MAT 15

Al’adun Shugabanni

1 Waɗansu Farisiyawa da malaman Attaura suka zo wurin Yesu daga Urushalima, suka ce,

2 “Don me almajiranka suke keta al’adun shugabanni? Domin ba sa wanke hannu kafin su ci abinci.”

3 Sai ya amsa musu ya ce, “Ku kuma don me kuke keta umarnin Allah saboda al’adunku?

4 Domin Allah ya yi umarni ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa lalle a kashe shi.’

5 Amma ku kukan ce, ‘Kowa ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni an ba Allah,” to, ba lalle ya girmama ubansa ba ke nan.’

6 Wato, saboda al’adunku kun bazanta Maganar Allah.

7 Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce,

8 ‘Al’ummar nan a baka kawai suke girmama ni,

Amma a zuci nesa suke da ni.

9 A banza suke bauta mini,

Don ka’idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’ ”

Abubuwan da Suke Ƙazantarwa

10 Ya kira taro ya ce musu, “Ku saurara, ku fahimta.

11 Ba abin da yake shiga mutum ta baka ne yake ƙazanta shi ba, abin da yake fita ta baka yake ƙazanta mutum.”

12 Sai almajiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisiyawa sun ji haushi da suka ji maganan nan?”

13 Ya amsa ya ce, “Duk dashen da ba Ubana da yake Sama ne ya dasa ba, za a tumɓuke shi.

14 Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.”

15 Amma Bitrus ya ce masa, “A yi mana fassarar misalin nan.”

16 Yesu ya ce, “Ku ma, ashe, har yanzu ba ku fahimta?

17 Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum ta baka, cikinsa ya shiga, ta haka kuma zai fice?

18 Amma abin da ya fito ta baka, daga zuci yake, shi ne kuwa yake ƙazantar da mutum.

19 Don daga zuci mugayen tunani suke fitowa, kamar su kisankai, da zina, da fasikanci, da sata, da shaidar zur, da yanke.

20 Waɗannan suke ƙazantar da mutum. Amma a ci da hannu marar wanki ba ya ƙazantar da mutum.”

Bangaskiyar Mace Bakan’aniya

21 Yesu ya tashi daga nan, ya tafi zuwa ƙasar Taya da Sidon.

22 Ga wata Bakan’aniya mutuniyar ƙasar, ta zo, ta ɗaga murya ta ce, “Ya Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina. Wani aljani ya bugi ‘yata, ba yadda take.”

23 Amma bai ce da ita kanzil ba. Sai almajiransa suka zo suka roƙe shi, suka ce, “Sallame ta mana, tana binmu tana cika mana kunne da kuka.”

24 Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin jama’ar Isra’ila kaɗai aka aiko ni.”

25 Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, ka taimake ni mana!”

26 Ya amsa ya ce, “Ai, bai kyautu a bai wa karnuka abincin ‘ya’ya ba.”

27 Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin ‘ya’ya.”

28 Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Kai, uwargida, bangaskiyarki da yawa take! Yă zamar miki yadda kike so.” Nan take ‘ya tata ta warke.

Yesu Ya Warkar da Mutane Masu Yawa

29 Yesu ya tashi daga nan, ya bi ta bakin Tekun Galili. Sai ya hau dutse ya zauna a can.

30 Taro masu yawan gaske suka zo wurinsa, suka zazzo da guragu, da masu dungu, da makafi, da bebaye, da kuma waɗansu da yawa, suka ajiye su a gabansa, ya kuwa warkar da su.

31 Har jama’ar suka yi ta al’ajabi da ganin bebaye suna magana, masu dungu sun sami gaɓoɓinsu, guragu na tafiya, makafi kuma suna gani, duk suka ɗaukaka Allah na Isra’ila.

Ciyar da Mutum Dubu Huɗu

32 Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.”

33 Sai almajiran suka ce masa, “Ina za mu samo gurasa a jeji haka da za ta isa ciyar da ƙasaitaccen taro haka?”

34 Yesu ya ce musu, “Gurasa nawa suke gare ku?” Suka ce, “Bakwai, da ƙananan kifaye kaɗan.”

35 Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa.

36 Da ya ɗauki gurasa bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma na, bai wa jama’a.

37 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai.

38 Waɗanda suka ci kuwa maza dubu huɗu ne, banda mata da yara.

39 Da ya sallami taron ya shiga jirgi ya tafi ƙasar Magadan.