MAR 16

Tashin Yesu daga Matattu

1 Da Asabar ta wuce, Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma Salome, suka sayo kayan ƙanshi, domin su je su shafa masa.

2 A ranar farko ta mako, da assussuba suka tafi kabarin, da fitowar rana sai suka isa.

3 Suna ce wa juna, “Wa zai mirgine mana dutsen nan daga bakin kabarin?”

4 Da suka ɗaga kai, suka ga, ashe, an mirgine dutsen waje ɗaya, ga shi kuwa, ƙato ne ƙwarai.

5 Suna shiga kabarin, sai suka ga wani saurayi a zaune daga dama, saye da farar riga. Sai suka firgita.

6 Shi kuwa ya ce musu, “Kada ku firgita. Yesu Banazare kuke nema, wanda aka gicciye. Ai, ya tashi, ba ya nan. Kun ga ma wurin da suka sa shi!

7 Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa, duk da Bitrus, cewa zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.”

8 Sai suka fita, suka ruga a guje daga kabarin, suna rawar jiki a ruɗe. Ba su kuma ce wa kowa kome ba, domin suna tsoro.

Yesu Ya Bayyana ga Maryamu Magadaliya

[

9 Da ya tashi da rai da wuri ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magadaliya, wadda ya fitar wa da aljannu bakwai.

10 Ita kuwa ta tafi ta faɗa wa waɗanda dā suke tare da shi, ta tarar suna baƙin ciki, suna kuka.

11 Amma da suka ji yana da rai, har ma ta gan shi, sai suka ƙi gaskatawa.

Yesu Ya Bayyana ga Almajirai Biyu

12 Bayan haka ya bayyana da wata kama ga waɗansu biyu daga cikinsu, sa’ad da suke tafiya ƙauye.

13 Suka koma suka gaya wa sauran, su ma kuwa ba su gaskata su ba.

Umarnin Yesu ga Goma Sha Ɗayan

14 Daga baya ya bayyana ga sha ɗayan nan, su kansu, sa’ad da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurinkansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba.

15 Sai ya ce musu, “Ku tafi ko’ina a duniya, ku yi wa dukkan ‘yan adam bishara.

16 Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi.

17 Za a ga waɗannan mu’ujizai wurin masu ba da gaskiya, wato da sunana za su fitar da aljannu, za su yi magana da waɗansu baƙin harsuna,

18 za su iya ɗaukar maciji, kowace irin guba kuma suka sha, ba za ta cuce su ba ko kaɗan, za su kuma ɗora wa marasa lafiya hannu, su warke.”

An Ɗauke Yesu zuwa Sama

19 To, bayan da Ubangiji Yesu ya yi musu jawabi, aka ɗauke shi aka kai shi Sama, ya zauna dama ga Allah.

20 Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa’azi ko’ina, Ubangiji yana taimakonsu, yana kuma tabbatar da maganarsu ta mu’ujizan nan da suke biye da maganar.]