MAR 9

1 Sai ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Mulkin Allah ya bayyana da iko.”

Sākewar Kamanninsa

2 Bayan kwana shida Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. Sai kamanninsa ya sāke a gabansu,

3 tufafinsa suka yi fari fat suna sheƙi, yadda ba mai wankin da zai iya yinsu haka a duniya.

4 Sai Iliya da Musa sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu.

5 Sai Bitrus ya sa baki, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin, mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.”

6 Ya rasa abin da zai faɗa ne, don sun tsorata da gaske.

7 Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena. Ku saurare shi.”

8 Farat haka da suka dudduba, ba su ƙara ganin kowa ba, sai Yesu kaɗai tare da su.

9 Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.

10 Sai suka bar maganar yasu-yasu, suna tambayar juna komece ce ma’anar tashi daga matattu.

11 Suka tambaye shi suka ce, “To, yaya kuwa malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya yă fara zuwa?”

12 Sai ya ce musu, “Lalle ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwa. Yaya kuwa yake a rubuce a kan Ɗan Mutum, cewa zai sha wuya iri iri, a kuma wulaƙanta shi?

13 Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, sun kuma yi masa abin da suka ga dama, yadda labarinsa yake a rubuce.”

Yesu Ya Warkar da Yaro Mai Beben Aljan

14 To, da suka komo wurin almajiran, sai suka ga babban taro ya kewaye su, malaman Attaura kuma na muhawara da su.

15 Da ganin Yesu sai duk taron suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ɗungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi.

16 Ya tambaye su, “Muhawarar me kuke yi da su?”

17 Sai ɗaya daga cikin taron ya amsa masa ya ce, “Malam, ga shi, na kawo maka ɗana, don yana da beben aljan.

18 Duk inda ya hau shi, sai ya doka shi har ƙasa, bakinsa na kumfa, yana tsukun haƙoransa, yana sandarewa. Na kuma yi wa almajiranka magana su fitar da shi, suka kasa.”

19 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ya ku mutanen zamani marar bangaskiya! Har yaushe zan iya zama da ku? Har yaushe kuma zan iya jure muku? Ku dai kawo mini shi.”

20 Suka kawo masa yaron. Da aljanin ya gan shi, nan da nan sai ya buge yaron, jikinsa na rawa, ya fāɗi yana ta birgima, bakinsa na kumfa.

21 Yesu ya tambayi uban yaron, “Tun yaushe wannan abu ya same shi?” Uban ya ce, “Tun yana ƙarami.

22 Ya kuwa sha jefa shi a wuta da ruwa, don ya hallaka shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”

23 Sai Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai, dukkan abu mai yiwuwa ne ga mai ba da gaskiya.”

24 Nan da nan sai uban yaron ya ɗaga murya ya ce, “Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata!”

25 Da Yesu ya ga taro na ɗungumowa a guje, sai ya tsawata wa baƙin aljanin ya ce masa, “Kai, beben aljan, na umarce ka ka rabu da shi, kada kuma ka ƙara hawansa.”

26 Bayan aljanin nan ya yi ihu, sai ya buge shi da gaske, jikinsa na rawa, ya rabu da shi. Yaron kuma ya zama kamar matacce, har ma yawancin mutane suka ce, “Ai, ya mutu!”

27 Amma Yesu ya kama hannunsa ya tashe shi, ya kuwa tashi tsaye.

28 Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a keɓe suka ce, “Me ya sa mu muka kasa fitar da shi?”

29 Sai ya ce musu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu’a.”

Yesu Ya Sāke Faɗar irin Mutuwar da Zai Yi

30 Sai suka tashi daga nan, suka ratsa ƙasar Galili, bai kuwa so kowa ya sani ba,

31 domin yana koya wa almajiransa ne, yana ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane, za su kuwa kashe shi, sa’ad da aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.”

32 Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambaya tasa.

Wane ne Mafi Girma?

33 Suka zo Kafarnahum. Da ya shiga gida sai ya tambaye su, “Muhawarar me kuka yi a hanya?”

34 Amma suka yi shiru, don a hanya sun yi muhawarar ko wane ne babbansu.

35 Sai ya zauna, ya kira sha biyun nan, ya ce musu, “Kowa yake son yă zama shugaba, lalle ne yă zama na ƙarshe duka, baran kowa kuma.”

36 Sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu, ya rungume shi, ya ce musu,

37 “Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”

Wanda ba ya Gāba da Mu, Namu Ne

38 Sai Yahaya ya ce masa, “Malam, mun ga wani na fitar da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya binmu.”

39 Amma Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ai, ba wanda zai yi wata mu’ujiza da sunana, sa’an nan, nan da nan ya kushe mini.

40 Ai, duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne.

41 Kowa kuma ya ba ku ruwan sha moɗa guda saboda ku na Almasihu ne, hakika ina gaya muku, ba zai rasa ladansa ba ko kaɗan.

Sanadodin Yin Zunubi

42 “Da dai wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan ‘yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku.

43 In kuwa hannunka na sa ka laifi, to, yanke shi. Zai fiye maka ka shiga rai dungu, da ka shiga Gidan Wuta da hannu biyu, wuta marar kasuwa kuwa. [

44 A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.]

45 In kuwa ƙafarka na sa ka laifi, to, yanke ta. Zai fiye maka ka shiga rai da gurguntaka, da a jefa ka Gidan Wuta da ƙafa biyu. [

46 A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.]

47 In kuma idonka na sa ka laifi, to, ƙwaƙule shi. Zai fiye maka ka shiga Mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka Gidan Wuta da ido biyu.

48 A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.

49 Da wuta za a tsarkake kowa, kamar yadda ake tsarkake abu da gishiri.

50 Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sane, dame za a daɗaɗa shi? Sai ku kasance da gishiri a zuciyarku, ku yi zaman lafiya da juna.”