MAR 8

Ciyar da Mutum Dubu Huɗu

1 A lokacin nan da wani taro mai yawan gaske ya sāke haɗuwa, ba su kuwa da abinci, sai ya kira almajiransa, ya ce musu,

2 “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna, ba su da wani abinci.

3 In kuwa na sallame su su tafi gida da yunwa haka, ai, za su kasa a hanya, ga shi kuwa, waɗansunsu sun fito nesa.”

4 Sai almajiransa suka amsa masa suka ce, “Ina za a iya samun gurasar da za ta ciyar da mutanen nan a jeji haka?”

5 Sai ya tambaye su, “Gurasa nawa gare ku?” Suka ce, “Bakwai.”

6 Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa. Da ya ɗauki gurasan nan bakwai, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiransa su kai wa taron, suka kuwa kakkai musu.

7 Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan. Da ya yi wa Allah godiya, sai ya ce su ma a kai musu.

8 Suka ci, suka ƙoshi, har suka ɗauki ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai.

9 Mutanen kuwa sun yi wajen dubu huɗu. Sai ya sallame su.

10 Nan da nan kuwa ya shiga jirgi da almajiransa, ya tafi ƙasar Dalmanuta.

Neman Alama

11 Farisiyawa suka zo suka fara muhawara da shi, suna nema ya nuna musu wata alama daga sama, don su gwada shi.

12 Sai ya yi wata doguwar ajiyar zuciya, ya ce, “Don me mutanen zamanin nan suke neman ganin alama? Hakika, ina gaya muku, ba wata alamar da za a nuna wa mutanen wannan zamani.”

13 Daga nan ya bar su, ya sāke shiga jirgi, ya haye wancan ƙetaren.

Yistin Farisiyawa da na Hirudus

14 Sun kuwa manta, ba su kawo gurasa ba, sai guda ɗaya ce kawai gare su a jirgin.

15 Ya gargaɗe su ya ce, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Hirudus.”

16 Suka yi magana da juna a kan ba su da gurasa.

17 Da yake Yesu ya gane haka, sai ya ce musu, “Don me kuke zancen ba ku da gurasa? Ashe, har yanzu ba ku gane ba, ba ku kuma fahimta ba? Zuciyarku a taurare take?

18 Kuna da idanu, ba kwa gani ne? Kuna da kunnuwa, ba kwa ji ne? Ba kwa kuma tunawa ne?

19 Da na gutsuttsura wa mutum dubu biyar gurasan nan biyar, kwando nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Sha biyu.”

20 “To, gurasa bakwai da na gutsuttsura wa mutum dubu huɗu fa? Manyan kwanduna nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Bakwai.”

21 Sai ya ce musu, “To, har yanzu ba ku fahimta ba?”

Warkar da Makaho a Betsaida

22 Suka iso Betsaida. Aka kawo masa wani makaho, aka roƙe shi ya taɓa shi.

23 Ya kama hannun makahon, ya kai shi bayan gari. Da ya tofa yau a idanunsa, ya ɗora masa hannu, sai ya tambaye shi cewa, “Kana iya ganin wani abu?”

24 Sai makahon ya ɗaga kai, ya ce, “Ina ganin mutane kam, amma kamar itatuwa nake ganinsu, suna yawo.”

25 Sai ya sāke ɗora hannu a idanunsa. Makahon kuwa ya zura ido ƙwar, ya warke, ya ga kome garau.

26 Sai Yesu ya sallame shi ya koma gida, ya ce, “Ko ƙauyen ma kada ka shiga.”

Hurcin Bitrus a kan Yesu

27 Yesu ya tashi, da shi da almajiransa, ya shiga ƙauyukan Kaisariya Filibi. A hanya kuwa ya tambayi almajiransa, “Wa mutane suke cewa nake?”

28 Suka ce masa, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, wani daga cikin annabawa.”

29 Sai ya tambaye su, “Amma ku fa, wa kuke cewa nake?” Bitrus ya amsa masa ya ce, “Kai ne Almasihu.”

30 Sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa labarinsa.

Yesu Ya Faɗi irin Mutuwar da Zai Yi

31 Ya fara koya musu, cewa lalle ne Ɗan Mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni, da manyan firistoci, da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da rai.

32 Ya ko faɗi wannan magana a sarari. Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawatar masa.

33 Amma da Yesu ya waiwaya ya ga almajiransa, ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Ka yi nesa da ni, Shaiɗan! Ba ka tattalin al’amuran Allah sai na mutane.”

34 Ya kira taron tare da almajiransa, ya ce musu, “Duk mai son bina, sai yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.

35 Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, saboda bishara kuma, tattalinsa ya yi.

36 Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa?

37 Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?

38 Duk wanda zai ji kunyar shaida ni da maganata a wannan zamani na rashin amana da yawan zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi, sa’ad da ya zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala’iku tsarkaka.”