Mai Dukiya

17 Ya fara tafiya ke nan, sai ga wani ya sheƙo a guje, ya durƙusa a gabansa, ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?”

18 Sai Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Ai, ba wani Managarci sai Allah kaɗai.

19 Ka dai san umarnan nan, ‘Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Kada ka yi zamba. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

20 Sai ya ce masa, “Malam, ai, duk na kiyaye waɗannan tun ƙuruciyata.”

21 Yesu ya dube shi duban ƙauna, ya ce masa, “Abu guda ne kawai ya rage maka. Sai ka je, ka sayar da duk mallakarka, ka ba gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”

22 Da jin wannan magana gabansa ya fāɗi, ya tafi yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.

23 Daga nan sai Yesu ya duddubi almajiransa, ya ce musu, “Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!”

24 Almajiran kuwa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ya sāke ce musu, “Ya ku ‘ya’yana, da ƙyar ne kamar me a shiga Mulkin Allah!

25 Zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”

26 Sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce masa, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”

27 Yesu ya dube su, ya ce, “Ga mutane kam ba mai yiwuwa ba ne, amma fa ba ga Allah ba. Domin kowane abu mai yiwuwa ne a gun Allah.”

28 Sai Bitrus ya fara ce masa, “To, ai, ga shi, mu mun bar kome, mun bi ka.”

29 Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko ‘yan’uwansa mata, ko ‘yan’uwansa maza, ko uwa tasa, ko ubansa, ko ‘ya’yansa, ko gonakinsa, sabili da ni da kuma bishara,

30 sa’an nan ya kasa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, na gidaje, da ‘yan’uwa mata, da ‘yan’uwa maza, da iyaye mata, da ‘ya’ya, da gonaki, amma game da tsanani, a lahira kuma ya sami rai madawwami.

31 Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”

Yesu kuma Ya Sāke Faɗar Irin Mutuwar da Zai Yi

32 Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na tafe gabansu, sai suka yi mamaki, mutanen da suke biye kuma suka tsorata. Ya sāke keɓe sha biyun nan, ya fara shaida musu abin da zai same shi.

33 Ya ce, “Ga shi, za mu Urushalima, za a ba da Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, su bāshe shi ga al’ummai.

34 Za su yi masa ba’a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi.”

Roƙon Yakubu da Yahaya

35 Yakubu da Yahaya, ‘ya’yan Zabadi, suka kusato shi, suka ce masa, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙe ka.”

36 Sai ya ce musu, “Me kuke so in yi muku?”

37 Suka ce masa, “Ka yardar mana, ranar ɗaukakarka, mu zauna ɗaya a damanka, ɗaya a hagun.”

38 Amma Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya sha da ƙoƙon da ni zan sha? Ko kwa iya a yi muku baftisma da baftismar da za a yi mini?”

39 Suka ce masa, “Ma iya.” Sai Yesu ya ce musu, “Ƙoƙon da ni zan sha, da shi za ku sha, baftismar da za a yi mini kuwa, da ita za a yi muku.

40 Amma zama a damana, ko a haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda aka riga aka shirya wa ne.”

41 Da almajiran nan goma suka ji haka, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya.

42 Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko.

43 Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.

44 Wanda duk kuma yake so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawan kowa.

45 Domin Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

Bartimawas Makaho Ya Sami Ganin Gari

46 Sai suka iso Yariko. Yana fita daga Yariko ke nan, da shi, da almajiransa, da wani ƙasaitaccen taro, sai ga wani makaho mai bara, wai shi Bartimawas, ɗan Timawas, yana zaune a gefen hanya.

47 Da ya ji dai Yesu Banazare ne, sai ya fara ɗaga murya yana cewa, “Ya Yesu, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

48 Waɗansu da yawa suka kwaɓe shi, cewa ya yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

49 Sai Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kirawo shi.” Sai suka kirawo makahon suka ce masa, “Albishirinka! Taso, yana kiranka.”

50 Sai ya yar da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu.

51 Yesu ya ce masa, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce masa, “Malam, in sami gani!”

52 Sai Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan take ya gani, ya bi Yesu, suka tafi.