LUK 1

Gabatarwa

1 Tun da yake mutane da yawa sun ɗauka su tsara labarin waɗannan al’amura da suka tabbata a cikinmu,

2 daidai yadda waɗanda suke shaidu tun farkon al’amari, masu hidimar Maganar, suka rattaba mana,

3 da yake kuma na bi diddigin kowane abu daidai tun farko, ni ma dai na ga ya kyautu in rubuta maka su bi da bi, ya mafifici Tiyofalas,

4 domin kă san ingancin maganar da aka sanar da kai baki da baki.

An Yi Faɗin Haihuwar Yahaya Maibaftisma

5 A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu.

6 Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.

7 Amma ba su da ɗa, don Alisabatu bakararriya ce, dukansu biyu kuma sun tsufa.

8 Ana nan, wata rana Zakariya na kan hidima tasa ta firist, a sa’ad da hidimar ta kewayo kan ƙungiyarsu,

9 bisa ga al’adar hidimar firistoci, sai kuri’a ta nuna shi ne mai shiga Haikalin Ubangiji, ya ƙona turare.

10 A lokacin ƙona turare kuwa duk taron jama’a suna waje, suna addu’a,

11 sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, yana tsaye a dama da bagadin ƙona turare.

12 Da Zakariya ya gan shi ya firgita, tsoro ya kama shi.

13 Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu’arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.

14 Za ka yi murna da farin ciki,

Mutane da yawa kuma za su yi farin ciki da haihuwa tasa.

15 Domin zai zama mai girma a wurin Ubangiji,

Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba.

Za a cika shi da Ruhu Mai Tsarki

Tun yana cikin uwa tasa.

16 Zai kuma juyo da Isra’ilawa da yawa ga Ubangiji Allahnsu.

17 Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya.

Yă mai da hankalin iyaye a kan ‘ya’yansu,

Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai,

Ya tanada wa Ubangiji jama’a, ya same su a shirye.”

18 Sai Zakariya ya ce wa mala’ikan, “Ta ƙaƙa zan san haka? Ga ni tsoho, maiɗakina kuma ta kwana biyu.”

19 Sai mala’ikan ya amsa ya ce, “Ni ne Jibra’ilu da yake tsaye a gaban Allah. An aiko ni ne in yi maka magana, in kuma yi maka wannan albishir.

20 To, ga shi, za ka bebance, ba za ka iya magana ba, sai a ran da al’amuran nan suka auku, don ba ka gaskata maganata ba, za a kuwa cika ta a lokacinta.”

21 Jama’a suna ta jiran Zakariya, suna mamakin jinkirinsa a Haikali.

22 Da ya fito, ya kāsa yi musu magana. Sai suka gane lalle an yi masa wahayi ne a Haikalin. Sai ya riƙa yi musu nuni, amma ba ya magana.

23 Sa’ad da kuma kwanakin hidimarsa suka cika, ya koma gida.

24 Bayan kwanakin nan mata tasa Alisabatu ta yi ciki. Sai ta riƙa ɓuya har wata biyar, tana cewa,

25 “Haka Ubangiji ya yi mini a kwanakin da ya dube ni da rahama, domin yă kawar mini da wulakanci a wurin mutane.”

An Yi Faɗin Haihuwar Yesu

26 A wata na shida Allah ya aiko mala’ika Jibra’ilu zuwa wani gari a ƙasar Galili, wai shi Nazarat,

27 gun wata budurwa da aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu, na zuriyar Dawuda, sunan budurwar kuwa Maryamu.

28 Sai mala’ikan ya je wurinta, ya ce, “Salama alaikun, yake zaɓaɓɓiya, Ubangiji yana tare da ke!”

29 Amma ta damu ƙwarai da maganar, ta yi ta tunani ko wannan wace irin gaisuwa ce.

30 Mala’ikan kuma ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah.

31 Ga shi kuma, za ki yi ciki, ki haifi ɗa, ki kuma sa masa suna Yesu.

32 Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki.

Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dawuda,

33 Zai kuma mallaki zuriyar Yakubu har abada,

Mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.”

34 Sai Maryamu ta ce wa mala’ikan, “Ƙaƙa wannan zai yiwu, tun da yake ba a kai ni ɗaki ba?”

35 Mala’ikan ya amsa mata ya ce,

“Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki,

Ikon Maɗaukaki kuma zai lulluɓe ki.

Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.

36 Ga shi kuma, ‘yar’uwarki Alisabatu ma ta yi cikin ɗa namiji da tsufanta, wannan kuwa shi ne watanta na shaida, ita da ake ce wa bakararriya.

37 Ba wata faɗar Allah da za ta kasa cika.”

38 Sai Maryamu ta ce, “To, ga shi, ni baiwar Ubangiji ce, yă zama mini yadda ka faɗa.” Sai mala’ikan ya tashi daga gare ta.

Maryamu ta Ziyarci Alisabatu

39 A kwanakin nan Maryamu ta tashi da hanzari, ta tafi wata ƙasa mai duwatsu, zuwa wani gari na ƙasar Yahuza.

40 Ta shiga gidan Zakariya ta gai da Alisabatu.

41 Sai ya zamana da Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, jariri ya motsa da ƙarfi a cikinta. Aka kuwa cika Alisabatu da Ruhu Mai Tsarki,

42 har ta tā da murya da ƙarfi, ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata, ɗan cikinki kuma mai albarka ne!

43 Ta yaya wannan alheri ya same ni, har da uwar Ubangijina za ta zo gare ni?

44 Domin kuwa da jin muryarki ta gaisuwa a kunnena, sai jaririn ya motsa da ƙarfi a cikina domin farin ciki.

45 Albarka tā tabbata ga wadda ta gaskata, domin za a cika abubuwan da Ubangiji ya aiko a faɗa mata.”

Waƙar Maryamu

46 Sai Maryamu ta ce,

“Zuciyata na ɗaukaka shi, Ubangiji,

47 Allah Mai Cetona, da shi ruhuna yake ta farin ciki,

48 Domin fa shi ya dubi ƙasƙancin baiwa tasa.

Ga shi, jama’a ta dukan zamanai,

Za su ce mini mai albarka ce nan gaba.

49 Domin fa shi da yake Mai Iko,

Manyan al’amura ya yi mini,

Sunansa labudda mai tsarki ne.

50 Daga zamanai ya zuwa wani zamani,

Jinƙansa yana ga waɗanda suke tsoronsa.

51 Manyan ayyuka da ya yi,

Masu girmankai, su da dabarbarunsu ya warwatsa.

52 Ya firfitar da sarakuna a sarauta,

Ya ɗaukaka ƙasƙantattu.

53 Mayunwata ya ƙosar da abubuwan alheri,

Mawadata kuwa ya sallame su hannu wofi.

54 Ya taimaka wa baransa Isra’ila,

Domin yana tunawa da jinƙansa.

55 Ya cika faɗarsa ga kakanninmu,

Ga Ibrahim da zuriyarsa, har abada.”

56 Maryamu kuma ta zauna tare da Alisabatu wajen wata uku, sa’an nan ta koma gida.

Haihuwar Yahaya Maibaftisma

57 To, lokacin Alisabatu na haihuwa ya yi, ta kuwa haifi ɗa namiji.

58 Sai maƙwabta da ‘yan’uwanta suka ji yadda Ubangiji ya ji ƙanta ƙwarai, har suka taya ta farin ciki.

59 Sai ya zamana a rana ta takwas suka zo yi wa ɗan yaron kaciya. A dā za su sa masa sunan ubansa, Zakariya,

60 amma uwa tasa ta ce, “A’a, Yahaya za a sa masa.”

61 Sai suka ce mata, “Ai kuwa, ba wani ɗan’uwanku mai suna haka.”

62 Sai suka alamta wa ubansa, suna neman sunan da yake so a sa masa.

63 Sai ya nema a ba shi allo, sa’an nan ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Duka suka yi mamaki.

64 Nan da nan ya sami baki, kwaɗon harshensa ya saku, ya fara magana, yana yabon Allah.

65 Sai tsoro ya kama dukan maƙwabtansu. Aka yi ta baza labarin duk waɗannan al’amura ko’ina a dukan ƙasa mai duwatsu ta Yahudiya.

66 Duk waɗanda suka ji kuwa suka riƙe a zuciyarsu, suna cewa, “Me ke nan ɗan yaron nan zai zama?” Gama ikon Ubangiji yana tare da shi.

Waƙar Zakariya

67 Sai aka cika ubansa Zakariya da Ruhu Mai Tsarki, ya yi annabci, ya ce,

68 “Ubangiji Allahn Isra’ila,

A gare shi ne lalle yabo yake tabbata,

Domin ya kula, ya yi wa jama’a tasa fansa.

69 Ya ta da Mai Ceto mai iko dominmu,

Daga zuriyar baransa Dawuda.

70 Yadda tuntuni ya faɗa ta bakunan

Annabawa nasa tsarkakan nan,

71 Yă cece mu daga abokan gābanmu,

Har ma daga dukan maƙiyanmu.

72 Domin nuna jinƙai ne ga kakanninmu,

Ya tuna da alkawarinsa mai tsarkin nan.

73 Shi ne rantsuwan nan wadda ya yi wa ubanmu Ibrahim,

74 Domin yana cetonmu daga abokan gābanmu,

Mu bauta masa ba da jin tsoro ba,

75 Sai dai da tsarki da adalci a gabansa,

Dukan iyakar kwanakin nan namu.

76 Kai kuma, ɗan yarona, za a ce da kai annabin Maɗaukaki,

Gama za ka riga Ubangiji gaba,

Domin ka shisshirya hanyoyinsa,

77 Kă sanar da ceto ga jama’a tasa,

Wato ta samun gafarar zunubansu,

78 Saboda tsananin jinƙai na Allahnmu,

Daga Sama hasken asubahi zai ɓullo mana,

Daga can Sama ne fa zai keto mana,

79 Domin yă haskaka na zaune cikin duhu,

Da waɗanda suke zaune a bakin mutuwa,

Domin ya bishe mu a hanyar salama.”

80 Sai ɗan yaron ya girma, ya ƙarfafa a ruhu. Ya kuwa zauna a jeji har ranar bayyanarsa ga Isra’ila.